Biyu

5.4K 400 12
                                    

***
  Tafsir din Marigayi Sheik Auwal Albani ke tashi a speaker din motar, yana magana akan mutane da suka dauki akidar yahudu da nasara suka rataya akansu babu sassauci. Sannan kuma  idan sun bude baki zasuyi turanci sai kaji tausayin su. Wa'azi ne mai shiga jiki kuma ga barkwanci, a hankali Haske tadan sake jikinta tana darawa sama sama.

   Da suka isa Havilla sai yayi parking motar sa, saida ya gyara zaman rigarsa sannan ya dauko tabaran sa yar yayee ya daura akan fuskan sa. Da murmushi ya kalle Haske sai yace, "Muje ko Madam" a tare duka suka fita suka dunguma shiga wajen, abinka da yamma rana ya sauka duk anzo shan iska. Hankalin mutane da dama a wajen ya koma kansu, sunyi ne iya yi. Yadda Bilal ke tafiya cikin izza kasan wani ne wanda ke juya naira.

   Ita kam Haske ta harde girar sama alamar wannan gayen ta ne yan mata suje su nema nasu. Kamar yadda rana keda haske ya haskaka waje to haka itama takeda Haske. Duk inda ta shiga saita haska wajen, tanada fari mai dauke ido da fata mai santsi lub lub. Farar mace alkaybban mata, faran mace sha kallo. Faran mace zinariya, faran mace HASKEN LANTARKI. Faran mace bakya laifi, Faran mace wata mai tsorata taurari. Faran mace mai sanyaya zuciyar mai kallonta. Full option, steering mota san kowa ƙin wanda ya rasa(afuwan ba cin fuska wajen bakake, kuma naku kirarin na zuwa)

   Sun shiga sunyi oda aka kawo masu, ita Haske Vanilla take so, Laila kuma chocolate shikam Bilal yana shan Smoothie din apple. Bayan sun batar da mintuna kusan arba'in sai suka wuce, bai maida su gida illa wuce gaba kadan Kanti Plus Stores. Shi ya shiga inda ya shiga siyayya kala kala, daga su tarkacen kayan zaki sai su maltina da biscuits. Haka halinsa yake, shi a cewarsa kudi na maganin komai. Idan Kanada kudi ka huta, idan kasha wuya to bakada ko sisi kenan.

   Laila kam kamar zata ara baki dan murna, taji dadi ainun. A duniya tana bala'in san wannan ranar, wai ace Haske Da Bilal sun samu saɓani, zai rinka masu dawainiya kenan. Juma'a mai kyau tunda daga Laraba ake ganewa kuma tabbas yau Laraba ne. Taso tace ya siyan masu Always da Roll on amma kuma saita fasa kafin Haske tace an kawo masu raini. Ita bata ga aibun abin ba kwata kwata.

   Daga nan ya mayar dasu gida watau Gidansu Laila dake Unguwan Shanu Layin Tambuwal. Laila ce ta fita domin ta kira su Baraka kannenta su kwashe kayan. Koda suka zo saida ta gargade su akan kar su kuskura su kai dakin Baaba watau mamanta. Bayan tafiyar ta babu wanda yayi magana. Mintuna 15 ya wuce babu abinda sukace. Shi keta danna IPad dinsa yana dube dube na rashin dalili. Daga bisani ya karkato ya kalle ta.

   "Madam fushin ne" yace cikin izgili. Kakalo murmushi tayi tareda fari da ido, "Fushi name kuma? Ni banida riko malam" saita daga girar ta sama. Shima murmushi yayi sai yayi narai narai da murya. "Amma baby kinsan ke ce silar komai, bakya min abinda nakeso kuma ga stress din aiki sai nayi losing control nayi maki hauka, ki rinka tausayi na mana"

   Batace komai ba, kuma batada niyyar tankawa, asali ma wasa da yatsan ta takeyi kamar bata jiba. Ajiyar zuciya yayi sai yace, "Koda yake ba excuse bane da zaisa nayi maki dibban albarka" a hankali ta kalle shi sai tayi murmushi, a ranta kuma tace gwara ka sani.

   Gyara zama tayi ta kalle shi, kana kallonta kasan babu wasa a tareda ita, "Meyasa idan kamin miss call daya baka sakewa?" sam maganar bai gamshe shiba kuma kana ganin yadda yayi kasan bazai canza wannan mugun dabi'a ba. "But Sweet kinsan haka akida na yake, kowaye duk duniya na kira bai dauka ba bazan sake kira ba, kada ki fara min wannan rigima" yace fuskar sa a daure

    "Kana nufin ban kai ba kenan? Wai tun yaushe muke tare fisabilillahi amma saboda ƙananan girman kanka muyita samun sabani. Ni ce zan zama iyalinka fa? A haka zamu rinka abu. Kullum kayita cewa baka ma mace kaza baka ma mace kaza akan mene? Mata basuda daraja a wajen ka kenan? " mts taja tsaki sai tayi kwafa tareda Kauda kanta. Bai amsa ba saboda ba karya tayi ba. Mata basuda wani amfani wajensa bayan ya biya bukatarsa.

Hasken Lantarki (Completed) Where stories live. Discover now