page 21

3.1K 232 1
                                    

'⋎´✫¸.•°*”˜˜”
..✫¸.•°*”˜˜”*°•.✫
☻/ღ˚•。*♥♥˚˚✰˚˛★*ღ˛°。*°♥。
/▌*˛˚˚.✰ •
/ ˚.★ *˛˚♥*✰。˚˚ღ。*˛˚♥。✰˚
        

                  ❣ *ALK'AWARI*❣
  _Bayan Rai_
     

~August 2017~

© *Hafsat Rano*

Edited by;
Miss xoxo👑

*Dedicated to* '''♡Anty Sis♡☆'''

☆☆☆☆☆♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡☆☆☆☆☆

           *21*
Lokacin da suka k'arasa station Affan har ya gaji da dialing number Daddy ya hak'ura, text messege ya tura masa.

Abinda ake tuhumar Nana akae aka karanto masu, duk jikinsu yayi sanyi don sunsan anyi haka,  itama gwanar bata wani musa ba, zancen da ya d'an girgiza su shine su kansu yaran data sa aikin basu san ina Aman tayi ba, ita Nana umarnin suyi nisa da kano da ita kawae ta basu amma banda cutarwa. Zufa ce kawae ke faman keto ma Affan, a farkon jin case d'in har ya fara hamdala yana da yak'inin anga Aman an gama.

Farhan ne ya shigo station d'in bayan ya karb'i wayar D.P.O akan sune nemansa.
Direct Office d'in ya wuce yana takunsa cikin nutsuwa yana fatan tozali da yarinyar da zata iya aikata irin wannan abun.

Murd'a k'ofar yayi tare da sallama, turus yayi ganin Mummy da Affan zaune kan kujera sae Nana wadda ta juya bayanta tana tunani.

"K'araso Mana Mr Kurfi". D.P.O ya fad'a yana masa nuni da kujerar dake gefen ta Affan.

Zama yayi ya mik'a ma Affan Hannu da D.P.O sannan ya gaida Mummy.

Sae a sannan Nana ta d'ago da sauri jin muryar sa, daidai lokacin shima ya kai kallon sa b'angaren da take yana bin bayanin da D.P.O yake masa.

"Wannan ita ce yarinyar da tasa gangs d'in aiki har aka samu akasi suka yi maka illah."

Ras ras ras gaban sa ya fad'i, "Nanaaaa", Ya furta chan k'asan mak'oshin shi, abubuwa da yawa suka shiga  yi masa yawo akae. Tunanin farkon had'uwar su yake da lokacin da yaje gidansu, maganar da Baba Maigadi yayi masa. Duk a tunanin sa Nana irin mutanen nan ne wanda sam basu damu da rayuwar kowa ba, be tab'a tunanin zata aikata irin wannan stupid act d'in ba.

Ganin yayi shiru ne yasa D.P.O ya sake maimaita maganar sa, sae a sannan Farhan ya maida idonsa kan D.P.O yace;

"I ll leave everything to u, duk abinda kukayi akae shikenan, one thing dana sani shine su fad'i ina yrinyar mutane take, dalilin ta na k'ok'arin salwantar ko kuma ma ta salwantar da rayuwar yarinya. As for my own part na hak'ura na janye"

"Sorry Mr Kurfi, ko ka hak'ura hukuma bazata hakura ba".

Mik'ewa kawae yayi kansa yana masa wani juyi ya sake gaisawa da Affan sannan ya fice.

Kicib'is sukayi da Daddy yana k'ok'arin shiga kamar zae hantsila, hanya ya bashi ya wuce masu biye masa baya suka tsaya a k'ofa.

Ganin Daddy yasa D.P.O mik'ewa da sauri ya bashi hannu, da kyr yayi convincing Daddy ya zauna in da Affan da Mummy suka fice waje suka zauna suna maida maganar.

"Affan kaga abinda nake jima Nana ko?Wannan wacce irin rayuwa ce."

"Karkii damu Mummy komae jarrabawa ce daka Allah, na tabbata Alhakin y'ay'an wasu ne ya fara kama Daddy. Gashi gayen chan ya bada points masu kyau, ya kamata a san in da suka kai Aman

"Haka ne Affan, Amma kasan me? Yaron nan shine wanda Nana ta fara shiryuwa saboda shi, son sa take sosae Affan, kana ganin yanzu zae dawo mata ne? Kana ganin ance fa sanadiyar shashancin ta har ya nemi rasa idanun sa, fisabilillah Affan Kana ganin zae cigaba da Son mace Irin Nana"? Cikin muryar Kuka da tsantsar takaici Mummy take magana.

ALK'AWARI BAYAN RAI (Completed✅)Where stories live. Discover now