page 13

6.3K 591 34
                                    

*Haske writer's Association* (home of expert and perfect writer's)

*SIRRIN MIJINA*

*Billy Galadanchi*

  Sadaukarwa ga qawata
*Nafeesatu sani kibiya....(Pheey)*

     13

Nafeesah zaune saman kujerar dake falon ta tana danna wayan ta yanzu sam ta soma cire Hisham a ranta ta kula ya tsane ta tsanar data rasa dalilinshi sam! Takasa gane me ta masa arayuwa..sallamar hajiyar su Mukhtar tajiyo wannan ya sanya ta miqe da fara'arta taje gunta suka gaisa cikin mutunci sannan hajiyar tace

"Dama nazone akan zancen komawarki gida,kinga dai sam be dace ace wai kinata zama acikin gida ba mijiba komai ze iya faruwa, sabida haka nace zanzo na sanar miki tunda ya kasance har kin gama takaba dan Allah seki koma gun iyayen riqonki, Mubarak ma muka yanke shawarar cewar ya dawo da zama anan din" kallonta tayi ,qirjinta yayi mugun dokawa ta kula da wani tsana datake fuskanta wurin Mommyn su zuhra wacce batasan dalilin taba, yaya zata zauna dasu kuma?? Bata tab'a tsammanin zasuce tabar gidan ba sam!! Wataqil sabida sunga batada jini da Mukhtar ne banda haka mezesa su mata haka kai tsaye kumama mubarak aiko aure beyiba jinjina kanta tayi cikin sanyin jiki

"Inshaa Allah mama nanda wani satin zan kwashe komai sena koma gida" kallonta mamar tai

"Gwara dai zuwa jibi Er nan kiyi qoqari zuwa jibin ki kwashe" tasha mamakin sauyawar har maman amma batace komai ba....

  Kallon ta mommy tayi bayan ta gama jin bayaninta

"Gaskia nikam Nafeesah namiki riqo iya wanda zan iya ga qaninki a wurina, gaki ga yayan ki sabida aiko Sudais nice uwarshi,komai nashi nice yaya zakice kuma nan zaki dawo nida zaki taimaka munma da gyaran gidan ku kikayi kuka kwashi qanin ki kuka koma can tunda kin mallaki hankalin kanki yanzu" Da sauri da d'ago ta kalli mommy se yanzu ta gane komai lalacewar aure yafi rashin sa, da mijinta nada rai bazata nemi matsuguni ta rasa ba murya na rawa tace

"Mommy dan Allah kimun rai, kodan mutane, yanzu zasuce  ina zaman banza nikadai a gida, kuma kinga yanayin aikina ina zankai shuraim idan zan tafi" kallon sheqeqe ta watso mata

"Shin nikam wai Nafeesah yanzu duk mutuncin dana muku bakya gani, ku koma dangin ubanku mana,kinafa ganin Allah ne kawai ya kub'utar da zuhra na duk a sanadin ki"  mamakin kalamanta ya sanya nafeesa ta kasa magana se hawayen da d'aya kebin d'aya yaa jalal dake zaune yace

"Mommy babu fa inda Nafeesa kedashi dayafi gidannan, yaushe ma kika kusa rasa zuhrah akan Nafeesah ita da akawa asarar miji fa, ki janye zancen koma warsu wani wurin anan zasu zauna Allah ya baku haqurin zama da juna" shiru tayi sabida tasan yafita gaskia ita dai tunda zuhra keso Nafeesa ta auri mijinta taji batasan yarinyar ko kad'an gashi zuhra ta kasa gane abinda take nufi dana sani ne mara adadi ze biyo bayan wannan haukan datake shirin had'awa.....

Yauma kamar kullum Nafeesa daga office kai tsaye gida ta wuce, dayake ta koma gidan su zuhrah dukda yake sam batajin dad'in zama  da mommyn yanzu damuwa ta mata yawa da har take mantawa da zancen Hisham a rayuwarta kullum fatanta ta samu miji tayi aure yanda yake nuna halin ko in kula akanta itama haka take masa sam ba ruwan ta da shi ko wurin aiki gaisuwa kawai ke shiga tsakanin su se kuwa maganar aiki idan ta taso!!! Gaida mommy tai ta ansata ciki ciki kamar yanda ta saba bata damu ba tawuce dakin su abinta idan da sabo dama ta saba...ko zama batayi ba mommyn ta shigo

"Ke Nafeesah Daddy yace a sanar dake ki fito da mijin aure kiyi aure indai ba kuma kema kamar yanda mijinki ya sanyawa zuhra ido haka kema kika sanyawa mijinta ido ba" qirjinta ne ya doka ta sani wannan sharrin mommy ne sam daddy bazece haka ba dudu yaushe ta gama takaba? Wata uku da suka wuce mijinta ko shekara beyi da mutuwa ba lallai duniya juyin juyi ce ita yanzu ina taga mijin aure? Mema ya kawo maganar mijin Zuhrah kodai dama shine mommy kewa d'age d'age sam ita tama manta yanzu idan bagida zuhra tazoba basa haduwa sesuyi wata basu hadu ba wani zubin ma koda zatazo tana gun aiki!!! Takaicin duniya dukya isheta tama rasa me zatace haka har mommh ta fita a d'akin bata lalubo bakin magana ba....

  Tati late sosai bacci ne ya sure ta yau sukeda ward round gashi har 9:15 am bata ma isa asibitin ba bare se wuraren da rabi ta qarasa ward d'in koda taje sun ga gado yafi uku bin bayansu tayi tanaso tabashu haquri amma ya had'e fuskar nan tamau ita ta mugun qagara ta kammala house manship d'innan idan ta dawo sam bazata zo wurim mata ba canja wa zatayi zuwa d'akin yara yafiye mata kwanciyar hankali da wannan mugun halin nashi.....

"Morn sir" shine abinda ta furta amma gogan ko kallon inda take beyiba haka har suka qare be tambayeta komai ba, bin bayan shibtai zuwa office tace bayan ta kalleshi

"Sir Am so sorry plss, bacci ne ya kwasheni sabida daren jiya nayi fama da ciwon kai ban samu bacci ba" qala bece mata ba harta juya ta fita cikin jin zafin shi sosai da sosai.... Har qwalla seda tayi meta yiwa mutane suka tsaneta? Ko qwaro bata kashe ba bare ace tayi kisan kai, tana zama a doctor's common room nasu ta cire takalminta ta kwanta saman gadon nasu se kuka ya qwace mata dama bata tarar da kowa ba tafi 30mns tana kukan daya haddasar mata da tsananin ciwon kai me had'e da jiri idan nan dama gashi qanana ya qara shigewa ciki yayi jajir fuskar tayi luhu luhu dama ga uban kumatu gabaki d'aya tausayin rayuwarta takeji a en kwanakin nan matsayin ta na likita ta tabbatar wa kanta hawan jini ne da ita sabida yawan tarin damuwar dake cikin ranta Allah yayita mace me tsananin yawaita sha'awa ga kuma qaddarar daya afka mata, gani take butulcewa Allah ne da Ni'imar bata mukhtar dayayi ke tambayar ta sabida ada bata tsintar kanta da tsantsar sha'awa kamar yanzu harta soma ramewa, tana zargin kanta da sanya sha'awar wanin kijinta alhalin tanada aure datayi ada...dabata saurari batutuwan zuhrah masu zuwa da sautuka na amon shedan ba da bata afka cikin wahala baa yanzu ya zatayi, tana haka Dr. Shamcia tashigo ta sameta a d'akin da sauri tayi kanta tayita bata magana harta tsagaita amma fir tasoma somewa a wurin taimakon gaggawa aka bata zuwa Emergency inda gwajin farko ya tabbatar akwai cutar hawan jjini a jikinta...duk wannan budurin da akeyi sam sam sam Hisham baida labari seda ya aika kiranta ake gaya masa yasha mamakin jin wai tanada hawannjiji ya matuqar ji tausayin ta ba iyaka besota da kamuwa da cuta ba kam haka yawa zuhra waya ta garzayo asibitin seda ta kwana uku akai discharging nata inda ya bata sabon hutu na  kwana biyar zuwa sati harta warke.....

  Zaune take a office d'insa suna fuskantar juna ya tattare nutsuwar shi kacokam zuwa gareta yace da ita cikin sanyin murya

"Pheey menene damuwar ki a rayuwa? Hawan jini fa me yawa akace kinada a en shekarunki har zaki tarwatsa rayuwarki haka cutar hawan juna aiba cuta bace me kyau ko a manya bare ku yara dududu shekarunki nawa Nafeesa? Dan Allah sanar dani pheey menene yake damun ki?" Zuwa wannan lokacin har qwalla ya taru a idanta sosai  ta kasa b'oye damuwarta sabida bata tab'a gayawa kowa ba shisa abin keso ya kasheta ta zayyane masa komai dan gane da kyarar datake gani agun mommy ta qara da cewar

"Yaa Hisham gashi kaima narasa dalilin daya sanya ko gani na ma baka sanyi bansan laifina ba a kisan da Zuhra tawa Mukhtar? Mezaisa ni kowa ya kama ya tsaneni? Mena maka yaa Hisham? Dacen bakamun hakan ba se yanzu? Idan wani abin namaka seka gayamun yaa Hisham ya kukeso nayi da raina? Zuhrace abokiyar shawara dajin matsalolina,itama ta sauya mun bata sakin jikin ta dani hasalima nauyi na takeji, idan na kira yaa sudais nan ma fitina yace na dameshi banida haquri banida uwar dazan gayawa matsalana yaa Hisham banida abokiyar shawara, er uwata zuhra ta denamun kamar da ya zanyi?" Shiru tayi taci gaba da kukan ta yayinda tayi mugun karyar masa da zuciya  ya langwabar da kai zuwa yanzu ji yakeyi tamkar ya kai mata kyakyawar runguma saisaita nustuwarsa yae yace

"Kiyi hakuri Nafeesah, ki gafarceni bazan qara miki wannan ba nima, kuma dan Allah na zama yayanki, abokinki,amininki,qawarki,er uwarki na zame miki komai ma kinji Nafeesah, dan Allah ki dena damuwar nan hankalina ya tashi sosai dajin kalar ciwon dake gareki bazan gafar tawa kaina ba idan wani abin yasameki" shiru tayi amma ta tsagaita kukan seda ya samu kanta tana murmushi sannan ya sallameta, ya nutse a kujera yana tsananin tausayinta  labarin data bashi ya gano tanada haquri yaji kuma kaso hamsin acikin qiyayyar dayake mata ha ragu lumshe idanshi yayi yana nazarin abinyi akan yarinyar!!!!!

Kwana bi'u bakujinj kuyi haquri inshaa Allah yanzu kam zamu ci gaba da samun daily update.

Ina buqatar comments d'inku en uwa inasan jin naku ra'ayoyin sis Azzah tace abaiwa phee nafa mijin abar zuhra da nata...lolxx

Wattpadd people u vote plss

Mom Nu'aiym .

SIRRIN MIJINAOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz