Chapter thirty one

11 1 0
                                    

So da Buri
Free Book
31

Cike da farin ciki Jalila wadda take ji kamar an tsundumata a Aljannah ta shiga cikin gida!
A tsakar gidan ta tadda Umma da alama ita take jira..
Ko k'arasowa Jalilan bata yi ba Umma ta hango wayar hannunta da kud'in!

Tana zuwa ta bud'e baki zata yi magana kenan Umman ta rufe bakin, ta jata d'aki.
Har da rufe k'ofa bayan sun shiga wai duk dan kar a jiyo su!
Abunda bata sani ba 'su Sakinan su kam ba ma sa cikin gidan' dan tun safe Khadija ta kira su tace "dan Allah su zo ita da Huda su taya ta zab'ar kayan da zata yi amfani dasu da bikin nata."

Suna shiga d'akin k'asa k'asa
Umma tace "Ya kuka yi da shi?baki yayi??"
Tayi maganar tana kallon hannun Jalilan kafin ta sa hannu ta karb'i wayar ta hau jujjuyawa.

Ajiyar zuciya Jalila ta sauk'e sannan ta jefar da mayafinta a kan gado ta nemi guri kan kujera ta zauna kafin tace
"Ba Arshaad bane ba! Wai k'aninsa ne, sunanshi Auwal!".

Da mamaki Umma take kallonta kafin tace
"Ikon Allah, me ya ce miki tou? Me ya kawoshi? Arshaad d'inne ya turo shi?".

"A'a, wai ce mini yayi wai Arshaad d'in aure zai yi, wai an zab'a mishi wata a gida...Shi kuma Auwal d'in wai yana sona ne zai aure ni! Sannan wai in yi shiru kar inyi magana da Arshaad d'in de komenene dai ni dai ban gane ba gaskiya."

"Ikon Allah!"
Shine abunda Umman tace
kafin ta sake cewa
"Tou ai Alhamdulillah."

Nufar wardrobe d'insu tayi mai b'allalliyar k'ofa.
Wajen kayanta ta hau bincikawa da alamun akwai abunda take nema...

Cike da son jin k'arin bayani
Umma ta matso kusa da ita tace "Jalila ki juyo ki yi mini bayanin da zan gane dan ni sam ban fahimci zancen ki ba."
A d'an razane kuma sai ta tab'ata sannan tace
"Ince dai ba Hudan zai auraba ko? Shi Arshaad d'in!".

"A'A"
Jalilan tace, kafin ta sake cewa
"Kina jina fa nace miki 'a cikin danginsu aka zab'ar mishi mata!
A yadda na fahimta kamar ma fa bai gayawa ita Hudan ba har yanzu."

Wata kalar dariyar mugunta Umma tayi sannan tace
"Allah shi k'ara!
Sai wani faman hura hanci suke yi su a dole y'arsu zata auri mai kud'i!
Ai ga irinta nan."
Sai da ta d'an yi shiru kamar mai tunani kafin ta sake cewa
"Ikon Allah, wani hanin ga Allah baiwa ne...Kiga fa babu yadda ban yi dake akan ki fita ku had'u da Yaron nan ba amma Allah bai yi ba!
Yanzu fa da tuni ke zai yaudara ya gudu yaje ya auri wata kinaji kina gani.
Daman nifa an dad'e ana  gaya min cewa
'In kwantar da hankalina, ba Mijinta bane ba!'.

To Amman shi wannan d'in in ce dai mai kud'i ne sosai shima, ko Arshaad d'in ya fishi?".

Juyawa Jalila wadda ta nemo layin ta da kyar a k'ark'ashin hargitsatstsun kayanta, tayi,
tana murmushin tambayar!
Sai da ta amshi wayar daga hannun Umma ta k'arasa ta zauna a kan yagalgalalliyar kujerar d'akin ta fara neman inda zata saka layin a wayar
tukunna ta fara magana
"Ai Umma, ba wai Arshaad d'in ne mai kud'in ba
Inaga kamar Babansu ne mai kud'in!
Domin kuwa shima wannan Auwal d'in yadda kikaga Arshaad tou haka yake..
Da had'add'iyar motar da gayun da yanayin turancin
duk! Kina gani kin san ya tsumu a naira!
Kinga fatar jikinshi kuwa?
Tafin hannunshi laushi kamar....."
Shiruuu, Jalila tayi ta daina k'ok'arin neman inda zata saka layin a wayar, kamar tana tunani....

Mik'ewa ta yi taje inda Umma
take tsaye kafin tace
"Amma Umma gani nake yi kamar d'an iska ne wannan d'in, ina shiga motar fa ya hau rik'e min hannu!
Gaba d'aya ma ni kasa sakewa nayi da shi sosai.
Kuma ni Umma har ga Allah Arshaad nake so!
Inaga gara kawai ki san yadda zakiyi kawai a fasa auren nashi! Dan ni ya fi kwantamin a rai, shi wannan Auwal d'in gaskiya jinina bai wani d'auke shi ba!
Watak'ila mafa kinga d'an iska ne!.
Idan ya zo kar In sake fita ko?
Harda fa matsa mini hannun ya dinga yi!."

SO DA BURI Where stories live. Discover now