Ki kwantar da hankalin ki zinat, in sha Allahu zamu rike ki tsakani da Allah, mu ma iyayen ki ne, baza ki taba maraici ba in sha Allahu, ki saki jikin ki, ga yan uwan ki, ku zauna lafiya yanda kuka saba, mu cgb da musu addu'a, Allah ya sa aljannah ce makoman su! Abba ke magana! Umma tace, ki daina kuka zinat, addu'a zaki dinga musu kinji, kiyi hakuri! Goge hawayen fiskan ta tayi, sannan tace, nagode da kulawan da kuka nuna mun, in sha Allahu zamu zauna lafiya da yan uwa na. Abba yace, masha Allahu, se ki shirya komawa makaranta, an miki transfer daga ABU zaria, zuwa nan makarantar su Nabila, se ku dinga zuwa tare ko, duk zata nuna miki abubuwan da ya kamata! Zinat tace, toh Abba nagode Allah ya saka da alheri! Zinat Nasir Dabo, yar shekara 19, diyar Alh Nasir Dabo da Haj Binta, yar auta kenan bayan Zayyad da Zarah. Abba wato Alh Nura Dabo, wa ga Alh Nasir, matar sa daya umma wato Haj Khadija, 'ya'yan su 3, Nasir(sultan), Najib da Nabila. Haj Binta, ta kamu da breast cancer shekara 2 da suka wuce, ta wahala sosai, a karshe Allah ya karbi abun shi, a dalilin haka ne, ciwon zuciya ya kama Alh Nasir, wanda yayi jinya kusan wata 5, kafun shima Allah ya amshi abun shi. Zayyad yayi aure, Salma matar sa, dan shi daya salim, yana zama a kaduna, zarah kuma tana da ciki kenan, tana zama a nan abuja, bayan rasuwan ne zinat ta dawo gun Abba. Sultan da najib suna aiki ne a kampanin su Abba da ke abuja, zayyad kuma na kaduna, Nabila da zinat kuwa suna 300lvl kenan.
VOCÊ ESTÁ LENDO
ZINAT......2013
RomanceZinat fell and fell hard for sultan! No matter what she did, he never saw the good in her.... The twists and turns and heartache! Is he made for her or is she made for him? Will he ever accept her or is she destined to suffer in love?
