********
       *Lagos 8:38pm*
     Daddy ne ya shigo gida da sallaman shi, kowa ya kalli fuskan shi yasan yana cikin nishadi da jin dadi. Islam ce ta amsa mai sallaman da yayi tareda da cewa "Daddy welcome" ,"tnx my dear, ykk, ina Momsie dinku" ,"lfy lau Daddy, Momsie na daki tunda taje yin sallah bata fito ba" ,"ok bari na dubota kila lazimi takeyi" ya tashi ta shiga dakin Momsie yaga tana linke kaya tazo tayi hugging dinshi "welcome swthrt" ,"madam ya yau" ,"kalau, yau da ganin ka nasan akwai magana bakin ka" kallonta yakeyi cike da shaukin so yace "hummm  hakane, yau nazo miki da albishir amma  bazan fada miki ba se kin gayamin wani tukwici zaki bani" dariya tayi dan ta gano inda ya dosa tace "duk abunda kakeso zanma" yayi murmushi yace "ar u sure" tace "sure,always at ur service" sukayi dariya gaba dayansu sannan yace mata "ur daughter is coming back tomorrow" ,"am excited, can't wait to see her, i missed her so much" yace "same goes with me".  Kallonshi tayi kafin tace "please swthrt in *ZYNAH* ta dawo inaso kayi kokari ka dinga boye son da kake mata a gaban Islam, in zaka musu abu kada ka banbanta cos dey ar all ur children kaji" seda ya sauke numfashi sannan yace "sure i will try my best" ,"dats my husband give me a high five" ya bata hannu suka tafa sannan yace "honey yunwa nakeji" ,"muje kaci abinci" suka sauko Islam na nan tana kallo ganinsu yasa tayi pause itama ta tashi sukaje dinning dan cin abinci.

**********
          *Kano*                     *WASHEGARI*
     Sun gama shirye shiryen koma wansu lokaci suke jira su tafi airport, dukda *ZYNAH* bataso kumawa yanzu ba amma ba yadda ta iya dole ta hakura kodan kar Uncle yaji wani iri saboda haka ta sake sosai suna hiransu da Granny da Uncle. Granny ce ta tashi tace tana zuwa nan ta shiga kitchen tasamo manyan ledoji ta zuba musu kuka,kubewa, daddawa,yaji da sauransu tafito ta ajiye musu tace "ga wannan ku kaiwa ýa ta tayi miya" *ZYNAH* ta kalli ledan ta kalli Uncle sannan ta kalli Granny tace "Granny me a ciki" tace "kuka ce da sauransu" *ZYNAH* ta gwalo ido tace "Granny ai ba'a shiga jirgi da kuka" ,"ke dan Allah rufa min baki, haka ubanki ke cewa duk sanda yazo gaishe ni, amma ai naga Zinaru duk sanda danta yazo gaishe ta tana bashi ya kaiwa matanshi kuma yana karba kuma shima naga jirgin yake bi". Shiru *ZYNAH* tayi dan kuwa yanzu batasan me zatace ba kuma,Uncle kuwa dariya yake musu danshi yanzu drama dinsu dariya yake ba shi, tsagaita dariyan shi yayi sannan yace "manta da ita, in bazata  kai ba ni zan kai" kallon Uncle dinta tayi a zuciyar ta tace "kardai da kukan ze shiga jirgi" itako Granny cewa tayi "yauwa kunga dan albarka , bari a kira Idi yazo yasa muku kayanku a mota" Uncle yace "a'a base an kira shi ba dayake Mubarak ne ze kaimu airport" ,"abokin ka na jiya" ,"eh, shi" ,"oo toh kun kirashi ne" ,"eh,anjima zaizo" ,"Allah ya kowa shi, ke kuma Madam sirina tashi ki duba ko Jummalo  ta gama girki" ,"Granny ni ba sunana Sirina ba"  ,"ke kika sani".

     Dan wake ne  da  mai da yaji wanda yaji kayan hadi Jummalo ta musu, dukda Uncle be cika son dan wake ba amma yaci sosai kuma yaji dadin shi. Sun gama cin abinci suka shirya Uncle ya kira Mubarak a waya yace yana hanya, cikin minti biyar se ga shi yazo suka sa kayansu a boot sukayi sallama da en gidan Uncle ya musu ihsani, sannan suka wuce airport cike da kewan Granny. Sun kai airport suka shiga da kayansu Uncle ya dauko ledan kuka ya mika wa Mubarak yace "ga wannan ka kaiwa tsohowan ka" ,"kai kuma ina ka samo kuka" ,"wa ze ban kuka inba Granny ba wai akai tsaraba" dariya yayi yace "toh shine ni zaka hada ni dashi" ,"kai dai yi hakuri ka raba ni da kukan nan" ,"toh shikenan zan kai gida" ,"ko kai fa" dariya sukayi gaba dayansu sannan sukayi sallama suka shiga ciki *ZYNAH* tace "Uncle baka zo da kukan bane kuma" yace "ai na ba Mubarak, dama saboda a zauna lfy da Granny ne yasa nace ta kawo" ,"kai Uncle  ka gan ka" murmushi kawai yayi ana haka akayi anounce cewar jirgin su ze tashi duk suka gyara zama tareda sa sit belt jirgin ya daga zuwa Lagos.

**********
         
*Zaria*
     Wasa wasa tun ranan da  *ASHRAF* da Minal sukayi magana akan mafarkin da yakeyi yarinyar ta daina zuwa mishi a mafarki yau tsawon kwana biyu kenan, tun yana boye damuwan shi har ya kasa aka fara gane yana cikin damuwa amma in aka tambayeshi me ke damunshi sai yace ba komai, da haka Minal taga bazata iya kyale shi tace se taje ta tambaye shi ko lfy. Da wannan tunani ta riske shi a dakin shi yana kwace kaman me barci amma a zahiri ba barcin  yakeyi ba. Jin alamun an shigo  dakin shi ne yasa shi dagowa yaga Minal tsaye a kanshi yace "Minal me ya kawo ki ko kina bukatan wani abune" ta nemi wuri kusa dashi ta zauna tace "ba abunda nake bukuta illa ina so nasan me ke damunka kwana biyu nan, u look doll, kowa ya  kalle ka yasan kana cikin damuwa, amma in an tambaye ka se kace ba komai, dan Allah ka daure ka fada mun damuwarka ko ba komai zamuyi shawara tare" ajiyar zuciya ya sauke sannan yace "Minal tun ranan da nagaya miki ina mafarki da yarinyar nan na dai mafarkin ta, amma ni ba rashin mafarkin da nadenayi bane ke damuna ba a'a, abunda ke damuna shine wat if da gaske aljanah ce tunda se da na gaya miki sannan na daina mafarki da ita" dafashi tayi sannan tace "calm down, karka sa wannan ya zame maka damuwa, addu'a zaka dingayi, mutum ce ko aljanah ce idan akwai alheri a tattare da ita to Allah ya tabbatar da shi in kuma sharri ke tattare da ita to Allah ya kareka,nima kuma zan tayaka da addu'a amma pls u need to cheer up, chill kar a gane abu na damunka" kallon ta yayi tareda murmushi yace "zanyi yadda kika ce, my lil sis" itama murmushin ta mayar mai sannan tace "zan shiga gida yanzu na dawo daga wurin dinki banshiga ciki ba tukun" ,"ok nima wanka zanyi yanzu zan shigo in na gama" tace "ok seka shigo" sannan  ta fita shikuma ya tashi ya shiga bathroom dan yin  wanka.

**********
          *Lagos*
     Se shirye shirye akayi na dawowan su *ZYNAH* gidan kaman wa'anda sukayi tafiyan shekara, gida duk ya dume da kamshin abinci, daga Daddy har Momsie kowa ka kalla fuskan shi kasan yana cikin farin ciki,harta Humaira ma tazo da ita ake komai a cewarta baza'a barta a baya ba wurin tarban bestee dinta, Islam ce kawai bata wurin da alamun ma bata gidan gaba daya. Misalin karfe daya da rabi Islam ta dawo gida da kayan Islamiyya a jikinta da alamun Islamiyya taje, tana shigowa taji gidan ya dume da kamshi taga se aiki akeyi a zuciyar ta tace "yau kuma meke faruwa" kitchen ta nufa dan taga me akeyi , da shigarta Momsie tace "aa mamana har kin dawo' ,'eh Momsie na dawo,anty Humaira yau kece a gidan namu, tunda sista ta tafi se yau kika leko mu" Humaira da take tsaye da cibin miya a hannu tace "wlh nima nawa registration dinne yasa kuka jini shiru" ,"ok hakane, Momsie hala zakiyi baki ne naga se girki kike" ,"Au ai na manta ban fada miki ba ur sista is on her way, yau zasu dawo" bammm taji gaban ta ya fadi a zuciyar ta tace "wato bcos i'm nt dat important an ma manta dani shiyasa aka rasa wanda ze bude baki yace min ai yau sista zata dawo se yanzu nakeji" amma a fili kuwa tsalle tayi tana nuna murnan ta harda rawa alhalin deep inside her abu daban take tunani. "Momsie ina zuwa bari naje na cire uniform" bata tsaya taji me Momsie zatace ba tayi sama a guje ta shiga dakinta ta kulle tasa mukulli seta sullale kasa tana kuka me cin rai.

     Ita a duniya in akwai abunda bataso ta gani be wuce taga iyayenta suna zakewa akan *ZYNAH* ba, ita ba wai batason er uwar bane a'a yanda ake nuna banbanci karara a gaban ta ne yasa takejin kin er uwar tata a zuciyar ta amma ita tasan she has to live wit it tunda *ZYNAH* din er uwarta ce ba yanda ta iya. Da ta gaji da kukan taga bame lallashin ta yasa ta tashi ta cire uniform ta zuba a basket din kayan wanki sannan ta shiga bathroom tayi wanka ta fito tasa kaya tayi sallah ta kuma ta kwanta saboda kanta da taji yana mata ciwo, bata dade da kwanciya ba barci ya dauke ta. Su Momsie sun gama girke girken su sun jera suka turara gidan sannan kowa yaje yayi wanka sukayi shirinsu na zuwa airport dauko su *ZYNAH*. Momsie jin Islam shiru ba ita ba alamun ta yasa taje dakinta amma taji kofan a kulle,nan ta fara knocking Islam cikin barci taji ana kwankwasa mata kofa ta tashi da kyar saboda kanta dake mugun tsara mata taje ta bude Momsie ta shiga tace "Islam shirya muje airport dauko er uwar ki" ,"Momsie kuje kawai bazan iya zuwaba kaina na ciwo" se alokacin ta lura da yanayin er tata tace "sannu, ba yanzu kika shigo lfy lau ba" ,"nima gaba daya naji ciwon ya tasar min" ,"ehya sannu kinsha magani","eh nasha" ,"toh kwanta ki huta bari muje mu dawo" ,"se kun dawo" Momsie ta amsa mata da yauwa tareda fita taje tasamu Humaira da Daddy ta fada musu Islam bata jin dadi duk sukaje suka dubata tareda mata sannu sannan suka fito zuwa airport.

     _Kuyi hakuri na rashin jina kwana biyu, nayi busy ne amma koda yaushe kuna raina my dear readers  nd tnx for being patient wit me😍_

       _Mzz Daddy 💋✍🏻✍🏻_

ZYNAHKde žijí příběhy. Začni objevovat