page 32

2.8K 246 21
                                    

'⋎´✫¸.•°*”˜˜”
..✫¸.•°*”˜˜”*°•.✫
☻/ღ˚•。*♥♥˚˚✰˚˛★*ღ˛°。*°♥。
/▌*˛˚˚.✰ •
/ ˚.★ *˛˚♥*✰。˚˚ღ。*˛˚♥。✰˚
        

                  ❣ *ALK'AWARI*❣
  _Bayan Rai_
     

~August 2017~

© *Hafsat Rano*

Edited by; miss xoxo👑

*Dedicated to* '''♡Anty Sis♡☆'''

'''Late is better than never'''
*Happiest Birthday Mss Xoxo👑, May Allah blesses ur New Age, with Iman.* Ameen.

☆☆☆☆☆♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡☆☆☆☆☆

           *32*
"Whats wrong with mie ne?" Ya tambayi kansa yana kallon screen d'in wayar da kiran Affan keta faman shigowa, haushi gaba d'aya yakeji, kara kashe wayar yayi a karo na biyu ya d'ora ta akan kujera ya shige cikin d'aki. Ruwa ya sakar ma kansa ya shiga cikin gashin sa sosae, ajiyar xucia ya sauke ya fito bayan ya chanja kaya ya koma d'akin Hajjan. Magana be ma kowa a falon ba ya wuce zuwa ciki. Zama yayi gefen gadon kamar me gadi yana ayyana abubuwa kala kala. Yanayin fuskar ta da kalar fatar ta kawae yake kallo, tun sanda ya fara ganin ta a hotel yaji wani abu game da ita, haushi ne ya kamshi da ya tuno a hotel d'in daya ganta har tana karbar kud'i yar karamar yarinya da ita, tsaki yayi da karfi wanda ya jawo ta fara kokarin bud'e idon ta. A hankali ta bud'e idonta ta tsura ma P.O.P d'in d'akin ido, ba tare da ta kalli gafen ta ta sake maida idonta ta rufe don har lokacin allurar bata sake taba.

☆☆☆☆
Affan ya fito ya sami Mummy tana zaune,

"Mummy zanje wajen Aman, ina ta kiranta bata picking karshe ma gaba d"aya aka kashe wayar."

"Ayya amma ya kafarta ka a haka zaka fita?" Mummy ta bashi amsa tana kallonsa.

"Inaji a jikina kamar something is wrong,shisa xanje."
"Owk Allah ya tsare, ka kula sosae kaji? Ka gaishe ta." Fita yayi yana taka kafar a hankali ya d'au mota ya fice.

A cikin gidan ya tarar da Farida da wani a tsaye, tana ganin sa ta tawo wajensa bayan tayi excusing kanta daka wajen shi.

"Ya Affan sannu da zuwa."
Gaisawa sukayi anan take fad'a masa Aman batajin dadi,
"Amma bari na fad'a ma Hajja sae ka shiga ka dubata.
"Owk." Yace ya karasa wajen saurayin dake tsaye ita kuma ta nufi ciki don sanar ma Hajja. Gaisawa sukayi da saurayin me suna Amjad, d'an introduction ya biyo baya inda yake sanar ma Affan shine zae auri Farida, da tuni anyi bikin ma sae suka tafi Germany nemar ma Baban sa lafia, hakan yaja aka d'aga biki.
"Ya salam, Ya jikin baban?"affan ya tambaya.
"Ah alhamdulillah ya sami sauki, dama kidney ne kuma an cire ta ma, He's sound and healthy yanzu kawae biki zaa sha."

Murmushi Affan yayi yace;
"Allah ya sanya Alkhairi." Ameen ya amsa cikin zumud'i, exchanging number sukayi, a haka Farida ta dawo ta samesu, gaba tayi Affan yabi bayanta yana jinjina saurin sabo irin na Amjad.

Hajja ansha lullubi aka irin suruki zai shigo, ta gefen ido take satar kallon sa, wanda duk koyarwar Farida ce don tsaf zata kunyata su. Tsugunawa yayi har kasa ya gaishe ta, sannan ya tambayi mai jiki.

"Da sauk'i, zazzabi ne da ake fama dashi, Farida rakashi ciki ya ganta don bana jin ta tashi.'
Cikin d'akin Hajjan Farida ta kaishi, to her most suprice Ya Farhan na zaune gefen gadon yana sak'e sak'e, jin an shigo ne yasa shi saurin d'agowa, karaf suka had'a ido da Affan, kicin kicin yayi da fuska yana mashi wani irin kallo, shi kansa Affan sae da yaji gaban sa ya fad'i, dakewa yayi ya karasa gaban gadon yana kallon Aman dake kwance tana barcin ta cikin kwanciyar hankali.

A hankali ta bud'e idonta ta sauke su akan Affan dake tsaye, murmushi ta saki me kyau don dama mafarkin sa take a lokacin, Idon Farhan na kansu kamar ya kurma ihu,  kamar me rad'a Affan ya furta,

ALK'AWARI BAYAN RAI (Completed✅)Where stories live. Discover now