page 13

3.2K 248 0
                                    

'⋎´✫¸.•°*”˜˜”
..✫¸.•°*”˜˜”*°•.✫
☻/ღ˚•。*♥♥˚˚✰˚˛★*ღ˛°。*°♥。
/▌*˛˚˚.✰ •
/ ˚.★ *˛˚♥*✰。˚˚ღ。*˛˚♥。✰˚
        

                  ❣ *ALK'AWARI*❣
  _Bayan Rai_
     

~August 2017~

© *Hafsat Rano*

Edited by _Aunty miss xoxo👑_

This page is for U *Aunty Fauza* Ban manta dake ba.. Thanks Allah ya bar zumunci

*Dedicated to* '''♡Anty Sis♡☆'''

☆☆☆☆☆♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡☆☆☆☆☆
   
           *13*

Shigar Safiya Alhaji yayi., Cikin dare Nana ta kira sa akan Mummy da Ya Affan suna blaming d'in ta akan aikin da ya sata.

Ko takan mutanen dake masa sannu a k'ofar gida beyi ba, afujajan ya shiga gidan.

Mummy ce zaune kan Sallaya tun asubah bata tashi ba, karatun Al'qur ani me girma take. Kamar daka sama Alhaji ya fad'o d'akin fuskar nan a murtuke.

K'arasa kai Aya tayi sannan ta rufe Alq'uranin..

"Sannu da zuwa Alhaji." Ta fad'a tana mik'e wa.

Yanayin Fuskar sa kad'ai ta gani tasan ransa a b'ace yake.

Cikin ko in kula ta wuce zuwa k'arshen gado ganin bashi da niyyar amsa mata.Ta rigaa tayi making mind d'in ta koma mene yaxo dashi ta fishi.

Hakan da tayi ne ya k'ara k'ular dashi. Tsaki yayi ya k'arasa closet ya shiga cire kayan sa.

Sae da yayi wanka ya shirya sannan ya sauko zuwa parlor.

Mummy ce zaune da Affan suna k'ara tattauna abinda ya faru, kallo d'aya zaka ma affan ka gane irin ramar da yayi daka jia zuwa yau.

"Ehmm Ehmn"...Yayi gyaran Murya. Kallo d'aya Mummy tayi masa ta kauda kai don tasan abinda yake nufi.
Affan ne ya gaida sa amma maimakon ya amsa sae ya basar ya nemi wuri ya zauna..
Cikin kakkausar murya ya fara magana;

"Naji duk irin abunda kuke k'ok'arin yi while bana nan, inason nayi warning d'inku, to stay out of it. Ni na bata dama and beside yarinyar deserves what she got. Kai kuma sokon banza yarinya ta mari ubanka amma kana claiming wai sonta kake. To hell with son naka"Ya fad'a yana nuna finger nashi akan Affan.

Duk cikinsu ba wanda yayi magana, hakan ya k'ara k'ular dashi, kafin yayi magana sae ga Nana ta fito janye da trolly nata. Sanye take da Lazy Sunday Outfit Red and Black. Sae wani veil silk black tada d'aura.

Ajiye trolling tayi a gefe ta k'arasa kusa da Daddy ta zauna.
Da murmushi a fuskar sa yake dubanta.
"Mamana har kin fito kenan?"
A dak'ile ta amsa wai ita a lallai ranta a b'ace yake.

Mummy ce ta mik'e zata haura sama Daddy ya dakatar da ita.
"Hajiya ina zaki kuma? Ban gama magana taba ai"

"Ina da abubuwan yi da yawa". Ta bashi amsa tana cigaba da tafia.

"I told you dama Ai, Mummy sam bata sona wlhi, bansan mesa ba, komi Affan Komi Affan. Anya kuwa ma ita ta haifen Daddy?"

Wani bak'in ciki ne ya kama Mummy tana k'arasa hawa last step, kamar ta juyo tayi magana sae kuma ta fasa.
Allah ya gani ta gaji da ganin Nana a wannan halin, dole ta san yaddaa zatai in ba haka ba tana kallo zata kasa auruwa.

Affan kua kamar ya had'iye zucia ya mutu don bak'in ciki, yana nan zaune har suka fice ita da Daddy don yayi mata rakiya, yana jin tashin motar ya mik'e ya wuce d'akin sa.

☆☆☆☆
A hankali ya shiga bud'e idonsa wanda yake jin kamar an zuba musu barkono. Daya bayan d'aya yake bin d'akin da kallo yana son tuna abinda ya faru dashi.
Last scene d'in incident d'in kawae ya iya tunowa, kansa yaji ya masa nauyi. Daidai lokacin Doc ya shigo tare da nurse.
"Wellcome back Mr Farhan Kurfi." Ya fad'a yana daria.
   Murmushi kawae yayi masa kasancewar duk jikansa cio yake masa.

Aune aune yayi masa , ganin komi normal sae bruises da ya rage suyi healing, wannan kam sae a hankali.

Fita sukayi, anan kaf family suka sami damar shigo wa, nan nan kawae ake dashi, while shi kuma mind nasa was somewhere else, tunanin sa kawae gangstars d'in jia. Face d'insu da kuma  innocent face d'in yarinyar shi ke masa yawo a zuciya. Her face seems familiar to him. Kamar ya santa a wani wurin.

Next day police suka xo don yi masa tambayoyi, iya abinda ya sani ya fad'a musu. Babban Architect aka d'auka Farhan ya bada describtion d'in face na ogan su, ba wuya ya zana shi sosai kamar ya ganshi. Godia police sukayi masa sannan suka juya suka fice, shima Architect d'in ya juya zae fita Farhan Ya tsaida shi.

"Inason na k'ara maka wani describtion na wata yarinya da nake son ka zana mani."
Ba musu ya ajiye kayan sa ya shiga zane. Sam Zanen be yi kama da Aman ba coz be wani ga face nata full ba a motar sae d"an abinda baxa'a rasa ba. Karb'a yayi d'auke da murmushi sannan yace ya karb'i bill nasa wajen Na'eem dake waje dasu Abba...

Kwanan sa uku aka sallame sa, suka rankaya zuwa gida.

A falon Hajia aka baje ana ta maida zance.. Hajia ce ta shiga tsokanar sa
 
"Kai dama rago ne ashe?aikuwa na fasa auren dakai wlhi, gwara na lallab'a na'eem d'in muyi abunmu ko Na'eem?"Ta fad'a tana daria

"Ahh haba Allah ya kiyaye ni ai sae yarinya sabuwar jini"Na'eem ya fad'a yana mata gwalo

"Mutan gidan ku ja'eeri"Ta wurga masa throw pillow. Gaba d'aya aka kwashe da daria..

☆☆
Satin Farhan biyu ya warware sosae, face nashi ne dai akwae tabo sosae, musamman side d'in idon sa na dama. Yayi bak'in ciki don a ganin sa ragewar class nasa ne, musamman wajen yan mata irin su Nana Boss...
Summer Dark Glasses ya nema ya fara sawa. Ranar kuwa hajia  daria kaman ta kashe ta don har cewa tayi ya nemi d'an jagora. Banza yayi mata ya fice zuwa unguwar su Nana Boss..

Ko da ya isa mai gadi ya sanar dashi yau ma batanan tayi tafia, mamaki sosae ya kamasa ganin cewa yawon nata yayi yawa a matsayin ta na mace, sae dai yanayin ta kawae ya isa ya nuna wacece ita. Ya rasa dalilin da yasa kawae take burgesa.

Jiki a sab'ule ya bar kofar gidan bayan ya cika me gadi da kud'i.

Direct Office ya wuce ya d'an taba aiki sannan ya duba schedules na flight d'in gobe. Deciding yayi na zuwa lagos gobe, a take ya gama dukka arrangement na tafiyar.

☆☆
Nana zaune gaban mak'ek'en pool cikin gidan shak'atawar dake Victoria Island. Jefi jefi take kallon wajen yanda mutane suke al'amuransu kamar baza'a mutu ba.
Tsaki tayi, ta jawo robar swan ta kafa kai , sae data shanye tas sannna ta sauke kanta tana ajiyar zuciya.

Tunanin Aman da Farhan ne ya dame ta, duk lokacin data rufe ido sae ta ganshi, ita kuma sam babu ma tsarin soyayya a rayuwar ta. Courage d'in gayen ne kawae ya burgeta amma bawai kyawun sa ba.

D'ayan side d'in zuciyar ta kuma regretting Abinda tama Aman take, fuskar yarinya so innocent.

Kara tsak'i tayi a karo na biyu bayan ta mik'e, ganin zaman ya isheta yasa ta wuce garden d'in wajen ta fara zazza gaya wa har wajen magrib sannan ta koma gida..

Washegari Farhan ya shirya ya wuce zuwa lagos.

Yau ma Nana ta fito zuwa gidan shak'atawar, tana zaune cikin mota kamar Ance Farhan ya juya, da mamaki ya bita da kallo ganin wadda beyi expecting gani ba, ba b'ata lokaci yabi bayanta. A zaune ya tadda ta kan wasu purple kujeru..

Sae da ya zauna, sannan ta d'ago tana dubansa, tsaf tasan yana binta tun a hanya. Take idonta ya sauka kan cion dake gefen side d'in idonsa, kallon sa tayi kamar bazata d'auke idonta ba, shima kallon nata yake. Rama sosae taga yayi dukda ba wani kallon k'urilla ta tab'a masa ba.
For the first time taji slight bit na tausayi a ranta. Shiko Farhan ganin yanayin da ta shiga yasa shi sake gyara zama.

Zuciyar ta ce ta tuno mata pride d'inta. Take ta murtuke fuska don kar ya gano weakness nata, mik'ewa tayi ta bar wajen da sauri.

Manage this pls.......
Mura wan kill mie a agazo da farfesu me yaji fulis🤢

Rano❣

ALK'AWARI BAYAN RAI (Completed✅)Where stories live. Discover now