Chapter ten

9 1 0
                                    

So da Buri
Free Book
10
                      

Ranar Monday aka yi chanjen aji, sannan da yamma aka nad'a shadow prefects wanda a ciki har da Maryam, Maryam ta so an bawa Zainab itama domin zuwa yanzu Maryam ta lura a duk lokacin da ta samu abu Zainab d'in bata samuba ne suke samun matsala da ita.

Duk da k'ok'arin ganin an zauna lafiya da Maryam d'in take yi hakan bai hana Zainab kyarar ta ba kasancewar hostel d'aya suke room d'aya aji d'aya kuma seat d'aya.

washegari Tuesday, suna zaune suna jiran first period na English, English theacher d'in ya shigo tare da wani kyakkyawan saurayi sanye cikin khakin sa na nysc,
kusan duk matan ajin ido suka zuba mishi....
Har suka k'araso bakin board suka tsaya da shi da English teacher d'in idanunsu na a kanshi, shi kam bai ma san suna yi ba don idanunsa suna a k'asa yana kallon k'asa yayinda su kuma ko fahimtar bayanin English teacher wanda yake cewa "ga sabon copper shi zai dinga yi musu English a yanzu for 10 months, daganan idan ya gama service d'inshi ya tafi aiki zai dawo hannunshi kamar farko" basa yi, har sai da yace "Are u guys with me??"
Da d'an k'arfi, tukunna hankulansu ya dawo jikinsu, suka ce "Yes sir."
Banda Zainab wadda tayi mutuwar zaune, dan a lokaci d'aya ta ji bawan Allah n ya tafi da imanin ta.
Kasancewar Madu da Bashir sun gayawa Malaman su su dinga zaunar da su sit d'aya ita da Maryam ya sanya akoda yaushe suna tare, hakanan wani lokacin zainab sai ta kawo jaka ta saka a tsakiyar su wai kar jikin Maryam ya goge ta ta kwashi bak'in jini,
Amman yau kam zainab bata san lokacin da ta kamo hannun Maryam da k'arfi  ba!
Ita maryam d'inma tsorata ta yi dan kwata kwata hankalinta baya ajin, ya tafi ga takardar da take hannun ta tanata bitar debate d'in da za suyi da safen nan, kawai ta ji an damk'o hannunta kamar za a karya ta.
Kallonta ta yi amman sai ta ga hankalinta gaba d'aya baya tare da ita, wani wajen ma daban take kalla.
Da sauri ta kalli inda zainab take kallo ta ga englishi teacher yana ta zuba bayani a gaban board da wani balarabe a gefen sa da koren kaya a jikin sa....dan  haka ta juyo gareta cikin kulawa tace
"Zainab menene?"
Kallon ta zainab d'in ta yi sannan tace
"Maryam kinga wannan kyakkyawa ko?.
Dama haka ake ji a lokacin da ka ga wanda kake so? kinji yadda k'irjina yake bugawa kuwa? haka kike ji idan kika kalli ya Usman?"
Ta yi mata tambayar tana mai sake kallon saitin da copper d'in yake.

Wani farin ciki ne ya lullub'e Maryam dan rabon da zainab ta yi mata magana mai tsaho haka har ta manta...dan haka ta saki wani k'ayataccen murmushin da ya sake fito da ainihin kyawun fuskarta sannan ta d'ago kanta domin ta kalla wanda y'ar uwarta ta haukace a kai haka cikin lokaci k'ank'ani. Tana d'ago kan nata dai dai shikuma English teacher ya mik'a masa chalk yana cewa "introduce yourself to them."
Karb'a yayi sannan ya d'ago
daidai ita kuma Maryam ta  juyo tana murmushi a take idanunsu suka sark'e a cikin na juna! Bai san ya aka yi ba kawai ya ji chalk d'in dake  hannunsa ya fad'i k'asa!  Lokaci d'aya zuciyarsa ta hau bugawa da sauri da sauri....
Itama Maryam kusan hakan ne a nata b'angaren, jin yadda zuciyarta ke bugawa gashi ya tsareta da manyan idanuwanshi farare k'al masu kama dana mai jin bacci, hakan ya sanya ta saurin sunkuyar da kanta k'asa.
Maganar Mr Solomon ce ta dawo da shi daga duniyar daya tsinci kanshi a ciki dak'ik'un k'alilan da suka wuce.
Chalk d'in da ya yar yaga yana mik'a mishi sannan ya sake cewa "introduce yourself to your students."

A hankali ya saka hannunshi ya karb'a sannan ya sake juyawa ya kalli inda Maryam take a ranshi yana adduar Allah yasa ta sake d'agowa ya kalli fuskarta, domin kuwa baya jin akwai abinda ba zai tab'a gundurar sa a duniyarnan kamar kallon fuskar wannan extraordinary beautiful young lady d'in ba.

Ganin tak'i d'agowa ne yasa shi juyawa...a hankali ya k'arasa jikin black board d'in ya rubutu sunan shi kamar haka
'YAKUBU UMAR FAROUK M.T'
Sannan ya juyo ya kalli students d'in yace "that's my name, but u can all call me 'ABBA'
I'm your new English Teacher...."
Cikin nutsuwa ya karanto  musu tsarinshi kamar 'baya son surutu a aji sannan yana son in ya bada assighment a dinga maida hankali ana yi......'
Sai da ya gama tukunna Solomon yace "akwai debate d'in da ya basu as an assignment group A B and C".
sannan ya mik'a mishi textbooks d'in da suke hannunshi ya juya ya fita....

SO DA BURI Where stories live. Discover now