Bata gayama mijinta balle yar uwanta dama ance Expected Delivery Date(EDD) ana yinsa 2 weeks before or after bayan wanda likita yace. Ranar Juma'a sunata kwalema ana gyara kitchen aka wanke duk kwanonin da aka shekara ba'a taɓa ba. Bayan nan sai Hafsa ta koma daki ta kishingida sai Hadiza zata dafa masu abincin rana.
   Ita Shamsiyya tana chan Paki batasan abinda ake ciki ba. Balle dama Ammi dinta na mata gizo saita rinka ganinta sau biyu. Hafsa bata daɗe da kwanciya ba taji ruwa yana binta ta kasan jikinta. Nan ta ƙokarta ta tashi kafin ya gama jika gadon. Tsautsayi ya riga fata sai ya zuba akan tiles aikam santsi yaja ta. Nan ta zame tareda fadi rubda ciki.

   Hadiza karar ihunta tajiyo mai rikitarwa. Nan ta artayo taga yar uwanta malale jini ya fara tsinke mata. Kukan kura tayi tabi titi a sittin domin a kawo mata agaji. Aikam ta samo na annabi inda aka shigo aka kamata aka tafi da ita. Kuma lokacin babu wayar handset sai telephone wanda ba kowane gida keda shiba wajen 90s ake magana.

   Koda aka kai ta asibiti ta zubar da jini bila adadi, tiyata aka shigar da ita inda aka ciro yaro babu rai sabida yanda ta faɗi kansa. Ita kam jini yaki tsaya mata saida ma Hadiza ta bata Leda daya amma a banza. Zailani yayi kuka kamar ranshi zai fita. Saboda yana matukar ji da ita kuma bayaso ya rasata.

   Haka yayi zaman dirshan yanata rizgan kuka babu abinda ya shalle shi da masu kallon sa. Ita ma Hadiza kukan takeyi saboda Hafsa mutum ce mai shiga rai balle uwa uba mahaifan su daya. A takaice bayan la'asar dab da magrib tace ga garin ku saboda nan ta koma gidanta na gaskiya wanda kowane dan Adam yake zaman jiran zuwa.

    Tashin hankalin Zailani saida ya karu saboda nan take ya zube sumamme. Gashi mutanen Zaria basu san da zance ba gari na rashin waya. Cikin haka ne wani za shi Zaria a daren cikin asibiti shine Hadiza ta roke arziki yaje gidansu ya sanar. Koda Zailani ya farka yayita sumbatu yana fisge fisge kamar tababbe. Saida aka bashi gado aka kwantar dashi tareda alluran barci.

***

    Kamar yadda Hadiza taga rana haka taga dare, tana zaune gefen Zailani zugudum abin duniya yayi mata cinkoso. Kwata kwata ranar bataci abinci ba, sallah kam tanayi tana tunane tunane daban daban hankalinta baya jikinta. Kashe gari da asuba yan Zaria suka dauki sammako suka nufa Abuja.

   Ko kafin goman safe suna chan, a lokacin Zailani ya farka. Banda hawaye baya komai. Hadiza ta samu taci abinci sanadiyar yar shegiya dake ɗawainiya da ita ga kuma cikinta yana neman haɗewa da bayan ta. Da suka koma gida mutane makil sai suka sake barkewa da kuka. Tabbas ba mafarki bane Hafsa ta rasu. Anyi mata wanka an mata sutura. Yan uwa sukazo suna mata addu'a tareda fatan dacewa a lahira balle kuma ta rasu ranar Juma'a mai girma.

    Da aka kaita gidanta na gaskiya kashe gari aka tattara karbar gaisuwa chan zuwa Zaria inda duka yan uwa suke na uwa da na uba. Duk abinda akeyi Shamsiyya bata san abinda ake ciki ba. Idan ta biɗa uwarta gurun Hadiza take rashewa abinta. Bayan anyi sadakan bakwai sai aka yanke shawara akan a haɗa auren Hadiza da Zailani balle ma duk duniya babu wanda zai rike shamsiyya fiye da ita. Aikam yaji dadin abin saboda duk wani so dayake ma Hafsa ya karkata zuwa ga Shamsiyya. Duk abinda takeso shi yakeso.

   Sannan kuma aka gargade dangi akan yadda Shamsiyya bata ganewa saboda kuruciya a barshi a hakan cewa Hadiza itace Ammin ta na asali. A cikin wata daya aka daura auren su inda lefe kawai ya sake. Sannan kuma duk wani gado na Hafsa daga kayan daki harna sakawa aka barma Hadiza. Tarewa kawai zatayi a gidan aurenta.

   Maman Zailani ta bukaci a bata rainon shamsiyya idan Hadiza tayi haihuwa na farko saita koma wajen sa duk su zauna. Bazai kyautu ace tana amarya tana raino ba. Zailani bai ji dadi ba amma yasan yau da gobe duk daya ne wajen Allah, wannan kenan!

   Bayan kusan shekara uku...

   Hadiza bata samu ciki da wuri ba saida ta kusan shekara, bayan nan ta samu ciki inda ta haifa yarta fara itama mai suna Fijr. Shamsiyya takanzo masu hutu amma baya wuce na sati daya. Ko sau daya Hadiza bata taɓa nuna ma Shamsiyya wani bambanci ba. Kamar ita ta haifeta take ji. Abin kam ya kara mata daraja a idon Zailani da kuma sauran dangi. Saboda ta nuna hankali da sanin ya kamata.

Hasken Lantarki (Completed) Where stories live. Discover now