...30...

575 12 1
                                    

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[30]

Goje baya nan,dan haka da ƙafata na taka zuwa gidan,kasancewar ba wani nisa ne dashi sosai ba.
Lace ne a jikina mai kyau a jikina wanda goje yayimin,sai hijabi dana saka da takalmi,naƙara fari da ƙiba ainihin siffah ta ta jin daɗi ta bayyana,ko makaho ya shafani yasan na sanja fiyeda da..
Sallama nayi daga shigata gidan,kasancewar ƙofarmu na dan ciki saida na gaisheda matan dake wajen tukunna.
Suma kallona suke da mamakin sanjawar tawa.
Wucesu nayi zuwa ƙofar tamu,ammi tana zaune da tiren gyaran shinkafa a gabanta,faɗi in faɗa suke da rammah wacce take daga cikin ɗakinta.
"Haka kawai dankin rainani kinga bana magana,lokacin da aka kawo Sumaimah nina ɗauketa,wannan kuma har an baki kice wajena zata dawo? To naji da nawa tarin gayyar mana,ba kayanta dazan ɗauka,kuna nan dake da itah mutu ka raba,indai kin auren ubanta. Yo ubanta mana tunda ya riga ya lakato ai dole ya tanɗe"
Sallama nayi ganin abinnasu ba ƙarewa zayyi a lokacin ba.
Ammi ce tafarayin shuru tareda ɗagowa ta kalleni,murmushin ƙarfin hali nayi mata kana na zauna a wata ƙaramar kujera a gefenta.
"Lahh Sumaimah kece a gidan"
"Ammi na sameku lafiya ya gida?"
"Uhm gida kam gashinan mana,kekam ai kinji daɗinki,muna jin labarin goje ai a gari yazama tamkar ba shiba"
Uhm kawai nace,daga zuwa sai zancen daɗi kawai,koda yake haka gidannamu suke,basuda aiki sai zancen ayi auren yarinya ta huta,a ga mai take sakawa kokuma mai take ci,sannan ya kuɗin mijinta.
Wata maganar da rammah tayine ta katseni daga tunanin.
"Ahh lallai kam,tayi bulbul da ita ga zahiri nan ma harda shigar ciki,da alama shine yasaka ta kyan bawai zallan jin dadin bane yanda ake tunani"
Wani takaici ne ya cikani amma haka na shanye,wai basuda abin faɗa sai wannan ne,ita kam inna rammah ko gaisawa bamuyi ba da itah,tafara zancen da bai shafeta ba.
"Ammi ina baba kuwa,ko ya fita?"
"Wai ya fita,tun safe ya tafi akan magana gonarsa rabin,ya siyar da ɗayan ai kuɗin ya bata,shine har kika samemu a asibiti wancan karon,to zancen ya tafi yau ma..
Shiga ɗaki ki cire hijabin mana,sannu da zuwa ya innar gojen?"
"Tana nan ƙalau"
Hira muka dan fara tabawa,wanda yawanci na abubuwan da suka faru bana nanne,muna tsaka da haka najiyo kukan yarinya tundaga bakin shigowa gidan,saikuma muryar Musbahu yana magana kaman mai faɗa.
Butt suka shigo a ƙofar yana riƙe da hannayenta,sai dadare take tana jijjiga kai.
"Kayi min rai yaya Musbahu wlh bazan sake fasawa kowanne yaro goshi ba daga yau,Allah da gaske nake"
Ihu take kan gari ya gari kowa na jiyota a gidan,abinda yabani mamaki babu wanda ya kulada sha'anin,har inna ma batace komai ba sai cigaba da tayi da aikinta. Hakanne yasa na gane cewar Deejah ce yar baba uwaisu daya samo a caca,wacce nake jin labarin ta..
Bulalar hannunsa ya zuba mata a gadon baya,ta kuwa sake ƙara saurin kukannata,ganin bazan iya jurewa ba yasa na tafi da sauri na karbeta,lallai itama wannan da sakarci take,ta kusana girman jiki amma take abin yara haka.
Haƙuri na fara bashi tareda janyeta daga hannunsa,har sannna bai kulada ni ba sai dukanta yake.
"Kayi haƙuri yaya Musbahu duka baya magani ko kaɗan,kada ka jimata ciwo a garin gyara"
Sakin hannunta yayi ta zube a wajen tana burburwa. Shikuma sai numfashi yake sakewa kaman wanda yayi faɗa da bijimi.
"Hmmm ƙyaleni Sumaimah na koya mata hankali,bakisan abinda tayi bane shiyasa,ɗan shugaban makarantar fah ta rotsewa kai,kuma a hakan bai isheta ba za'ayi mata hukunci ta zazzagi malaman da sunyi jikanu da itah,shine yanzu suka ƙirani kan naje na tafi da itah sun koreta a makarantar. Wannan fah itace makaranta ta uku dana sauya mata,banida buri illah naga tayi hankali,amma ita da alama ba hakanne a ranta ba,a na tausayinta bata tausayin kanta"
Yana nunata yake maganar,kana gani kasan ransa ya baci sosai. Maida idona nayi kanta,tana sunkuye tana rira kaman wata ƴar bori.
"Kayi haƙuri yaya Musbahu komai da sannu zai wuce kaman bai faru ba Inshaallah"
"Hmm Allah yasa,sannun ki dazuwa ya gidan?"
"Lafiya kalau nake"
"Barina je na dawo,yawwa inaso muyi magana dake  amma barina sauya kaya tukunna"
To nace masa daga nan yafita daga ƙofar,komawa nayi wajen zamana na zauna ina kallon Deejah wacce ta dasa aikin kuka a tsakar gidan,kayan makarantar tata sunyi butu butu dasu. A yanayin girmanta bai kamata a ace tana haka ba. Su ammi har akayi aka gama babu wanda yayi ko tari a cikinsu,da alama sun saba ganin hakan ba yau ne farau ba.
Wata kazace tazo zata wuce,aikuwa takai mata cafka kaman wata kuliyah,saurin tsallakewa tayi ta gudu domin ta tsira da ranta.
Wata mata ce daga cikin matan gidan tayi magana.
"Ahah dakata kada ki huce akan kazata bataji ba bata gani ba,inkuwa kika kasheta saina faɗawa wanda ya dakekin ya ƙara miki"
"Yiiii Ki faɗa ɗin mana,ina ɗan ki zaizo kwanciya da daddare koh,wlh saina sanja masa kamanni,ƴar matsiyata kawai"
Zaro ido nayi ina kallon yarinyar,wai dama haka take ashe,babu wanda tabari a gidan da jarabarta,gaba ɗaya ta zame musu ƙarfan ƙafa. Shikam uwaisu yanzu ko hanyar gidan cacar bayayi,gani yake kaman za'a ƙara bashi wata Deejah. Wancan satin ɗakinsa ta shiga zata yankashi d wuƙa a hannunta,wai taji labarin bai kawo kuɗin cefane ba kuma yunwa take ji. Tunda bazai ciyarsu ba toh bashida amfani. Tun daga ranar kullum sai ya iyo cefane yakawo gidan,ko yana dashi ko shida shi,dan daga taga ba abinci zata fita neman sa a garin,kowa ma yasan hakan.
Shiyasa ba shiri ya maida hankali kan sana'arsa,gashi sai taga Musbahu baya nan takeyi,ba wanda kuma ya isa faɗamasa in ya dawo saboda yana tsoron ta huce akansa.
Nidai na daɗe a nan zaune ina kallon ikon Allah.
"Khadija ki tashi a ƙasannan haka,babu kyau mace ta dunga zama a ƙasa,Sannan kinga kayanki duk sun baci da datti kaman ba babbar yarinya ba,ko so kike yara su rainaki kai?"
Cikin sigar rarrashi da jan hankali nayi maganar,yanda zai ɗau hankalinta. Aikuwa nayi nasara,dan tayi shuru dayin kukan,amma bata daina tofah yawu a gaban hijabin ba.
"Kinga shi wanda aka dukaki akansa yana can yayi shuru kuma bai bata kayansa ba,idan ya ganki cewa zayyi ashe ma ba ƙarfine da itaba,tunda ni nayi shuru ita kuwa tana kuka,zaice ma yafiki ƙarfi,hakane?"
"Ahah wlh nafishi ƙarfi,niba sa'ar sa bace"
"Yawwa to kin gani,kuma inkina faɗa da maza darajarki da mata zata zube,ko so kike duk inda kika wuce a dunga cewa ga wannan wacce take faɗa da mazan"
"Na daina toh"
Tashi tayi daga ƙasan tafara kakkaɗe kayanta,a dole ita kar a ce tayi datti,hakan da tayi ba ƙaramin dariya yabani ba,batada girman kai kaman goje,a haka ne mutum zai gansu sunada wuyar sha'ani,amma idan mutum ya zauna dasu a hankali zai gano sauƙin kansu.
Gyaran murya Musbahu yayi ,ashe yana wajen lokacin da nake magana da Deejah,har ta tashi daga wajen ta nufi ɗakinsu..
"Ban taba ganin tayi abu cikin ruwan sanyi batareda duka ba sai yau,da alama magana zata iya yin amfani a kanta kenan"
"Hhhh yaya Musbahu kenan,shin akwai wanda magana bata tasiri akan sa ne,har zaki ma ai yana jin magana wani lokacin"
"Abinda ya faru har yasake tunamin abinda nake son faɗa, wani satin zan tafi training na aikin sojoji,shine nakeson barmiki kulada Deejah a hannunki,bawai zata zauna a wajenki bane,illah dai koda sama sama ne ki dunga bincikar ya take,sannan ki ɗan ja ta a jiki tasan abubuwa a matsayinta na ƴa mace,yanda zata kula da kanta"
Dallla dalla yakemin maganar ina saurarensa,haƙiƙa ya burgeni sosai,kuma nayi na'am da wannan taimakon dayake shirin yi,harni ma yasakani a ciki,mai zai hana na taimaketa kuwa,indai abinda zan iyane.
"Ba damuwa yah Musbahu karka damu,Inshaallah zanyi iya kokarina,kai kuma Allah yabaka sa'a ya tsareka daga mungun abu da mungun nufi"
"Ameen ya Allah nagode sosai"
Muna cikin hirar ne naji wayata tayi ringing,ɗaukowa nayi nasan bazai wuce goje ba,ko ya faɗamin sun isa..
Da murmushi na na ɗaga wayar,saidai abinda naji a ɗaya bnagarenne yasa yanayin fuskata ya sanja nan take,jikina ya tsaya da aiki na wani lokaci,iyah ƙwaƙwalwata ce kawai take aiki sai jinin dayake bugawa a cikin zuciyata kaɗan kaɗan.
Sakin wayar nayi ta faɗi a saka yayinda fatar bakina tafara rawa ina rarraba idona akan su ammi da yah Musbahu.
"Ya....yahh yah Musbahu mmmi.....mijinah ya Musbahu mijina kukaini wajensa yanzu na roƙeku"
Ganin nafara maganganun da bansan mai nake cewa ba ne yasakashi ɗaukar wayar dan yaji mai naji..
"Hello hello Sumaimah kina jina,muna general hospital anan gwagwaladan sun shiga dashi emergency,saboda kansa ya bugu sosai"
"Ba ita bace yayanta ne Musbahu,Tunga bai kamata ka fada mata,wannan maganar ba,yanzu dai karka damu gamunan zuwa garin,yanzunnan zan kawota"
Yana kashe wayar ya fita waje da sauri,jan lilon ƙafata nayi dasauri na bishi wajen,saboda kada ya tafi ya barni,dan ji nake idan bangnashi ba bazan iya sukuni ba.
Ina fita naganshi yana tada mashin ɗinsa,ban tsaya tambayarsa ba kawai na ɗale.
Gidana muka tafi domin sanarwa inna abinda yake faruwa,a Ƙofar gida ya tsaya nikuma nashiga ciki domin sanarwa mata.
Tana zaune da tukarta a gabanta daga na faɗo gidan ko sallama babu,kaman banice mukayi sallama da itaba na tafi gida ɗazu..
"Hasbunallahu Sumaimah lafiya na ganki haka kaman an jefo ki?"
"Inna goje yayi hatsari inna kizo muje da sauri mu ganshi"
"Innalillahi wai inna ilaihi raji'un yanzun ke daga ina kike?"
"Uhn tare muke da Musbahu a mashin ɗin sa zai kaini. Inna karki damu ki shirya barina je inyaso saiki taho"
Ina faɗamata hakan nafita daga gidan batareda na jirata ba,saboda bana cikin hankalina ko kaɗan.
Tafiya muke a mashinɗin amma gani nake kaman baya sauri.
Munsha iska kam saboda tafiyar da ɗan nisa sosai,amma ko kaɗan bata wannan nake ba,burina na isa naga mai yake faruwa dashi..
Kai tsaye babban asibitin muka wuce,bamusha wahala ba tunda munsan inda aka kwantar dasu,wato a emergency..
Muna shiga ward ɗin wajen bada suna muka nufa,bakina har rawa yake wajen fadamata sunan wanda aka kwantar.
Muna cewa goje suka gane,dan sunan da Tunga ya shigar kenan.
"Am sorry madam patient ɗinku yana dakin tiyata basu fito ba tukunna,amma ku shiga ɗakin can akwai wanda aka kawosu tare"
Bin hanyar data nuna mukayi ,ina gaba Musbahu yana bina a baya,ɗakin mukashi anan nayi arba da Tunga a kwance an naɗe ƙafarsa da bandeji..
Cikin sauri na isa bakin gadonnasa,cikeda zumuɗin jin amsar tambayata,duk kuwa yanayin Tunga ma bamai daɗi bane,amma daga gani zai iya magana.
"Tunda mai yafaru,ya akayi kukai hatsari,meya sameshi,yaji ciwo sosai,zai tashi ko........"
Yah Musbahu ne ya dafa kafaɗa saboda ya tsayar dani daga tambayoyina marasa adadi.
"Ki kwantar da hankalinki Inshaallah zai samu lafiya"
Ya Musbahu yafaɗa cikin tattausar murya.
Muryar Tunga naji wanda dama ita nakeson ji yanzu,saboda amsoshina.
"Nima wlh Sumaimah bansan mai ya faru ba,kawai muna cikin tafiya yana tuƙawa,shigowarmu garin kenan kawai sai gani nayi yasake kan mashinɗin kaman wanda ya suma,kafin na ɗagoshi har mota ta hau kanmu,kasancewar shi baya cikin hayyacinsa shiyasa buguwar tayi masa mummunan rauni akai. Shine mukazo a asibitinnan,amma batun sauƙi kam saidai a wajen Allah"
Ban gama jin maganar Tunga ba naji wata nurse ta shigo.
"Am wacece mrs goje"
Ɗagowa nayi tareda kallonta,itace wacce ta nuna mana ɗakin Tunga.
"Am sorry to say,amma likita yace kuyi shirin tafiyah babban asibiti a abuja,domin yasamu ciwo sosai a kansa,ko motsi bayayi har yanzu. Ki kwantar da hankalinki fah zai samu sauƙi"
Hmmm zancen kwantar da hankali takemin a wannan yanayin..
A bakin gadon Tunga na zauna ina yaƙi da numfashi na dayake cikowa.
Ina cikin wannan yanayin inna ta iso,itama dataji abinda yake faruwa ba ƙaramin kiɗima tayi ba.
Ƙarar tura gado naji irin na aikin tiyata,hakan yasa na tashi tsaye ina kallon masu turowar,mutumin dana rabu dashi ɗazu muna zance,shi ake turomin akan gado kaman gawa.......

Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan
09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan
09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

SANADIN CACAWhere stories live. Discover now