1.

11.2K 332 41
                                    

Tsaye take agefe d'aya ta takure kanta, yayin da wasu matan da mazan ke gefe suna chashewa abunsu. Tsaki take ta yi ba ko tsayawa. Bata Ankara ba taji kawai an janyota an rungume, ta fara kiciniyar k'wace kanta, kafin ta san ko waye sai kawai ji tayi ya had'a bakinta da nashi ya fara kissing d'inta. Iya k'arfinta ta saka tana k'ok'arin k'wace kanta amma ta kasa, sai da ya gaji dan kansa ya saketa. Tayi taga-taga ta fad'i k'asa kan k'arfin da ta saka gurin janye kanta, ga kanta da ya shiga juya mata. Cikin tsananin masifa da tashin hankali ta mik'e tsaye domin ganin waye ya mata wannan cin zarafin, wane d'an iskan ne yake k'ok'arin keta mata haddinta? Dara-daran idonta har sun k'ank'ance kan tsabar masifa.
Tan d'agowa tayi arba da kyakkyawar fuskarsa. Kyakkyawa ne ajin farko, dogo ne k'ak'k'arfa mai cikakkiyar halittar da kowanne namiji yakeburin samu. Ba fari ba ne shi, sannan kuma shi ba bak'i ba ne, kuma ba za'a kira shi da chocolate color ba, dank alar fatarshi ta fi chocolate haske. Kalar fatarshi mai tsada ce, sai shek'i take yi. Ga wani murmushi da yake d'auke da shi, wanda shine ya k'ara fito da kyaunsa kuma ya k'ara k'awata fuskarsa.
Duk a cikin dak'ik'u da basu wuce biyu ba Iftihal ta k'are masa kallo. Amma duk wannan kyau nasa da kwarjini bai hanata d'aga hannu ta wanke kyakkyawar fuskar tasa da mari ba. Sannan ta had'a da cewa, "kai wane irin d'an iska ne jaki? Meh kake tak'ama da shi ne da har ya baka damar yi min wannan cin zarafin? Dan ka ganni a irin wannan wurin ba wai shi zai baka damar ka ci zarafina ba, bakada damar da zaka tab'ani with your filthy hands. D'an iska kawai fasik'i, shashasha da bai san abunda yake yi ba." Ta ja tsaki ta wuce cikin sauri kamar zata tsinke k'afafunta.

K'awarta ce da suka zo tare ZEE, wacce ta lura da abunda ya faru ta sha gabanta tana fad'in, "haba IFTIHAL, ya kike haka ne wai? Ke wai har zuwa yau she ne zaki waye? Wannan guy da yayi kissing d'inki na tabbata duk macen da take wurinnan ko kud'i zata iya biya da zata samu ma ko Magana ne yayi da ita, bare har ya tab'ata. Bayan shi ma ga had'ad'd'un guys nan sai so suke ki kula su kin wani had'a rai, ki duba kiga yanda had'ad'd'un y'an mata suketa walwala suna jin dad'in rayuwarsu, amma ke kin wani had'a rai sai cin rai kike. Ai shi yasa Gwaggo da Kawu suke wulak'antaki da cin zarafinki kullum dare da rana son ransu. Ke kuma kin kasa sakewa ki nemawa kanki mafita har ki ji dad'in rayuwarki."

Cikin tsananin b'acin rai Iftihal tace, "wallahi Zee ki bani hanya na wuce, kin sanni kin san halina sarai, dan da nasan ma irin wannan wurin da ake wannan shashancin zaki zo da ni ba zan yi kuskuren biyoki ba." Daga fad'in haka ta juya ta fice wurin kamar zata tashi sama.

Shi kuwa wanda ta fallawa mari ta bar shi rik'e da kunci yana murmushi, dan yarinyar ko kad'an bai ji haushinta ba, sai ma birgeshi da tayi.Shi kanshi ya rasa yanda zai yi ne ya rabu da masifar Ibtisam shi yasa yayi haka. IRFAN MUHAMMAD Kenan, saurayi mai kyau da kwarjini da kuma tarin farin jini a gun y'an mata. Amma shi a cewarsa har yanzu baiga budurwar da ta masa ba, dan duk macen da ta kulashi haka zai fatattaketa, sai fa IBTISAM ALI SADIQ, yarinya y'ar gata, mai ji da kud'i, kyau da gata. Ita kad'ai ce ta zame masa k'adangaren bakin tulu, yayi-yayi ta rabu da shi amma ta k'i, ta nane masa kamar kaska. A yau ne da yayi hakan a gabanta yake tunanin ya yadda k'wallon mangoro ya huta da k'uda.
Abokinsa ne ASLAM ya matso wurinsa yana fad'in, "baba ya hakane? Ya akayi yau ka bari wata ta tsinkaka a bainar jama'a? ya akayi hakan ta faru yau? Ni fa nayi mamaki da naga ka rungume wata macen a yau har da kissing d'inta, hanyar da muka dad'e muna d'oraka dan kaji dad'in rayuwarka amma kak'i ka bi. Amma kuma yau da kayi gashi karon farko ka samu red card." Ya fashe da dariya sannan ya k'ara cewa, "amma yarinyar nan y'ar gidan uban waye da zata maka haka? Bata san yanda y'an mata ke rububinka ba ne?"

Irfan yayi murmushinsa mai d'aukar hankali sannan yace, "ban sani ba Aslam. Kuma ni ba abunda ya dameni da tsinkanin da tayi a bainar jama'a, dan ni da matan ma zasu k'yaleni da na fi son hakan. Kuma ita wacce nayi hakan da ta gani ta rabu da ni bataga lokacin da aka tsinkanin ba."
Aslam ya fashe da dariya sannan yace, "amma wallahi Irfan bakada mutunci, kana nufin dama dan Ibtisam kayi hakan?"

MAI SONA KO ZAB'INA? (ONLY PREVIEW) Where stories live. Discover now