page 26

7K 558 118
                                    

*Haske writer's Association* (home of expert and perfect writer's)

*SIRRIN MIJINA*

*Billy Galadanchi*

  Sadaukarwa ga qawata
*Nafeesatu sani kibiya....(Pheey)*

Vote me on wattpad at 68 billygaladanchi.

*Masu rubuta cewa nace na dakatar da rubuta littafina banida abinda zance muku anniyarku tabiku, idan kun isa seku hanani rubutun, wannan ta isheku*

                  26

Da rarrage zuhra taje d'akinta tana me zubar da qwallan tashin hankali, yau ita Hisham ke duka yake kuma umarta akan ta kwashe kayanta zuwa part d'inda bekai girman nata ba, cikin qunan rai  ta zari wayarta ta soma kiran mommy tana kuka ta sanar mata yanda ake ciki

"Kiyi haquri Zuhra na ki kwashe kayanki ki koma inda yace din,ai shima wurine me kyau kuma yamafi wannan zama cute girmane kawai banbanci"

"Haba mommy? Yaya zaki ce na qasqantar dakaina akan zeyi aure? Kuma ke gani kike abarshi yae auren yafi" tsaki mommy taja

"Quruciya tana d'awainiya dakene kawai Zuhrah waike bakya gane karatune? Yanzu da mahaifinku yake shirin mayarda ni senayi wani gigin haukan, kiyi yanda yace kafin na koma zansan abinyi" kuka ta saka wiwi akan bazata tab'a barinshi aure ba uwar taace ke kika sani kiyi yanda kikaga daidai ne" ta kashe wayarta

*********

    Zuhra na zaune da yammacin washe garin ranar katsam taga maza anata kwasar kayan d'akinta da komai seda akayiwa gidan qanqat!!! Kuma abin takaici qarti har cikin dakinta haka aka fita da kayan se ashar takeyi Hisham ko kallon ta beyiba iya kayan sawarta aka kai part din amma komai a manyan motocin daukar kaya akai waje dasu....

"Ki shirya zan kaiki gidan Aunth Angel na sati daya zuwa biyu zan miki gyarane gaba daya gida,zan zuba miki komai sabo" kallonshi tayi

"Akan zakayi aure zakace zakamun gyara ka dawomun da kayana banaso" murmushi yae

"Nafasa auren ai, karki wasu en damu gyaran dai nakeso namiki haka kawai" wawiyar seta yarda ta shiga godiya da washe baki takuma shirya  ta wuce gidan Aunty Angel itada erta ummie......

    Shamsiyya zaune tare da babban yaronta tana bashi abinci a baki kasancewar yana fama da zazzab'i me tsanani gashi mahaifin shi be dawo ba tunda yafita har yamma batasan dalili ba, tana nan tana tunanin inda yashiga kuma bata samun wayarshi  se kawai taga ya shigo gidan kamar baya cikibmn nutsuwa miqewa tayi

"Abul khair lapiya kuwa?" A wahalce ya kalleta

"Banda lapia ne shamsiya, zazzab'i nakeyi sosai tun d'azu nake kwance wlhy seda ma aka qaramun ruwa yanzu haka,ance typhoid fever ne" dafe kanta tayi

"Very Own shine bakamun waya ka gayamun ba" zama yae kusa da saleem
"Banga wayar ba ta fad'i d'azu gaba d'aya na nema bangani ba daga bayama se akace dani a kashe take dana kira da wayar masinjan mu, naso nakiraki da wata wayar naga rashin dacewar hakan" hannunta takai jikinsa taji zafi rauu

"Sannu Habeeby kaji inshaa Allah zakaji sauqi kaga ko saleem baida lapia koda aka dakko su daga school ko tsayuwa baya iyayi seda na bashi paracetamol nasamu yakecin abinci" tausayin yaron yaji ya kamashi matuqa ya daurashi akan cinyarsa

"A shiryashi akaishi wurin yara emergency kuje tare nizanyi bacci kadan" ba musu ta rakashi daki ta dawo takira driver ya kaisu!!!!

Nafeesah tasha mamakin rashin ganin CMD ko wayarshi wuni daya cur har dare tana kranshi bata samu,hankalinta ya tashi amma haka ta haqura shi kuwa CMD sosai yake jin jiki bekoyi ta tasu ba sam ta kanshi yakeyi!!! Saleem ya samu sauqi sosai shikam dagashan anti malaria ya miqe..... Se washe gari da yamma sannan yace da shamsiyya

SIRRIN MIJINAWhere stories live. Discover now