page 22

5.9K 477 56
                                    

*Haske writer's Association* (home of expert and perfect writer's)

*SIRRIN MIJINA*

*Billy Galadanchi*

  Sadaukarwa ga qawata
*Nafeesatu sani kibiya....(Pheey)*

           *Maman Mufeedah kd wannan shafin nakine ke kadai kiyi yanda kikeso dashi ki kacaccala shi kin burgeni dakike assisting nawa da taimakawa mutanen dake neman book d'innan Allah yabar qauna*

    Pheey tunda aka sallamo ta a asibiti Hisham ke matsa mata lamba, kullum seya zo yauma kamar kullum bayan magrib tana kwance saman kujera se sallama shuraim taji ya shigo bayan ya gaidata ya ce

"Anty Pheey dan Allah yau kawai ki daure kije kiga yaa hisham yana waje,inyaso ki gayame daga yau karya qara zuwa wurinki har abada tunda bakyaso" kallon shi tayi ka.kaishi parlorn baqi  ina zuwa yanzu" da wannan ya juya

Ya jima yana tunanin ta inda ze fara kafin dabqyar ya lalubo kalmomin

"Nafeeaah nasan namiki laifi kuma na cutar dake amma dan Allah kiyi haquri ki gafarceni wlhy ina cikin tsananin damuwa da tashin hankali tun barinki gidana" kallonshi tae da murmushi akan fuskarta

"Karka damu Hisham ni harga Allah nama manta wanzuwarka a duniya bare abinda kamun, kuma zancen Allah ya isan da kake na janye a wuce wurin Allah ya bamu hakuri dukkanmu amma dan Allah ka nisantar da kanka daga zuwa wurina sabida wlhy bazan lamunci ganin kaba, ka manta dani a rayuwarka ka dena sakawa a ranka cewar zan taba zaman aure dakai kaji" kallonta yae hisham se qwallah

"Haba Pheey kasheni kikeso kiyi,wlhy idan ban rayu dake ba na tabbatar yau ko gobe ko anjima sena rasa raina, rayuwa matsayina na namiji babu amfani idan babu ke acikinta wlhy" sheqeqe ta dago ta kalleshi

"Sabida zallan sha'awa nake ranka? Sabida son dakakeyi muyi aure na zame maka sex machine dazakataci ba yau ba gobe, sabida kana so ka riqa moruwa da laushin fatana? Ko sabida kanaso ka riqa jinqa kana iwo acikin kogina? Kokuwa aa so kake ka riqa bin mazaunai na da kallo a duk inda nabi sabida ragewa kanka sha'awa? Bari kaji Hisham dire laifin dakamun na sakina a gefe Amma saurari wannan " Wlhy summa tallahi bazan tab'a yin auren ramuwar gayya ba ba riba aciki sabida badan Allah bane, bazan tab'a auren wanda ke sha'awa naba sabida sha'awar gushewa take with time, bazan taba auren wanda bana so kuma kaga wlhy ban sanka ko kadan megadin gidana ma bansanka bare me gidan gaba d'aya, sa'arka d'aya danace maka  na yafe shima sabida ka sako Allah a cikine banda haka bazan yafe ba dan Allah Hisham ka bar nan gidan wlhy idan ka qara zuwa mun korar karnuka zan maka ta wulaqanci ma kuwa!!!!" Shiru yae be tnka ba sabida ya rasa bakin magana anan dai ta barsa tayi ta takanka zuwa ciki jiki ba qwari ya kama hanyar waje  acen yaci karo da CMD yana jingine a jikin motarsa se tashin qshi yake qarasawa yae suka gaisa yace dashi

"Yallab'ai ka tayani murna matana dai ta amince zata koma gidan ta nagode da qoqarin ka akaina, yanzu ma haka tin d'azu ina ciki mun gama sasantawa fitowa na kenan" wani irin mugun kishine  ya tarnaqe CMD ya kalleshi

"Naji kaje Allah ya kyauta" juyawa yae yasani ya kare masa gwiwa wataqil ma yae fushi da ita me tsanani ya kula ya shaqa sosai se murmushi yake,ita kuwa bayan ya kirata  a wayan akan yana waje se yaa sudai's ya mata waya yana gaya mata hukuncin da yayyun babanta da qaninshi suka yanke akan baiwa daddy ita kuka ta saka masa wiwi akan wlhy sedai ta shiga funiya to tayi sa'a shima yana bayanta yace sam gobe ze boyo jirgin safe kuma ze dawo ne inshaa Allah suje bula d'in tare ayita ta qare bazata aure tsoho ba....

Tana zuwa kusa dashi takasa magana kuka keso yaci qarfinta sosai ba kadan ba har ranta takejin zafin abubuwan dake faruwa da rayuwarta kodai duniya zata shiga ne kukan kawai taci gaba dayi bayan ta sunkuya saman gwiwowinta, wani takaici take baiwa Saffwan seda ta gama yanke hukuncin komawarta gidan tsohon mijinta zatazo tana masa kukan munafurci ga shaida ya gani daga cikin gidan Hisham yafito kuma baze tab'a masa qaryaba ai da ba ayi hakan ba tsaki yaja ya zaga ya shige motarsa ya tayar tarasa dalilin yi mata hakan koshima yaji labarin auren da en uwanta suke shirin had'ata da daddy ne? Ko zato yake ta amince ne? To amma aidaya mata waya yana waje har wasa ya mata menene dalilinshi na mata haka? Shida idan yaga tana kuka ma ze rud'e sosai!!! Komawa tai cikin taci gaba da kuka tana faman kiranshi tun baya da d'agayawa harya soma rejecting qawata tashiga tashin hankalin daya janyo ta kwana tana kuka....

*Washe gari*

Se wuraren shabiyu sudais ya iso zuwa lokacin ma pheey wani zazzafan zazzab'i takeji amma haka suka je qauyen na Bula zaman dirshan sukai dukkansu suka gama jin bayanin iyayen nasu kan sudais yace

"Baba lauwali dan Allah ku janye maganar tsohon nan ku mayar masa da sadaqinsa yarknyar dai bata sansa" wani harara Baba iro ya wurgo masa ya tsirgar da yawun asuwakin dayake yace
."wlhy bazaku hanamu cin arziqi ba  dolene seta aureshi bawan Allah dayazo ya zaga dangi yabi kowa da abin arziqi wlhy baku isaba" takaicine ya ishi nafeesah tace

"Baba iro ka manta aurena danai na farko kawu manga ne kurun yajemun daurin aure daddy n ne yamun komai,wannan na biyun kuwa ba wanda yaje har komai ma shi kuka qara sakarwa se yanzu dan azababben kwadayu zakuce ni taku ce to na rantse da sarkin dake busan numfashi bazan aure shiba har abada!!! Kunada yaya ai ku bashi ya aura idan arziqi zakuci badai niba. Baki suka riqe dukkansu sukai mamakin jin kalamanta gashi tafisu gaskia kowa ya kasa magana miqewa tai

" kar naji wanda ya dauran aure dashi idan ma kun daura kwa warware babu wanda ya tab'a damuwa da cinmu shammu suturunmu yaya muke rayuwa se yanzu dan tsabaragen san abin duniya zakuce dani wai na aure wani yanzu, bazan ba wlhy" hakuri suka basu akan zasu bashi hakuri sudais ya musu alkhairi ya qara rufe bakinsu sukace zasu bashi haquri akan bataso.

Wasa wasa fa kwana biyu harta wuce Saffwan ya d'auka da zafi dukda shima yanashan wahala amma yace lallai shikam  baze qara zuwa guntaba tunda yake bata ganin girmanshi sam!! Taci amanar zamansu tare zata komawa tsohon mijinta to mema zata ce dashi haka dai itama ta d'auki fushi akan bazata qara kiransa ba har abada sedai sansa yae ajalinta!!.

*kumun uzuri jiya banjin dadi yau kuma na danyi tafiyane inshaa Allah gobr zanyi da yawa sosai*

Mom Nu'aiym.

SIRRIN MIJINAWhere stories live. Discover now