page 59

2.6K 210 6
                                    

'⋎´✫¸.•°*”˜˜”
..✫¸.•°*”˜˜”*°•.✫
☻/ღ˚•。*♥♥˚˚✰˚˛★*ღ˛°。*°♥。
/▌*˛˚˚.✰ •
/ ˚.★ *˛˚♥*✰。˚˚ღ。*˛˚♥。✰˚
        

                  ❣ *ALK'AWARI*❣
  _Bayan Rai_
     

~August 2017~

© *Hafsat Rano*

*Dedicated to* '''♡Anty Sis♡☆'''

_Vote and Follow mie on wattpad @HafsatRano, My facebook page @Rano Online Novels_

_This page is for U Hafsat Rano Fans group, My Wattpad Fans, Khaleesat Hydar group, Feenat Ja'afar, Qurratul Ayn group, Deeyart Novels and My Facebook group fans, Rano Online Novels.. Lurv u lodi lodi_

☆☆☆☆☆♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡☆☆☆☆

           *59*
Bayan komawar Fav. Uncle da k'wana biu Amaan ta fara labour, cikin ikon Allah bata yi wata doguwar nak'uda ba Allah ya sauke ta lafia..

Kyakkyawar healthy baby gurl ta sunkuto sak Affan. Lokacin da aka gyara ta aka mik'o mata wani irin kuka ne ya k'wace mata, kuka ne me cike da ma'anoni da yawa, Allah me yadda yaso, ga yar Affan a duniya lokacin da ya jima da barin ta, lokacin da suka fi buk'atar sa Allah ya d'auke abun sa, addu'ar samun rahma tayi masa tare da addu'ar Allah ya raya ya albarkaci abinda ya bari..

Tare suka shigo Mammy na gaba Fav. Uncle na take mata baya, murna da tsantsar farin ciki ne shinfid'e akan fuskar su, d'aukar jaririyar sukayi suna kallon ta gwanin sha'awa.

"Kin ganta sak ni ko Mammy...?" Fav. Uncle ya furta yana sakin murmushi..

Tabe baki tayi alamar wasa tace,

"Ko ma dae menene nice dae ta k'arfen.." bushewa Fav. Uncle yayi da daria, zae bata amsa kenan wayar sa ta d'au sowa. Haka ya dinga amsa waya, wata na kashe wa wata na shigowa duk daka Nigeria,  Mummy, Hajja, Mama, Abba, Farida, Na'eem da sauran yan uwa sae da suka kira cikin farin ciki..

Number Omar mijin Jalila ya k'ira ya sanar musu da haihuwar, a take suka kira Saudia suka sanar dasu Ummi..

☆☆
Ana yi saura k'wana biu suna su Mama suka duro, ansha artabu da Hajja akan shiga jirgi, tun wani zuwan ta saudia bata k'ara yadda ta shiga jirgi  ba saboda bala'een tsoron da take masa, sae yanzu, ga tafia ba kusa ba , sau uku tana sakin fitsari a wando, kashi sau d'aya.. kafin azo birnin london ta zabge sosae bakin ya mutu murus..😂Lol

Amaan kamar sallah haka take ji ganin yadda kowa ke farin ciki, Mummy kamar ta cinye little baby Afnan wanda Fav. Uncle yayi mata hud'uba dashi tun ranar data xo duniya.

Washegari Sae ga Ummi Jalila da yaranta, Omar
be sami damar zuwa ba saboda aiki.. Gida ya k'ara cika sosae, Farida bata samu damar xuwa ba itama saboda d'anyen jego data ke wanda ta samu Baby Boy One month before haihuwar Amaan.. kamar ta had'iyi zucia ta mutu haka taje ji bini bini ta bugo waya..

Su Ummi ma basu sami damar zuwa ba saboda jikin Abby yak'i dadi sam, haka suka had'o kayan arzik'i Ya Muhassin ya kawo..

Ranar suna anci an sha an kashe kud'i, manyan abokan Fav. Uncle turawa sunxo da Familyn su, abu gwanin sha'awa. Sae da komae ya lafa ne Amaan ta shiga d'aki tayi kuka sosae, kuka wanda ta dad'e bata yi irinsa ba, a haka Umminta Jalila taxo ta sameta, bata baki tayi ta nuna mata yadda ta k'addara, sae data ga tayi shiru sannan ta fita ta barta..

☆☆
*A year later*

Abubuwaa da yawa sun faru, daka ciki harda auren Rahmata da Habu, Nafi da Is'hu d'an k'walisa , wanda suka jone daka baya..

ALK'AWARI BAYAN RAI (Completed✅)Where stories live. Discover now