EPISODE 12

6 0 0
                                    

♦️AL'AJABI ♦️
(DAGANI BABU TAMBAYA)
HAJARA YUSUF
   BY
REAL HAJARA YUSUF

            ᗴᑭIՏOᗪᗴ 12

𝐈𝐍𝐀 𝐖𝐀𝐃𝐀𝐍𝐃𝐀 𝐒𝐔𝐊𝐄 𝐒𝐎𝐍 𝐅𝐀𝐑𝐀 𝐒𝐀𝐍𝐀𝐀𝐑 𝐒𝐀𝐘𝐀𝐑 𝐃𝐀𝐓𝐀. 𝐆𝐀 𝐃𝐀𝐌𝐀 𝐓𝐀 𝐒𝐀𝐌𝐔.
Nakowadata.com 𝐒𝐔𝐍 𝐊𝐀𝐑𝐘𝐀 𝐅𝐀𝐑𝐀𝐒𝐇𝐈 𝐊𝐔𝐌𝐀  𝐀 𝐒𝐇𝐈𝐑𝐘𝐄 𝐒𝐔𝐊𝐄 𝐃𝐎𝐌𝐈𝐍 𝐊𝐎𝐘𝐀 𝐌𝐔𝐊𝐔 𝐘𝐀𝐃𝐃𝐀 𝐙𝐀𝐊𝐔 𝐒𝐀𝐌𝐔 𝐊𝐔 𝐀𝐊𝐀𝐋𝐋𝐀 3000 𝐊𝐔𝐋𝐋𝐔𝐌 𝐓𝐀 𝐇𝐀𝐍𝐘𝐀𝐑 𝐒𝐀𝐘𝐀𝐑𝐃𝐀 𝐃𝐀𝐓𝐀, 𝐊𝐀𝐓𝐈𝐍  𝐊𝐈𝐑𝐀, 𝐑𝐄𝐒𝐔𝐋𝐓 𝐂𝐇𝐄𝐂𝐊𝐄𝐑 (𝐖𝐀𝐄𝐂 𝐀𝐍𝐃 𝐍𝐄𝐊𝐎), 𝐍𝐄𝐏𝐀 𝐁𝐈𝐋𝐋 𝐃.𝐒

𝐑𝐄𝐆𝐈𝐒𝐓𝐄𝐑 𝐊𝐘𝐀𝐔𝐓𝐀𝐍𝐄
𝐀𝐘𝐈 𝐌𝐀𝐙𝐀 𝐀 𝐓𝐔𝐍𝐓𝐔𝐁𝐄𝐌𝐔 𝐀 𝐖𝐀𝐍𝐍𝐀𝐍 𝐋𝐀𝐘𝐈 𝐊𝐀𝐌𝐀𝐑 𝐇𝐀𝐊𝐀
08136230000

Kaka tayi saurin mikewa tadau hijabi tace tazo Muje gidan malamin ni zan bashi akuya da bakar agwagwan ya kashe min wannan tsinannen Aljani da yake bibiyar rayuwar fati kuma dukda tayi aurenma bai barta ba. To wllh ba zanyi kaffara ba dole sai ankona shi da Jinin agwagwa... Dariya ne ya kufcewa zainab batare da tayi niyyar yin dariyar ba, kaka ta galla mata harara sannan tace ke kuma dariyar me kike? Zainab wayance tace dariyar farin ciki nake kaka yadda zakisa a wulakanta wannan azzalumin da yake so ya cutar da fati, Gaskiya kaka ke jaruma ce.

Kaka ta saki murmushi sannan tace ai badan yanzu inada tausayi ba da kuwa da kaina zan kona wannan Aljanin amma banaso na dawo da jarumtata irinna bayane shiyasa zan mika shi ga malamai. Yanzu dai tashi mutafi zainabu dan da zafi - zafi ake dukan karfe.

Sai a sannan mama tayi mgn tace Amma ni aganina da andai tsaya shi Mallam din yadawo a fada masa watakila da abunda zai iya. Kaka tayi shiru sannan tace aa Hamsatu nidai ba zanyi kunnen uwar shegu ba gameda Al'amuran fati.

Mama tace wannan gaskiya ne saidai koda da wani abunda zaa bukata kinga zai iya taimakawa. Wayar zainab ce tayi kara tana dubawa taga Ya'u dan Adaidaita sahune yake kira. Tayi saurin cewa yauwa kaka kinga wannan mai kiran shine dan Adaidaita daya kai fati amma ni ya gagara kaini.

Kaka tace to kice masa jibi yazo zai kaimu gidan fatin Da izinin Allah Bazai gaji a banza ba kuma zamu bashi duk kudinda ya bukata tunda dai yanzu ana tsadar man fetur. Kafin zainab tadau kiran har kiran ya katse. Dan haka ta ajiye wayar a gefe ta cigaba da cewa Wllh shi kanshi Ya'u abun ya kulle masa kai. Amma tunda zaa dau mataki ai shikenan komai zaizo da sauki.

Kaka tace mataki kam kamar an daukeshi angama dan ba zance a yiwa wannan Aljani sassauci ba. Yanzu dai zainabu kije gida ki nemi izinin iyayenki kice zakiyi mini rakiya gobe da safe. Zaki kaini gidan malamin naku, yanzu zan kama akuyata daya sannan zan aika hashimu sayen agwawan kinga kenan gobe sai tafiya.

Zainab tace to shikenan kaka Allah ya kaimu goben, saida safe mama' dukkansu suka amsa da Allah ya kaimu. Zainab tasa kai tafita.

Bayan Mallam ya dawo saida mama tabari yayi wanka yaci abinci, sannan tayi masa bayanin dukkanin abunda ke faruwa Harda shirin kaka na komawa gidan Mallam Zakirun.

Mallam ya jinjina Al'amarin amma yayi karfin halin cewa ba komai ai ba abunda ya gagari Allah, zamu cigaba da Addua har Allah ya yaye mata. Mama tace hakane amma yanada kyau ayi Addu'ar sannan a hada da magani. Mallam yace to Allah yasa a dace,

Mama tace Ameen Ya Allah.

Zainab kuwa da taje gida zama tayi a gaban waya tana jiran Ya'u ya sake kira amma taji shuru bai kiraba. Gashi bata San dalili ba Haka kawai take jin sonyin magana dashi.

Saida dare yayi Ya'u bai kiraba sannan ta cire rai da ganin kiran shi.

Shima ta bangaren Ya'u duk abun ya dameshi ganin bata dau kiransa ba kuma bata bishi da kira ba a haka ya kwana da tunanin dalilin rashin daukar wayarsa ko binsa da kira.

A can bangaren fati kuwa tanata shiri ita a dole zasuje ganin iyayen Jibrin. Amma abun mamakin shine wani mafarki da tayi mai kama da gaske amma tayi hakuri ta barwa zuciyarta komai.

Gari na wayewa zainab tayi shiri tun da sanyin safiya, yayinda itama kaka ta shirya dawuri tayiwa mama da mallam sallama sannan takira hashimu tace yazo suje tare.

Bayan ta fitane ta shiga gidansu zainab. Ummar zainab na ganinta tayi mata sannu da Zuwa tareda fadin cewa haba Inna ai ba saikin zoba, zainab ai jikarki ce.

Kaka tace hakane amma ai yakamata nazo din. Bayan sun gaggaisa zainab tafito suka nufi bakin hanya duk su ukun suka hau a daidaita sahu sai gidan mallam Zakiru.

♦️AL'AJABI♦️ (DAGANI BABU TAMBAYA) Where stories live. Discover now