Chapter twenty nine

20 2 0
                                    

So da Buri
Free Book
29

Kafin minti ashirin Kaka, Madu, Shuwa, Baaba Talatu, Baaba Laraba da K'asimu sun k'araso cikin gidan!.
Baaba Laraba sai lallashin y'arta take yi itama tana nata kukan.
Baba ne ya shigo a k'arshe daman shi ake jira, dan haka yana zuwa su Kaka sukace "ba b'ata lokaci, bara a bi sahun su...".

Sai a lokacin tukunna Sakina tayi magana, tace
"Sun tafi da shi Lagos fa!".

Wani uban ashaar!! K'asimu ya buga sannan yace
"Wai wannan wanne irin rashin mutunci ne!
Haka kurum sun zo sun tafi da Yaro, kuma bama zasu barshi a nan ba sun kama sun kaishi har Lagos!! Sai kace wanda akace yayi kisan kai!
Sun fad'a muku laifin da yayi??".

Cikin Kuka Hudan ta share hawayenta sannan tace
"A jikin takardan cewa aka yi wai 'sun yi fashi su uku a gidan cheif justice jiya kuma sun kasheshi sun kashe y'ay'an shi hud'u!".

Salati tsakar gidan ya d'auka, gaba d'aya. Baba kuwa dab'ass!! Haka ya zauna a k'asa...
Da sauri Umma tace "wallahi k'arya ne, sharri aka yi mishi, Junaidu tun yana Yaro ko cinnaka idan ya cije shi baya kashewa ballantana mutum, wallahi k'arya ne."

Kaka ne yace "Sadiya ki yi shiru, kowa anan ya san k'arya ne, abun da ya kamacemu yanzu shine addua sai kuma mu nemo lawyer mu fara k'ok'arin fitar da shi ko?
Tunda kunga har an tafi dashi."
.....
Nan suka hau shirye shirye aka ware masu tafiya Lagos d'in, sannan suka kira Ya Jamilu (Yayan Baba) shima.
Kuma suka nemo lawyer sannan aka yi shirin tafiya.....
Gidan Ummu za su fara zuwa su tambayi Mijinta akan ya barta a tafi da ita tunda lawyer ce itama mai zaman kanta..

Hakan kuwa aka yi a ranar zasu bishi.
Sai da suka raba sauk'ar Al Qurani da addu'o'i a wajaje daban daban, sannan suka d'au azumi kaff d'insu, har Jalila wadda rabonta da azumi har ta manta wai tana da ulcer Umma kuwa ko da yaushe cewa take yi "ai Allah ma ya ga zuciyarta kuma shine ya d'aura mata rashin lafiyar".

Baba, Madu, Ummu, Kaka sai d'ayan lawyern da aka tafi da shi ne suka kama hanyar Lagos, sai washegarin ranar tukunna suka samu kansu bayan sunyi settling a hotel d'in da suka kama lokacin
Ya Jamilu shima ya k'araso dan haka ba tare da b'ata lokaci ba suka nufi inda aka kaishi!.
A nan ran Kaka ya sake b'aci da yaga wajen da aka kaishi  d'in! Shi da ba a gama tabbatar da laifin shi ba saboda Allah meyasa zasu kawoshi prison?!

Haka nan yayita fad'a su Ummu suna bashi hak'uri... da kyar yayi shiru suka nufi gate d'in..
Kalar binciken da ake yi musu duk wanda ya gani zai yi tunanin 'sun zo ganin wani hamshak'in d'an ta'adda ne'. Kuma dukda haka cewa akayi "sai dai mutum uku su shiga ba zai yiu su shiga su duka ba!".
Baba, Ummu sai d'ayan lawyer d'in da aka tafi da shi ne suka shiga, shi kam Ya Jamilu ID card kawai ya nuna musu ya wuce...

Bayan y'an gwaje gwaje aka kaisu wajen zama (chan gaba da parking lot) aka ce "su jira shi a nan"
Anfi 30 minutes tukunna aka fito da shi.

Daga nesa da ya taho basu gane sa ba sai da aka matso dashi aka zaunar, tukunna.

Kuka kawai Baba yasa yayi saurin tashi a wajen.
Mai tsaron da ya kawo shi ne ya had'asu ya bashi iya lokutan da yake dasu sannan yad'an koma gefe kad'an ya tsaya.
Ganin basu da isheshshen lokaci yasa Ummu tace
"Junaidu, how are you?"
Ahankali muryar shi baya fita sosai yace
"Alhamdulillah"
Ba tare da b'ata lokaci ba tace
"ya aka yi? Mai
ya faru? Me 
ka sani?".

D'an gyara zama yayi tukunna ya fara magana.....

"......shekaran jiya da daddare  ina d'akin Abokina.

Ba a Kano yake ba, a nan Lagos yake, amma yana da apartment a Kano d'in.
Shekaran jiyan ya kira ni yace mini 'zai shigo gari amman a jiya zai koma kuma akwai wani aiki da za muyi akwai samu a ciki sosai!
In da hali yana son ganina sharp sharp'.
Nan da nan nace mishi gani nan zuwa.
Ina zuwa ba tare da b'ata lokaci ba ya hau yi mini bayanin business d'in..
..'Wake ne zamu kawo daga Taraba, ko wanne a kan 9k zamu siya amman idan yazo Kano zamu iya siyarwa a kan 23k!
Kuma kud'in mota dududu bai fi mu biya dubu arba'in ba dan ya san wani me mota da suke irin wannan harkar, sannan za a kawo mana buhu sama da d'ari, a mota daya!'.

SO DA BURI Kde žijí příběhy. Začni objevovat