page 10

3.1K 238 3
                                    

'⋎´✫¸.•°*”˜˜”
..✫¸.•°*”˜˜”*°•.✫
☻/ღ˚•。*♥♥˚˚✰˚˛★*ღ˛°。*°♥。
/▌*˛˚˚.✰ •
/ ˚.★ *˛˚♥*✰。˚˚ღ。*˛˚♥。✰˚
        

                  ❣ *ALK'AWARI*❣
  _Bayan Rai_
     
    
~August 2017~

© *Hafsat Rano*

*Dedicated to* '''♡Anty Sis♡☆'''

☆☆☆☆☆♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡☆☆☆☆☆

_Afwan da rashin post on time, waya tace sae a slow wlhi.._

Ina Kuma yi maku Barka da sallah dafatan anyi sallah lapia?! To Allah ya maimaita mana Ameen🙏🏽

           *10*
Kallon ta yake fuskar sa d'auke da murmushi. D'auke kanta tayi daka kallon sa ta k'ura ma bedsheet d'in dake kan gadon ido. Mik'ewa yayi ya karaso zuwa gaban gadon yaja ya tsaya.

"AMAAAAN"
Ya kira sunanta cikin wani irin salo. 'D'ago kanta tayi ta watsa matsa idanun ta kamar me jin barci, kasa kallon k'wayar idonsa tayi hakan yasa tayi saurin maida kanta k'asa.
Murmushi yayi me sauti yace;

"Ina son mace me kunya a rayuwa tah"
Shiru bata tanka ba, hakan ya bashi damar cigaba
"Tun farkon dana fara ganin ki ranar dana dawo naji wani irin yanayi game dake.. I feel kamar akwai wani bond tsakanin mu..  Irin protection d'in da Mummy take baki ne yasa na gane akwae wani abu on ground. A hankali na rink'a bin komi har na gano abun takaicin da Daddy da Nana ke shirin aikata maki"

"Daddy!"Ta nanata a zuciar ta, "yana nufin Alhajin nan mahaifin sa ne kuma a gidan take zaune?"

"Ina son nayi amfani da wannan damar na  baki Hak'uri, lalle akwae zalinci sae dae mahaifi na ne babu yadda zanyi dashi"

Sae a sannan ta gama fahimtar inda maganar sa ta dosa.

Da har tana tunanin ta samu hannu na gari ashe ma bata fita daga cikin gidan ba..

Katse mata tunani ya k'arayi.. Sae da ya gama jawabin sa tana jinsa, sam ta kasa gane abunda ya kamata tayi.. Jin yayi shiru ne yasa ta gane yakai full stop.

Dagowa tayi ta kalle sa har lokacin yana tsaye a kanta yayi folding hannayen sa.
Kok'arin nemo courage tayi sannan ta shiga magana;

"Nagode sosae da irin karamcin ka dana Mummy, Allah ya baku abinda kuke so, Alfarma d'aya nake nema don Allah"

"Wacce Alfarma kenan?"Ya tambaya

"Ka fitar dani daga gidan nan, inason na cigaba da neman dangina"Ta fad'a a hankali.

"Zanyi iya kokari na ganin kin samu abinda kike nema, for now ki cigaba da zama anan, ki kula da kanki. Xan dawo anjima around 11pm haka mu karasa tattauna wa"

Murmushi tayi masa me sauti sannan tayi godia. Waving nata yayi ya nufi k'ofa..

☆☆
"Kan bala'ee"Nana ta ambata bayan ta gama jin komi.

"Amma gaskia Mummy Oga ce, wato ita ce tai ruin plans d'ina.. Hmmm nasan me zanyi"
Jin za'a bud'e kofar yasa ta juya da sauri ta haura sama.

☆☆☆☆☆
Sanye take cikin Rock Chic Outfit Purple and black.. G ashin ta ta kama da purple ribbon, sannan ta kawo Polka Dot Cap black ta saka, Hip Star Glasses ta dora akan kyakkawar fuskar ta.. Sosae tayi kyau sae dae fuskar nan kamar ta Daru😝. Ba fara'a

Cikin takun kasaita ta sauk'o, kamar gaske ta gaida Mummy da fara'a sannan ta juya wajen Affan.

"Morning Sweet Bruh"
"Morning kanwata nana gayu sae ina kuma??"
" Zanje NYSC Office ne."
"Lalle, amma me makon ki ma Daddy magana yayi waya kawae, ai basae kinje ba ko? "
"No inason xuwa da kaina ne shi ya sa, and beside Ba wani dade wa xan ba.. C U Bye"

"Bye.."Ya bata amsa ya cigaba da abinda yake.

Ko sallama bata ma Mummy ba , balle neman permission zata fita , kawae waving hands nata tayi ta fice..
Cikin motocin dake jere ta zabi d'aya
Ta fice a 360.

Sultan road ta nufa direct, kofar wani gida ta samu waje tayi parking.
"M out"Kawae ta fad'a ta sauke wayar.

Gaban motar ya shiga ya zauna.. Like 20min suka d'auka suna magana sannan ya fita ita kuma taja tayi gaba abunta..

Direct gida tayi, da mamaki Mummy ke dubanta ganin yau wacce rana ta fita ta dawo da wuri haka.

Zama tayi ta shiga jan su da hira, gaba daya hankalin Mummy da Affan yana kan Aman amma Nana ta kafa ta tsare.

Ita kuwa gogar Tana lura dasu, amma sam tak'i barinsu.. Wunin ranar sallah ce kad'ae ke tashin su, da an mik"e sae tace Ya Affan yaja su sallah. Hamdala Mummy tayi a ganin ta Nana ta fara hankali..

Har akae magrib tana manne da MUmmy suna kitchen. Ganin tak'i barinsu yasa Affan shirya wa ya bar gidan.

Da aka zo kwancia ma sae data raka Mummy d'aki ta dawo  falo ta cigaba da kallonta..

Wajen 11pm wyarta ta fara ringing. Ganin number yasa ta mik'e ta sauka balcony.

"Alright ku shigo kawae naji tace ta kashe wayar"

K'arasa wa gate tayi ta umarci Baba me gadi ya bud'e tana da bak'i..
Su uku ne maza..
Direct Parlo ta wuce dasu, d'akin Aman ta k'arasa tayi knocking

Tun d'axu dama take expecting zuwan Affan, zaune take tana shan Lemo da ragowar bread da aka kawo mata da safe..

Da hanzari ta mik'e, ba tambaya ba komi ta zare lock, ja da baya tayi ganin Nana tsaye da maza Uku. Kafin tayi aune d'aya ya toshe mata baki ya shiga janta,  da haka har suka fice da ita..

Tura ta sukayi a mota sannan D'aya daga ciki ya d'aga hannun sa alamun sarawa yana kallon Nana. Sara masa tayi ita ma suka ja suka fice ita kuma ta juya gida..

Daidai lokacin Affan ya shigo cikin link d'in nasu yaga mota ta fito daga gidansu. Be kawo komae ba a tunanin sa Nana ce.. Girgiza kai yayi kawae ya danna horn.

Mamaki ne ya kamashi ganin Nana a zaune tana kallo. To ko kuma jama'ar Daddy ne? Amma ai Daddy baya nan..

"Su waye naga sun fita yanzu a mota?"Ya jefa mata tambayar yana kokarin cire takalmin k'afar sa.

"Bak'i na ne."Ta amsa masa a tak'aice ta tashi ta nufi sama.

Tabe baki yayi "Yarinya kamar me aljanu daxu normal da ita amma ji yanzu"Mtsww ya fad'a yana gyara zama.
Sae daya tabbatar ta kwanta sannan ya nufi d'akin da Aman take ciki da murnar sa... Waya ga wayam😆

Manage dis xua anjima kadan .

Rano💃🏻💃🏻

ALK'AWARI BAYAN RAI (Completed✅)Where stories live. Discover now