Chapter eighteen

12 1 0
                                    

So da Buri
Free Book
18

Babu inda ba a duba ba, amman babu Maryam babu alamar ta, gaba d'aya hankalin kowa a tashe yake, tunba ma da Innaa ta dawo daga kasuwa nik'i nik'i da kayan d'aki ba!.
Babu kalar zagin da bata yiwa Madu ba, Mallan shima yana k'arasowa ya iske mummunan labari.
Har dare basu zauna ba domin shi Madu ya dage akan 'bai yarda Maryam guduwa tayi ba!'.  Sune har police station
da daddare bayan sallar Isha........da kyar suka iya cin abinci tun safe.....

Suna zaune a gidan Madun, Inna tana ta yada magana tana cewa "Madu ya janyo musu abun kunya! Itakam Allah ma yaso ta tunda idan aka bi tsattso ba a jikinta ya fito ba!! Kuma kowa ya san Shuwanta bata da laifi..."waye waye....
Har sai da taga ran mallan ya b'aci ya fara yi mata bala'i shima, tukunna tayi shiru.

Sallamar da aka yi da Madu ce ta katse mata guna gunin da take yi akan 'itafa shiyasa tun farko bata so auren Shuwa da Madun ba'.....

Cikin mutuwar jiki Madu ya mik'e Baba Bashir yana binshi suka fita tare domin amsa kiran da ake yi mishi a waje!.
Suna fita suka tarar da dattawan unguwar, da sauri Madu ya k'arasa ya shiga basu hannu yana tambayar su "ko lafiya??" Dan shi a tunanin sa  anga Maryam ne. Amma sab'anin hakan sai yaji wai 'su meeting d'in gaggawa suka zo ayi saboda guduwar da y'arsa tayi, domin kuwa y'an unguwa sunce ya kamata a chanza sabon Limami.!'
Da mamaki yake kallon su, shi yana ta neman y'arsa, su kuma suna ta muk'ami! shiyasa ba tare da b'ata lokaci ba ya sanar musu da 'ya sauk'a!'.

Amman hakan bai sanya sun barshi ba saida suka jashi akaje wajen meeting d'in.
Suna zuwa yaga dubban mutane, su kawai ake jira.!

Sai a wannan lokacin Madu ya san ba K'asimu kad'ai ba ne mak'iyinsa a layin!! Harda waenda yake ganinsu Abokanan sa duk cikinsu babu ya bi bayanshi..
Mutum uku ne kawai suka bi bayan Baba Bashir wanda Allah sarki dudda halin da Usman yake ciki bai sa ya juyawa Madun baya ba.

A lokacin mutanen gurin rabuwa sukayi kashi uku
Kashi na farko 'sune su Baba Bashir su hud'u!'
Kashi na biyu 'sun ce, y'ar Madu tayi laifi kuma shi ya janyo tunda shine ya shagwab'ata kuma baya son laifinta, amman bai kamata ace laifinta ya hau kanshiba, har a kai ga sauk'e shi ba'.
Kashi na uku kuwa (su K'asimu) sunce 'ai laifinshi ne y'arsa ta gudu yawon karuwanci, tun farko shine ya yi mata lagalaga ya shagwab'ata, baya tsawatar mata duk abinda takeso baya hanata! Haka k'iri k'iri aka koreta a makaranta saboda abunda take yi amman ya rufe yak'i gayawa kowa idan an tambayeshi sai dai  yace chanza  mata makarantar yake son yi! Ai y'an unguwar da aka taso sama da shekaru ashirin da biyar tare ya kamata ace yanzu an zama d'aya dan haka su ba zasu dinga bin mutumin da yake ha'intarsu! Sallah ba. Su idan matsala ta taso a nasu gidajen tuni sunzo sun saki baki dan neman shawara da yarda da juna, amman shi y'arsa daya kamata ace tun kafin abun ya kai haka a taka burki yak'i yarda ya bada k'ofar yin hakan kuma shima ta bangarenshi bai yi ba, gashi yanzu ta tafi tabi saurayi.
Saboda haka..
Su baza su bi uban karuwa ba a masallaci har ma da unguwa.'
Harda cewa 'ci yake yi da addini.'

Nan suka fara jidar kaya za suyi zanga zanga!
Dattawan unguwa na ganin haka suka hau basu hak'uri, sannan a take aka sake sauk'e Madu daga matsayinshi na mai unguwa ma gaba d'aya!
Dan a samu a zauna lafiya.

Babu kalmar da ta fi b'atawa Madu rai irin na kiran 'Maryam karuwa da aka yi'
Shiyasa tun baya mayar musu har ya zo yafara mayar musu da martani, da kyar Baba Bashir ya janye sa suka bar wajen sukayi gida.
Dishi dishi kawai Madu yake gani, bai san ta Ina zai fara ba,
Da kyar ya iya kai kanshi gida.
Yana shiga Inna ta tisa shi a gaba da tata mitar, harda d'akko mayafinta tace 'sai ya kaita gidan Yayan Abba! Ai sunce sun yi bincike dan haka ya kaita ko wajen wani nashi ne...'

Madu kuwa tun rana, suke ziryar zuwa ganin Alhaji Yahaya amman mai gadi yace musu wai yace 'kar a barsu su shiga!!'. Shiyasa ma abun ya kuma dagule musu, amman dai basu fad'awa kowa ba suna so  suyi settling ne a tsakaninsu,
shiyasa yanzu furucin Inna ya sake rikitashi!.

SO DA BURI Where stories live. Discover now