Chapter five

12 1 0
                                    

So da Buri
Free Book
05

Jan hannunta Mom ta yi sannan suka yi sama,suna shiga d'akinta tace
"Adama ba fa inda zanje sannan suma babu inda za su je."

"Na sani"
Shine abinda Mom tace sannan ta fara dube dube kamar tana neman wani abu.
Drowern gaban mudubi ta kai hannunta ta bud'e,aikuwa ta ci karo da abinda take nema..da sauri ta d'auko littafin da ta gani da biro sannan tace "oya d'auko mini takardar gidanki wanda ya baki in kalla signature da wani note haka da ya tab'a rubutawa."

D'an tsayawa Ummi ta yi tana kallon ta da alamar tsoro a fuskarta.

Ganin haka ya sa Mom ta kawo gabanta ta tsaya sannan tace
"I'm just trying to help,ba mu da ishesshen lokaci,ki daina
dogon nazari.
Besides har yanzu ukune akan ki so don't worry about one ballantana ma bashi da masaniya,so babushi a lissafi.
Kowa ya sani a estate d'innan kece weakness d'in granpa,ki
duba ki ga abubuwan da yake yi just to make sure u stay happy..I can assure u ba zai bari Abba ya tafi ko Ina ba idan ya ga wannan."
tayi maganr tana nuna mata takardar da ta yaga daga jikin book d'in.

Shiru Ummi ta yi kafin tace
"Adama I love my husband, banaso in shiga tsakaninshi da mahaifinsa.."
Wannan karon tsaki Mom ta yi sannan tace"Zainab kin fara bani haushi wallahi zan yi tafiyata, shiga tsakani kuma na nawa??
Waye ummulaba'isin fad'an nasu?sai da abu ya zo gangara za ki fara tunanin tsame hannunki?
To bari kiji! ta inda akabi aka hau ta nan ake sauk'a sannan
na san Dr Abba farin sani If things get out of control zan yi paying nashi ya maka masa case na memory loss, a ce yayi for a day ne,
a time din kuma yayi ta misbehaving,sai mu ce a lokacin ne yayi shi kansha kenan bai san yayi ba. Dan mutumin da ya kwana ya wuni bai san inda kansa yake ba ai zai yi morethan this,kuma babu wanda ya isa ya musa."

Da sauri Ummi tace"ok ok"sannan ta nufi wardrobe d'inta ta d'auko key a k'asan tulin kayanta sannan ta saka key d'in a jikin wani d'an k'aramin locker wanda yake nan ata k'asan kayannata ta murza mukullin ya bud'u. Wani suitcase ta d'auko ta yo kan gadon da shi,a tare suka hau bincikawa har sai da suka d'auko wani file da wata envelope.
File d'in takardun gida ne, envelope d'in kuwa da suka bud'e ta wani had'add'en rubutu ne ya baiyana a cikin da alama wasik'a ce .
Zama Mom ta yi a kan gadon sannan ta saka wannan wasik'ar a gaba ta yi shiruu...ta kai kusan 2 minutes tana k'are mata kallo kafin ta ajjiye ta a gabanta tukunna ta hau rubutu akan wannan blank papern data yago....exactly handwriting d'in irin na wannan wasik'ar takeyi.
Ta d'auki y'an mintuna tana rubutawa kafin ta d'auki dayan file din ta bud'o dai dai wajen signature ta kalla da kyau sannan ta ajiye ta yi irinta a k'asan takardaar da ta gama rubutu a kai.
Tashi tayi daga kan gadon sannan ta juyo ta kalli Ummi tace mata
"Done!!"

Mik'a hannu Ummin ta yi ta karb'a ta karanta sannan ta sauk'e ajiyar zuciya kafin tace
"Yanzu ta Ina zan wuce??
kin san fa yana falo."

"D'auko mayafinki"
inji Mom.
Cikin wardrobe d'inta ta bud'e wajen mayafai, sannan ta jawo abinda hannunta ya kai kai .
Warewa ta yi tana shirin saka hijabin Mom tace a'a bani nan zan saka a cikin nawa maya fin in fita in yaso sai ki sak'k'o daga baya ki yi kamar kin shiga kitchen,ni kuma zan jiraki a k'aramin compound ta baya,sai ki fito mu wuce."
Har ta juya za ta fita,sai kuma ta dawo ta k'ara rad'a mata wata magana sannan ta fice.

Yadda Mom d'in ta tsara hakan kuwa akayi...

Bayan sun fita daga gate d'in gidan suka nufi na granpa.
Suna zuwa daniel ya gaidasu suka shige suka isa k'ofar main parlor.
Suna shiga kamar kullum sukaga ba kowa,shiruu sai k'arar ac
Ganin hakane ya sa suka nufi kitchen a tunanin su ko za su ga granma ta yi musu iso,amman nan d'in ma ba su sameta ba,sai masu aiki.
Ganin suna b'atawa kansu lokacine yasa Mom ta d'auko wayarta, ta kira gramma,bugu biyu ana ukun ta d'auka.
"Assalamu alaiki, Adama."
Aka fad'a daga d'ayan b'angaren.
Cikin girmamawa mom tace
"Ameen wa alaiki assalam,Ina wuni gramma"

SO DA BURI Where stories live. Discover now