page 39

2.6K 208 3
                                    

'⋎´✫¸.•°*”˜˜”
..✫¸.•°*”˜˜”*°•.✫
☻/ღ˚•。*♥♥˚˚✰˚˛★*ღ˛°。*°♥。
/▌*˛˚˚.✰ •
/ ˚.★ *˛˚♥*✰。˚˚ღ。*˛˚♥。✰˚
        

                  ❣ *ALK'AWARI*❣
  _Bayan Rai_
     

~August 2017~

© *Hafsat Rano*

Edited by; Miss Xoxo👑

*Dedicated to* '''♡Anty Sis♡☆'''

This page is for U my one and Only Lil Momma, Aunty Maryam *(Maryam Ahmad Arab)* Uwar gda Amarya  a gidan  Yaya *(Alhaji Rabi'u)* M head over hills inlurv wit U😍❣

☆☆☆☆☆♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡☆☆☆☆☆

           *39*
Da sauri Na'eem ya karasa gaban gadon yana jijjiga shi, ganin ba motsi yasa shi saurin ciro wayar sa ya shiga kiran number Dr Bilal, cikin mintuna kad'an ya karaso, lokacin Abba da Na'eem na zaune gaban gadon, gefe suka matsa ya shiga aune aunen sa, ajiyr zuciya ya sauke yana duban Abba;

"Dogon suma yayi wanda sanadiyar shock d'in daya shiga ne, Alhamdulillah zae iya farfad'o wa anytime."
"Alhamdulillah." Abba da Na'eem suka furta a tare, falo suka koma Dr Bilal  yayi ma Abba bayani sosae akan rashin lafiar Farhan d'in. Goge zufa Abba yayi bayan jin abinda Dr Bilal yace,

"Shikenan zan san yadda zanyi Dr, nagode sosae." Daukar first aid box d'in sa yayi ya juya ya fice daka falon.

"Abba dan Allah ka sanar dani damuwar bruh ko zan iya wani abu akae." Na'eem ya fad'a yana kallon Abba, girgiza kai kawae Abba yayi ba tare da yace komae ba ya fice daka part d'in.

☆☆
Shirye shiryen biki sosae ake from both side,Farida da kawayenta sune akan komae, Sun fitar da anko me kyau na dinner da kamu, sae mother's eve wanda Hajja ta shirya zata gayyato tsofaffin kawayenta daka Kurfi, anko itama tasa aka fitar atamfa ta aika musu dashi, farin ciki wajen Hajja ba'a magana. Ranar jumma'ah suka shirya suka tafi Mad'achi don tawo wa dasu Rahmata, Amjad ne ya kaisu yana ta santin kauyen, Rahmata da Nafi farin ciki kamar su goya su, da daddare suka shirya suka nufi dandali, sosae abin ya burge Farida, su Is'hu da jama'ar sa ma an hallara ana ta k'wambo ansha tabarau, Farida ce ta sake suna ta hira tana fasa masa kai, sae da suka gama kwasar daria sannan suka wuce gida.

Kwanan su biyu a garin, sun sha madara sosae fresh.
Ranar da zasu tafi, Gaji tasa aka kawo musu da yawa su tafi da ita bayan ta jaddada musu muhimmancin ta.

Affan ne yazo d'aukar su bayan ya biya ta kibiya ya d'auko Habu.
A hanya Habu yana ta tsokanar Aman taki cewa komae, ta mirror suka had'a ido ta Affan ya kashe mata ido d'aya, d'auke kanta tayi tana murmushi kasa kasa, chan ta kara d'agowa ta kalli cikin mirron, a hankali ya furta *I Lurv U* runtse idonta tayi da sauri tana jin wani abu, kasa d'aga kanta ta kuma yi har suka shigo kano

☆☆☆
A jiyar zuciya ya sauke yana kallon Abba, mik'ewa yayi a hankali ya nufi toilet, ya dad'e zaune yana watsa ma kansa ruwa, sannan yayi wanka ya fito. Doguwar jallabiya fara ya jawo ya zura ba tare da ya shafa mai ba ya fito zuwa harabar gidan, ba kowa kasancewar yamma ce, hakan yasa ya k'arasa gate ya sami gefen bench d'in gate man ya zauna. Yana nan zaune yana dannan wayar sa a hankali, yawanci sakonnin Nana ne, tausayin ta sosae ya keji ganin halin da ya shiga, yasan tabbas soyayya ba abar wasa bace, ko ba komae zae cigaba da kulata, ko dan son data ke masa, dama shi chan ba tsanar ta yayi ba. Motar Affan ce ta shigo gidan, wani irin matsanancin fad'uwar gaba yaki, a take ya fara karanto duk addu'ar data zo bakinsa, sosae yaji sauki a ransa, suna gama parking Aman ta fito da sauri ta nufi in da yake,

"Ya Farhaaaan.." taja sunan nasa tana kare masa kallo, murmushi ya sakar mata me kyau yace,

"Naam Sis." Kallonsa kawae take da mamaki, ganin irin muguwar ramar da yayi lokaci daya shi yafi d'aga mata hankali, mik'ewa yayi yana nuna mata bayanta,

ALK'AWARI BAYAN RAI (Completed✅)Where stories live. Discover now