page 19

6.1K 481 42
                                    

*Haske writer's Association* (home of expert and perfect writer's)

*SIRRIN MIJINA*

*Billy Galadanchi*

  Sadaukarwa ga qawata
*Nafeesatu sani kibiya....(Pheey)*

              19

Miqewa Pheey tayi daga tsugunen da take ta qura masa ido na en daqiqu ta kasa gane inda ya dosa,saki kuma har biyu washe garin tariyarta

"Innalillahi wa inna ilaihirraji'unn"
Shinr kalmar farko data soma furtawa kan tayi wani kukan kura tayi kanshi tsaye Hisham yayi yanajin yanda take saukar masa bugu tako ina cikin qunan rai iya karfinta sedai ya kasa aiwatar da komai ba ita ba koshi yaji zafin sakin Allah ne shaidarsa ya rasa meyazo kanshi baze iya haqurin rashin zuhraba,cikin qaraji tace

"Dakayi sakin seme Hisham!!! Wace ribar ka qaru da ita? Ta tozartar dani? Kokuma ta wulaqanta igiyar aure? Kayi cuta kana ganin cewar Allah ze barka ne? A tunanin zaka qara zaman nutsuwa da zuhran baya ka kwanta dani?" Dikan qirjinta tayi tace

"Wlhy summah tallahi ni nan dakake gani hisham sena zame maka matar jaraba!! Seka nemeni a lokacin dana maka nisa, sekayi kukan rashina seka tabbatar wa kanka acikin matan ma akwai banbanci,sekayi dana sani mra iyaka! Zaka fara danasani tun daga farkon sanina dakai, zakai dana sanin auren mu abinda zefi komai zamowa babban danasani a gareka shine tarawa dani wlhy kayi ka gama samun gamsuwar kowaceace kuma ni d'in nan nidakai har abada,ka sani hisham dabadan kar Allah ya tsinemun ba dana nemi cikon igiya d'ayan data rage tsakanina dakai shima ka datse mun,kuma ka sani Allah ya isa tsakanina dakai" ta juya zuwaga   zuhrah

"Ke kuma na dawo gareki, wace tsiyar kika tsinana kike gani da kika sanya ya sakeni? Gani kike kamar bazak mutu bane? Kokuma gani kike kamar shima baze tab'a mutuwa ba a duniyar zaku dauwwama? To idan mafarki kike ma ki farka domin kuwa kamar yanda qaddara ta sanya kika kashe mijina mukhtar haka kema dashi qaddara koda ta mutuwar salin alin ce seta riskeku yau ko gobe ko jibi ko wani satin ko wani watan ko wata shekarar ko wasu shekarun masu zuwa badai za'a wuce hakan ba wasu shekarun masu zuwa..... Kuma kamar yanda kika ga mukhtar ya mutu amininshi Hisham ya shuri takalmin sa haka shima hisham ze mutu wata rana yabar takalmin daya shuri yake iqirarin baze rayu ba idan basu  wani ya shura san ransa, ya mora yanda yaso bakuma lallai a riqe masa yanda ya riqe ba wataqil a darenta na farko a wurgo mai takalminsa yanda ya wurgo na waninsa, idan kuma ta Allah ta juye a kanki sekiga kin mutu kin bar qafafuwan dake shuraki matsayin takalmin su masu laushin taki, masu dad'in hawa mafi soyuwa a garesu su shuri wasu takalmin bakida ikon hanawa koki tsinka kamar yanda kikayi yanzu kinaji kina gani ze kuranta wasu takalmin, kinaji kina gami ze yaba wasu takalmi,kina ji kina gani ze d'aga darajar wasu takalmi fiye da yanda ya d'aga ke naki takalmin, wlhy zuhrah akan *auren kwana d'aya tak!!* danayi da mijinki zaki banbance tsakanin so, qauna da sha'awa!! Zaki gano ta inda Ni'imar mace ke janyo mata so had'e da qauna ta har abada, Akan *Auren kwana d'aya tak!!* danayi da kijinki  zaki nemi nutsuwar sa ki rasa  harma da taki,ki sani Akan *Akan auren kwana d'aya tak!!* danayi da mijinki  zaki ga jarabawaowi iri iri wlhy Zuhrah bana miki fatan tsiya kuma idan kina ganin kamar kinci zarafinane to kinyi kuskure domin sana Allah baze barki ba sedai ki sani wlhy zuhra naji zafin wannan sakin kodan mutane!! Naji zafin rabuwar Auren nan sabida inason auren matuqa!! Bana son mijinki ko kadan kuma banso aurarshiba amma daga jiyan dana tare naji ina san auren,amma Alhamdulillah tunda daga sakin naji auren ya ficemun akai" hannayenta duka biyu ta sanya ta tura xuhra baya taje taga taga zata fadi Anty Angel ta tareta ta sake cewa cikin qaraji

"Kije keda Hisham ku cinye juna kuma mujina da kika kashe Allah ya isa, aurena dakika kashe Allah ya isa,ina roqon Allah ya saukar muku da ayar wa'azi me zafi da shiga zuciya" juya tayi gun Anty Angel

"Lallai Angel kin tabbata yaya me hankali, kin taka rawar gani sosai a rayuwar zuhrah Allah ya saka miki da kwatankwa cin abinda kika aikata idan Alkhairi ne kya gani idan sharri ne kya gani, haihuwar biyar kuma da y'ay'a mata kika fara ina fatan Allahu ya sanya yanda kika miqawa Hisham biro da takardar sakina wani ko wata ya miqa takardar sakin 'yarki agabanki ko kyajj kalan azaban da uwata dake kwance qasa zataji" cikin qunan rai ta kalli mommy

"Ke kuma mommy kin cika uwa ta gari me d'aura yaranta saman turbar kirki kema kije ai jikokin ki mata sunfi yawa,kuma yaranki ma akwai mata kema kuma macece bazan gushe ba wurin roqon Allah ya sanya yau d'inan igiyar aurena dakika tsinka naki sufi nawa tsinkewa kuma ki gani a kwaryar shanki!!!"

"Daga qarshe kekuma zuhra, zanta Addu'a Allah ya bani ikon auren ubanki inkuma sanya ya saki uwarki agabanki inci moriyar wulaqancin da kukamun idan hakan bata samu ba ko yau ko gobe ko wata rana zan waiwayeku dukkanku!!! Zan rama daidai gwargwadon yanda kuka cutar dani dukkanku dukkuwa dayake sankn danayi annabin rahma yaana nuni dacewar haqurin Shine yafi..... Daga yau bani baku kuma wlhy zuhrah ko ban auri ubankiba sena auri kijin dayafi naki komai banza dabatasan mutunci ba wacce tai gadon mugun surutu danike da tabbacin shine ze kaita mahallaka!!!.

Juyawa tai da gudu ta koma ciki ta tattare dukkanin abinda ya zama nata na dangane da suturu tabar gidan dama bata yayibo danyawa ba.....mutuwar tsaye dukkaninsu sukayi suna mamakin kalamanta da kuma sanyasu abtunani dukkansu shikamma Hisham kasa cewa komai yayi sabida harga se yanzu kanshi yake saituwa shinma wai tashin farko meze da Mommyn shi? Yasan alwai rigima.

    Ranar da abin ya faru komai Hisham be boyewa daddy komai ba da mommhnshi wannan ya harzuqa daddy har ya yiwa mommy saki biyu abinda be taba shiga tsakaninsu ba kenan,wannan ne ya qara dasa musu qiyayyar nafeesah me tsanani....

**********
*Bayan kwana Arba'in da biyar*

Nafeesah tayi zamanta gidansu inda Allah ya taimaketa ma ta kammala da asibiti se zuwa zancen bautar qasa kuma, dukta gama ramewa sabida baqin ciki abu mafi tashin hankalinta shine rashin komai daga wurin Safwan har wannan lokacin sedai tun bayan mutuwar aurenta ta sauya layi amma tayi tsammanin ko gida ne yazo neman ta ai, daga bisani ta nuna ma zuciyarta dana ai bawata doguwar alaqa bace a tsakaninsu kumama sam shibece yana santaba wataqil yaji labarin tayi aure amma be nemetaba ne dan bata gaya masa ba da wannan ta tattare shi ta watsar!!!! ..

Hisham zaune a parlor gidanshi abubuwa sun masa yawa sam baya gane komai ga mommynshi da qyar ta sakko kuma ko yanzu bata sake mai kamar da gashi kuma wani irin son nafeesah ya taso masa dabesan sanda ya kamu dashi ba sam!!!! Ya gagara zuwa yace ta yafe masa a dawo da aurensu tunda batai idda ba amma bashi da idan kallonta tunda ko a asibiti bata masa magana ko sun hadu! Yana nan zaune zuhra tazo ta sameshi tasomayi wasanni ganin har goma ta gota be shigo ba ta kasa gane wa kanshi akan rashin walwalar dayake da ita da qyr taciwo kanshi ya biye mata amma abin takaici yana amfana da ita sunan Nafeesah yake kira mata wannan shine karo na barkatai ta gayawa Aunty angel amma ta sanar mata wai kartai fada da mijinta asiri ne aka musu kuma ze dna ne!!! Yau abin yafi komai bata haushi ganin yanda Hisham ya dage se sunan  pheey yake kira yana shan yaji tunkan ya qare ma ta tureshi da masifa a haka suka kwana baram baram ita kamma ta gagara bacci se jiyo shi tae a mafarki yana ambatar sunan Nafeesah ta qara tabbatar wa kanta asirin ne dai dole ta nema masa magani!!!!

***"***
Nafeesa ta kammala iddar ta tayi wata rama me ban mamaki sedai ramar ta mata kyau se shape dinta ya qara fitowa jikin yaui daidai da ita gashi tana shirin zuwa camp domin an kirasu kuma lagos aka turata acewarta ma bazatayi relocating ba gwara tae nisa dasu Zuhrah sabida  suna gaf dayi mata sharri tunda mahaifinsu yaqi dawo da uwar su yace tsawon zawarcin dazanyi shi itama xatayi a gidansu!!!

*Lagos Nigeria*

Kwanan Nafeesah Biyar a camp ta nemi pass sabida bazata iya rayuwar camp ba yau dai ta shirya komawa gun yayanta dama can takai shuraim sabida tare suka zo.... Beach suka je yawon shan iska acan sukayi kicib'is da safwan shida matarshi da yaransu uku cikk hadda jinjirar da seda aka fita waje kafin asamu haifota lapia wanda dirarsu kenan Nigeria kusan wata uku basanan suka yanke hukuncin zaman su a Lagos suyi sati d'aya!!! Kallon kallo aka shiga yi tsakanin Safwan da pheey ya nemi layinta harya gaji  baya smu tunda yaci sa'a akayi aikin shamsiya cikin nasara yake neman layinta har yaronsa ya tura gidansu aka sanar masa ranar aka daura mata aure ba qaramin tashi hankalinshi yayi ba se gumi yake had'awa bil haqqqqq duk sanyin wurin har shamsiya ta fahimci  hakan!!

Mom Nu'aiym ce.

SIRRIN MIJINAOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz