2

4.6K 142 31
                                    

GEFEN IFTIHAL
Iftihal kuwa haka ta bar wurin party ranta a b'ace, ga Zee ta b'ata mata rai ta kaita gun party ba da son ranta ba, ga shi kuma wani d'an iska da bata ma san shi ba ya shammaceta ya tab'ata dan rashin mutunci har da ma kissing d'inta. Ta masa Allah ya isa ya fi a k'irga. Ko mai a daidaita sahun da ya d'auketa sai da ya kasa hak'uri yace, "Hajiya wai wa kike ta la'ana da tsinewa haka ne tin d'azu? Ai dai ko kece kika haifeshi kin rigada kin gama kwashe masa albarka, ki raga masa haka mana."

Tsabar takaici Iftihal bata ma san sanda ta zunduma masa wata uwara ashar ba, wanda ita kanta bata san ta iya shi ba, ai ba shiri d'an a daidaita ya kama bakinsa, Allah-Allah yake ya sauketa ya k'ara gaba, dan ya lura ranta a b'ace yake ko mai zata iya yi. Yana sauketa kuwa ta fito da nera d'ari biyu ta bashi, dan ya d'auki nera d'ari ya bata canji, ko da ya duba yaga ba canjin sai ma yace ya bar mata kud'in, ya k'ara gaba abunshi.

IFTIHAL IBRAHEEM SHU'AIB kenan, yarinya mai nutsuwa da kamun kai, amma kuma bata d'aukar raini da wulak'anci. Ko mai girman mutum ya tab'ata sai ya gwammace bai yi ba, sa'o'inta duk shakkarta suke yi. Marainiya ce gaba da baya, domin duk iyayenta sun rasu. Tana zaune ne a tare da kawunata MALAM KALLAMU da matarsa ABU, da ita da y'an tagwayen k'annenta maza FARHAN da RAIHAN. Wannan k'annen nata su kad'ai take da kuma take ji da su kamar ranta, bata k'aunar abunda zai tab'a su. Ko kawunta da matarsa idan har suna son su k'untata mata, sai dai su tab'a mata y'an tagwayen k'annen nata, ta wannan hanyar suke cin galabarta har ta musu abunda suke buk'ata.

Iftihal na isa k'ofar shiga gidansu ta tsinkayi tashin kukan k'annen nata Farhan da Raihan. Ai kuwa ta kwasa da gudu ta k'arasa cikin gidan, ta nufi k'annenta ta janyo su tana tambayarsu abunda ya faru.

Farhan ne yace, "Sister tun da kika fita da safe ba mu k'ara cin komai a gidannan ba, kuma Gwaggo Abu sai aiki take samu, amma bata bamu abinci ba, gashi Raihan ya ce min jiri yake ji, shi yasa muke kuka."

Iftihal ta lalubo jakarata ta ciro d'ari biyu, dama ita kad'ai ta rage mata, ta mik'awa Farhan tace, "ungo je gidan Iya Rabi ka karb'o muku abinci." Farhan ya karb'i kud'in cikin murna ya mik'e zai je siyo abincin.

Ai kuwa dama Abun tana kusa, sai ganin sukayi ta fito tayi sharaf ta karb'e d'ari biyu tace, "munafukan Allah, an hanaku abincin. Naga dai ba ubanku ne ya aiko da buhunan abinci daga lahira yace na dinga dafawa ina baku ba."

Iftihal na jin haka ranta ya k'ara b'aci ta mik'e a fusace ta nuna Abu da yatsa tace, "Abu wallahi ya isheki, duk tsiyar da zakiyi ta tsaya a kanmu, kar ki sake ki k'ara ambaton iyayenmu da suka rasu. Kuma da uba yana aiko buhunan abinci daga lahira da naki uban ya dad'e da aiko miki, dan tun da dad'ewa nike jin yanda Kawu yake zaginki da miki gori akan haka aka kawo mishi ke k'yamusasai a bushe ba ko y'ar gara, meh ya hana naki uban ya aiko masa garar daga lahira ko kya huta da gori? Kuma mu sanda namu mahaifin yake da rai wanne irin kalar buhun abinci ne bai baku ba? Dan mutuwa ta rabashi da duniya shi yasa har kike furta hakan? Nan gidan ma da kuke wata wadak'a da iyayi a cikinsa na uban waye? Naga dai gidan na uban namu ne, dan ya taimaka ya ajiyeku dan ya rabaku da wahalan yawon garari kuna yawon haya? Shine yanzu da bashi da rai kike fad'ar yanda kika ga dama gun y'ay'an da ya haifa, dan tsabagen butulci? Kuma duniya dai kowa sai ya barta ya je lahirar ko d'an uban waye kuwa."

Tinda Iftihal ta fara masifa Abu ta rik'e hab'a tana kallonta, sai da taji gyaran muryar Malam Kalla zai shigo gidan sai kawai ta fashe da kuka. ta cakume Iftihal tana fad'in, "yanzu y'arnan ni kike zagi kina kiran iyayena matsiyata? Toh bari Malam ya zo, sai na ji ko ni ko ku a gidannan. Wayyo ni Allah y'ar cikina yau ta zageni dan ni Allah bai bani haihuwa ba. Daga cewa Farhan ya karb'i d'ari biyunnan yayo cefane ki d'ora mana girki dan ni yau bana jin dad'i shine zaki hau zagina? Nice baiwarku dole na girka na baku tinda dai a gidan ubanku nike zaune, Kawun naku kuma sakarai ne ba abunda yake iya tsinana muku, bayan shine cinku da shanku a gidannan."

MAI SONA KO ZAB'INA? (ONLY PREVIEW) Where stories live. Discover now