EPISODE 13

10 0 0
                                    

♦️AL'AJABI♦️
(DAGANI BABU TAMBAYA)
   BY
REAL HAJARA YUSUF

Episode 13

Da yake zainab tasan gidan basu wani sha wahala ba suka isa, Da yake sammako sukayi sunje babu kowa hakan ya basu damar Shiga. Gaban zainab ne yafadi yayinda tayi ido hudu da Mallam Zakiru. Hakan yasa takoma bayan kaka ta rakube, Mallam Zakiru ya kalleta yace Kizo nan kizauna yayi mata nuni da wata darduma dake gabansa yana fuskantarsa.

...... Jiki na rawa zainab ta tashi ta zauna a inda aka umurceta, gabanta sai faduwa yake. Mallam Zakiru yace Fadamin meke tafe daku...... Dama... Da... Zainab takama in ina, kaka tace to ai gani ni sai a tambayeni tunda ita takasa Magana.

Mallam Zakiru yace Nasan tabbas dole saikun dawo amma dai ina Sauraron ku ya maida hankalinsa kan kaka da ita dinma shi take kallo. Bayan kaka tayi gyaran murya sannan tafara magana ba tareda da huta ba saida ta zaiyano masa komai harda Akuya da agwagwa da suka kawo sannan ta zaiyano masa irin Azabar da takeso ayiwa Aljaninda yake tsorata fati. Mallam yayi Shiru Sannan Yace....

Ni Mallam Zakiru ba zan iya yi muku aikin nan ba sabida yanzu wannan aikin yafi karfina. Lokacin da naso taimakonku baku bani dama dan haka yanzu saidai kuyi hakuri ni Bazan iyaba saidai ku nema awani wajen.

Kaka tace haba Mallam da girmanka yaushe zaka tsaya gaba da kananan yara dan kawai sunyi maka rashin kunya a baya haba kar ka manta d'a Nakowa ne, Mallam Zakiru yace hakane kuma ni tun tuni na yafe musu, kama tace yauwa to godiya muke ke jeki kice hashimu ya shigo da Akuya da agwagwan. Mallam yace aikinne bazan iyaba kuje kawai. Kaka zatayi magana mallam yace wani ya shigo domin wasu sunzo a bayansu. Hakan yasa kaka da zainab tashi su fita badan sun so ba.

.... Bayan sun fitane suka tsaya a kofar gidan suna jira ko wani zaizo a adaidaita saisu samu su shiga, ana haka saiga a daidaita sahu yazo juyawar da zainab zatayi kawai sai taga Ya'u nan take taji wani farin ciki ya lullubeta. Yana yin parking zainab tace kaka wannan Shine Ya'u mai Adaidaita. Ya'u shi kuwa bai ganeta ba sabida tasa face mask. Yazo zai wuce kenan sai tayi saurin cire face mask din sannan tace sannu! Yana ganinta yaji farin ciki ya ziyarce shi bai San sanda ya saki murmushi ba Haka itama murmushin take har ya iso gabanta suka gaisa sannan tace zaka dade ne idan ka shiga Ya'u yace da wani abune, zainab tace munaso ka kaimu gidane, Ya'u yace ay gaskiya zan dade saidai yanzu bari zan kaiku saina dawo daga baya nayi uzurina, zainab tace aa ai naga ba layi zaka iya shiga zamu jiraka idan kagama saika fito mutafi. Ya'u yayi murmushi sannan yace ba wajen Mallam nazo ba gida nadawo. Da mamaki zainab tace kana nufin kai dan mallam ne, Ya'u yace kwarai kuwa. Zainab tace sai yanzu kuwa na lura kuna kama kuwa ba banbanci. Ya'u yace saidai niba tsoho bane, gaba dayansu sukayi dariya. Kakace ta kwalawa zainab kira sai ananne zainab ta tuna ta zake dayawa da har ta manta dasu kaka, Ya'u ne ya tsuguna har kasa ya gaida kaka sannan yace kuzo Muje sunje sun shiga kenan sai Ya'u yaga hashimu rike da agwagwa yana Jan Akuya zai shiga. Ya'u yace baku samu ganinsa bane? Kaka tace inafa korarmu yayi, da mamaki Ya'u yace kora? Kuma Mallam din? Zainab tace ay Wallahi anan tadan bashi bayani amma taboye sauran. Yau yace kuyi hakuri yanzu zanje na rokar muku Insha Allahu zaiyi muku aikin.

.... Bayan mutum na ciki yafita Ya'u ya shiga yayiwa Mallam bayani harda yadda gidan fati ya bace masa. Da farko mallam yaki amincewa amma daga baya ganin yadda Ya'u ya nace hakan ya sashi amincewa. Amma da sharadin zaiyi musu aikine kawai ba tareda ya fada musu da baki ga inda Matsalar take ba. Ya'u yace ya amince sannan ya roki Alfarma a fada masa menene Matsalar sannan yayi Alkawari bazai fada ba. Mallam bai boyewa Ya'u komai ba gameda abunda ke faruwa da fati. Ya'u ya jinjina Al'amarin sannan yayi godiya ya fita.

Su zainab suna zaman jiransa a waje shiko ya tsaya a zaure yanata sake-sake a ransa.

.... Anya zai iya rike wannan Alkawari kuwa ba tareda ya fadawa zainab ba?

..... Shida yake son taimakonsu ta yaya zaayi kuma yabarsu suyita lalube acikin duhu?

.... Idan ya fada yaci Amanar Mahaifinsa idan kuma ya bari fati da zainab zasu sha wahala.

Murya da hqyaniyar jamaa ne yadawo dashi haiyacinsa, Yayi waje da gudu dan ganin meke faruwa.

♦️AL'AJABI♦️ (DAGANI BABU TAMBAYA) حيث تعيش القصص. اكتشف الآن