Chapter twenty two

11 1 0
                                    

So da Buri
Free Book
22

Kamar yadda Arshaad d'in ya fad'a, ranar litinin da yamma sai gashi ya zo. Wannan karon bai zo da Jamil ba shi kad'ai ya zo dan bayan tafiyar su ranar asabar Jamil d'in yayita yaba  kyawun Hudan yana cewa "ai yaga dalilin da yasa Arshaad d'in yazo ya mak'ale a irin wannan arean" har da cewa "In tanada k'anwa mai kama da ita ya had'a su, yanaso."
Shiyasa yau ya k'i zuwa dashi, dan in yana yaba Hudan ji yake kishi na neman kumbura mishi zuciya.
Kamar ranar farko, yau ma Yaro ya kira ya aika yace ace "Hudan tazo inji Arshaad"
Yau d'in Jalila tana makaranta suna tsakiyar jarabawa Umma kuma ta tafi yawonta ita da  wata bazawara y'ar k'anwar dillaliya da take zaune a gaban dillaliyar shiyasa abun ya zo da sauk'i.
Yauma Hudan bata dad'e da dawowa daga makarantar ba,
suna tsakar gida ita da Mama suna d'an tab'a hira, tana cin d'umamen tuwon masararta da miyar kuka Yaron ya shigo ya fad'i sak'on ya juya ya fita...
Rau rau Hudan tayi da ido sannan tace "Mama na ce mishi kin ce bana zance shine ranar yace 'yau zai dawo' ai na fad'a miki ko?"
Murmushi Maman tayi ganin yadda duk Hudan ta bi ta rud'e.
A hankali Mama ta mik'e ta shiga d'aki ta d'auko wayarta da pencil da y'ar k'aramar takarda sannan ta fito.
Har lokacin Hudan tana zaune tana cin tuwon ta.
Umartata Mama tayi da ta tashi taje ta wanke hannunta ta kai masa sak'o.
Yadda Maman tace haka akayi
Bayan tayi copying number Baban Sakina ta rubuta da sunanshi a jikin takardar ta bawa Hudan tace mata "gashi ta kai masa."

D'aki Hudan ta shiga ta d'auko hijabinta sannan ta fita zuwa wajenshi.
Motar ta fara ganewa dan da ita suka fara had'uwa, yana tsaye ya jingina a jikin motar yana daddana waya...
wata dakakakkiyar sky blue d'in shadda ce a jikinsa, d'inkin Boda mai d'an k'aramin hannu da hularshi zanna bukar itama sky blue mai d'an ratsi ratsin black a jiki, sai takalminsa na fata black wanda kana gani ka san mai mugun tsada ne dan sai wani kalar shek'i yake yi yayi wa fararen sawunshi mugun kyau.

Bai san ta k'araso ba dan gaba d'aya hankalinshi yana kan chatting d'in da yake yi da Yayansa.

Sallamarta ce ta dawo da hankalinshi wajen...
A hankali ya d'ago ya zuba mata kyawawan idanuwanshi kafin ya sakar mata wani tsadadden murmushi sannan
a hankali ya amsa.
K'asa tayi da kanta ta gaidashi,
Yanzun ma a hankali ya kuma amsawa yana mai tambayarta "ya gida"
"Lafiya" kawai ta iya ce mishi sannan ta mik'a mishi takardar hannunta tace gashi inji Mama, dan ita Allah Allah take ta koma gida saboda yadda yake ta faman kallonta....

Babu wani datti ko squeezing a jikin kayanta dukda iya hijabin yake iya gani baya ganin rigar dan hijabinnata ma ya kusan rufe zanin jikinta gaba d'aya
amman yadda kayan suka kod'e tashi d'aya zaka tabbatar da sun ji jiki kuma sun gaji da ruwa!
Tausayinta ne yaji ya lullub'e shi, ahankali ya fara tunanin ta yadda zai yi ya taimaka mata dan gaskiya suna buk'atar taimako. 
Ga gidan nasu ma kanshi yana buk'atar a d'an gyara shi
Gabansa ne yaji yayi mugun fad'uwa da ya tuno da Granpa domin kuwa ya san ko a verge of death yake wallahi Granpa ba zai tab'a yarda ya barsa ya  auri Yarinyar data fito daga irin wannan gidan ba!
Ajiyar zuciya ya sauk'e a ranshi yana cewa "tabbas he has to do a lot kafin ma yaje ya fara nunata.....dan he don't think he can keep on living idan aka yi tunanin rabashi da Hudan!
Shi fa har mamaki yake yi ta yadda kawai lokaci guda yaji yana mugun mugun sonta!
Dan ko lokacin da yayi tafiya ji yake kamar yayi hauka, a gaggauce ya gama aikin da aka turashi ya dawo dan kawai ya samu yazo ya ganta.......
"Zan tafi, sai anjima."
Shine abinda tace masa wanda yayi sanadiyyar dawo da hankalinshi wajen.

Murmushi yayi sannan ya ware takardar ya duba...
Number waya ne a ciki an rubuta Alhaji Muhammad a saman.
Kallon ta yayi kafin yace
"Your Dad??"
Yayi mata tambayar yana mai nuna mata number.

Kallon sunan tayi, sai da 
ta had'a gumi tukunnan kwakwalwarta ta iya karanta mata 'Muhammad' d'in amman abun farkon kam sam ta gagara karantawa ita dai taga 'A' da su 'L'.
Kalmar Muhammad d'in ta furta mishi.

SO DA BURI Where stories live. Discover now