Shida

3.6K 334 33
                                    

***

  Alhaji Zailani yana cikin barci sai gabansa ya fadi ya farka na rashin dalili. Hakanan yaji bazai iya barci ba face ya zaga yaga kowa na gidan. Hadiza da Baraka suna kwance gefensa suna razgan barci da sauti na barci yana tashi a hankali.

   Dakin Haske yaje wanda take kwana tareda Fijr, ita tana sama sai Annoba tana kasan gadon. Abin al'ajabi sai gashi babu Haske babu dalilinta. Ƙara haska tocila yayi amma bata wajen. Asalima gefen kayanta babu komai. "Ke ina yar uwarki?" yace da karfin tsiya. Fijr ta farka tana mistike ido. Sake daka mata tsawa yayi mai rikatar wa "Ke nace Shamsiyya ina take?" yadda taga fuskansa babu wasa sai ta soma inda inda.

   "Dama... Dama... Dama"

   "Daman mene? Tana ina ko saina saɓa maki" ya zare mata kyawawan idanuwan sa.

   "Ammi ne tace bazata kwana cikin gida ba saboda tayi mata rashin kunya, kila tana wajen........" bata karasa ba ya arce a sittin ya soma bude kofar falo zai fita. Ita kuma Hadiza taji hayaniya saita fito sanye da rigar barci.

   "yaya dai! Lafiya Naji hayaniya ba'a so muyi barci?"

  Baiko tanka taba sai ya fita abinsa, Fijr na bakin dakinsu tana raba ido, ita ma Hadiza haka. Koda yaje varanda yaga Haske ta kankame jikinta duk sanyi yayi mata yawa tana numfashi da kyar. "Innalillahi"

  "innalillahi" yayita maimaitawa bila adadin.

   Haka ya dauke ta kamar yar tsana ya shiga da ita, kan 3 seater ya ajiyeta duk ta fita hayacin ta. Gaban Ammi ya ɗan faɗi amma saita kanne fuska. Daki ya wuce ya dauko bargo ya lullube ta. Daga nan ya wuce ya duba flask, cikin sa'a akwai ruwa a ciki saiya saka a kwano tareda dauko tawul. A hankali ya rinka shafa mata a fuska da jikinta.

   Dakin tsit baka jin karar komai saina Fridge dake chan kurya yana aikinsa. Ammi tanata dai kallo daga tsaye, tsab batayi nadaman abinda tayi ba. Fatan ta bai fi yace zai mayar da Haske Zaria da zama ba. Wajen minti talatin ana abu daya sai Haske tayi ajiyar zuciya a hankali.

   "Shamsiyya, kina jina kuwa?" yace da sauri.

   "Idan kina ji dan Allah ki bude ido" ya sake faɗi. A lokacin muryansa yayi kauri. Kanaji kasan dab yake da yin kuka. Babu abinda yake tunawa sai Hafsa, ya san cewa bai kyauta mata ba. Ta bar masa amanar yarta gashi ya kasa riƙe wa. Sam ya kasa gane me Haske ta tsone ma Hadiza take gallaza mata haka. Da tun farko yasan zatayi mata haka da wallahi bai aureta ba saboda shifa baya santa ko ɗis. Amma kuma yanzu sunada yara, daya sani yaje ya aure wanda yakeso idan zaa gallaza sai yasan dama bare tayi. Sai dai cikin ikon Allah komai ya kare. Dama talauci ne ya kawo masa wannan abu, amma yanzu komai yazo karshe.

   A hankali Haske ta soma hawaye tun kafin ta bude ido, dogon suma tayi wanda sai yanzu ta farfaɗo. Shafa mata kai da hannun sa yayi na wasu dakikai kana yace, "Na zuba maki abinci?"

    Yunwa na bala'in ɗawainiya da ita amma batajin zata iya ci, bala'in sanyi takeji har cikin ɓargonta. Girgiza masa kai tayi alamun a'a. "Na hada maki shayi?" wannan Karon saita yarda. Ragowar ruwan Flask ya samu kofi ya zuba, saiya saka lipton da siga yakai mata. Taimaka mata yayi ta zauna sannan ta soma sha.

   Hadiza cikin borin kunya ta kama hanyar ɗaki, har ta kusan shiga saita waigo ta kalle Fijr," Kije ki kwanta gobe akwai makaranta karki makara" haka itama ta tafi suka bar wajen. Da kansa ya wuce kitchen ya kunna kettle, sannan daya tausa ya zuba mata cikin bokati yakai mata bayi. . Haka taje cikin 3 na dare tayi wanka. Abin ya bala'in mata daɗi saboda taji dama dama bayan yanda ta jibgu. Baka ganin komai a jikinta sai shedan duka, ga gefen bakinta yayi bala'in kumbura. Sannan idanuwan ta sunyi ƙanana kamar zasu shiɗe.

   ***

   Barci kadan tayi asuba yayi, haka ta tashi tayi sallah wanda kayan Fijr ne Daddy ya ara mata dukda yayi mata girma. Haka ta koma barci saboda ya gargaɗeta akan karta fito balle tayi wani aiki. Abin yayi ma Hadiza ciwo sosai, su suka yi ma kansu breakfast suka fita abinsu. Shima Daddy ya fita wajen bakwai da rabi amma yace ma Haske zai dawo kafin azahar.

Hasken Lantarki (Completed) Where stories live. Discover now