...20...

491 16 3
                                    

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[20]

Zamana na gyara a tsakiyar gadon na saka wannan kayan daɗin a gabana,saida na cinye indomien tass kafin na buɗe peak ɗin,itama gamawa nayi da itah na ɗauko itama maltinar. Saidai ita ban sha dayawa ba na ajiye,dan batayimin daɗi sosai ba kaman wancan madarar.
Wata nurse ce ta shigo ɗakin hannunta ɗauke da littafi tana rubutu.
"Mrs goje ruwanki ya ƙare koh?"
Tafaɗa tana kallon hannuna na hagun,oh ni na manta da ruwan dayake shiga jikinnawa ma.
Matsawa kusa dani tayi ta zare ruwan,iyah canular kawai tabari a jiki.
Murmushi tayimin da muka haɗa ido.
"Hhhh kin burgeni wlh,bakida lafiya amma kin cinye abincinki tass"
Kunya ce ta kamani,hakan yasa na sunkuyar dakai,hmm batasan rabona da abinci ya isheni bane shiyasa.
"Karki damu babu wata matsala,tunda kina cin abinci basai an sake saka wani ruwan ba,ga magunnan dazaki dunga sha da shafawa duk ya siyo ɗazu,saiki dunga kulawa sosai karki ƙara taba abinda jikinki bayaso"
Ɗaga mata kai nayi alamar na fahimta.
Har tazo fita saita sake dawowa,
"Yawwa ya kawo kaya akan ki sanja,dan haka idan kin gama kizo office ɗinmu daga kin fito ta gefennan kiyi wanka,yace yana zuwa yanzu"
"Ohh nama gama bari kawai mutafi"
Binta nayi a baya a hankali har muka isa office ɗin nasu da tace,a matsayina nasan bankai har a kaini wajen ma'aikatan jinya nayi wanka ba,ya danganta ne da wanda ya kawonin shiyasa ka.
Bayan nafito daga wankan bandegi da sake sauya min na hannunsa,wanda na ga ashe sun cire fatar jikin hannun ne. Doguwar riga ta miƙomin maroon mai kyau da mayafinta,sai pad dakuma pant.
Karba nayi na koma banɗakin na shirya kafin na sake fitowa.
Kasancewar ban iyah surutu ba musamman da wanda bansani ba,shiyasa na zauna nayi shuru.
Muna nan zaune kaman kurame naji muryar gojen suna magana da wata nurse,lokacin ana ƙiran magriba a wasu masallatan.
Yana shigowa dani muka haɗa ido,nayi saurin sauƙar da kai,wai karfa in mukaje gida ya casa ni,dana tuno rashin kunyar danayi masa jiyah.
"Oh sainace ki fito tukunna zakizo mu tafi,ko baki ganni ba kai"
"Uhm naganka"
Binsa nayi kaman jela a baya ina ta kakkare jikina saboda mayafin bashida girma,dan ma dare ya ɗan fara shiga.
Wani mashin naga mun nufah sabo irin bajaj ɗinnnan mai babban mazauni a baya.
Saida ya hau yafara diri kafin na hau bayan,dadumeshi nayi ƙanƙam,saboda ban taba hawa mashinba.
Nasan yajini dan har ƴar tsuka yayi amma baice komai ba.
A hankali yake tafiyah wanda nasan saboda nine har muka iso gida.
Sauƙa nayi daga kan mashinɗin ina rarraba ido.
"Nagode"
Nafaɗa a hankali,bai kalli inda nake ba ballantana ya amsa,duk da nasan yajini sarai.
Kafe mashin ɗin yayi ya nufi cikin gidan,nima binsa nayi a baya,mamaki yabani ganin ba hanyar ɗakinsa yayi ba.
Ɗakin ya shiga ya tattaro kayansa wanda ya juyemin su a jikina,harda zannuwan gadon wanda ya nabata da jini da kuma ruwan daya zuba duk ya tattaro ya fito dasu waje.
Ɗakinsa ya sake nufah sai gashi da bargonsa da zanin gadonsa nan ma.
Dukka zubasu yayi a gabana,nidai ina nan tsaye ina kallonsa,jikina har yafara karkarwa,kaddai yana nufin a darennan zan wanke duk uban kayannan kai?.
Wuceni yayi ya shiga ƙofar gaji,can sai gashi ya fito Atika tana binsa a baya, itada kursiyyah.Taci kwalliya da alama fita zatayi a daren.
A tsayawa suka yi a gefe dani suna kallonsa.
"Ku ɗauki wannan kayan ku wanke su a darennan,idan har suka kai gobe baku gama ba wlh kunji na rantse sai na ɗaureku na tsawon satin bakuga rana ba.
Sannan idan kungama ku cikamin randa ta da ruwa"
Sakin baki mukayi haddasu muna kallonsa,hanyar ƙofar sa ya nufah hankalinsa kwance.
Bayan ya tafi juyowa atika tayi tana kallona.
"Wannan aikinkine ko,kema nan tantiriya ko,wato bari ki juyashi shikuma ya juyamu,toh baki isa ba,dan kuwa ke zaki sha wahala ma idan hakan za'ayi,ina zai tafi ya barki a gidan"
"Menene me naji ana cewa ne? Kekam ba fita zaki bane mai kike anan,ko ta dawone dama ba mutuwa tayi ba da mukaga ya fita da itah"
Kallon gaji nake tasaka wani figalallen hijabi,da wani zaninta mai kama da three quarter na wando,wai a hakan sallahr magriba da dungura,wato da suka ga yafita dani ɗazu so sukayi ace na mutu.....hmmm mai nayiwa waɗannan mutanen suka tsaneni ne?
Ganin gaji tafito yasa Atika rushewa da kuka tana bubbuga ƙafa,kaman ba itace take magana yanxu ba cikin tsiwa..
"Gaji kiji wani sabon salon iskanci,ɗazu da kikaga yafita dai itah,ashe suman ƙarya tayi,suka fita taje ta kitsa masa munafurci,yana shigowa ya jibgo wannan uban wankin wai mu yi shi a darenann,nida ko nawa ma bannayi shine zaice wai muyi mata wankinta da nasa??? Nikan wlh gaji bazan iyaba,Allah gaji ki ɗau mataki"
Atika ta faɗa tana rushewa da kukan munafurci.
"Ke ƴar nan mai kikecewa,ayi mata wanki,akan uban me za'a maida ƴaƴana bayinki,ƴar gwamna ce ke ko ƴar sarki,toh wlh baxai yiyuba komai za'ayi saidai ayi,kuma kwanon abincin ki a gidannan babu shi,idan yunwa zata kasheki ma saidai ta kasheki"
Nidai ina nan tsaye in jinsu,ganin jiri yana ɗibana yasa na juya zan shiga ɗaki.
Gaji ce ta jawoni baya ina shirin faɗuwa,da ƙyar na tsaya akan ƙafafuna. Hannu ta ɗaga zata shararamin mari,da sauri na rife ido ina jiran naji da wanne waje zai saƙƙo.
Naji ƙarar marin amma kuma banjishi a kuma tu na ba.
"Kambuuu nika mara goje ina matar kawunka zaka mareni,saboda kai......"
Wani marin yasake kifa mata ta ɗaya kuncin daidai buɗe idona,kutt dama goje gaji yamara,kai matar kawunnasa?..na faɗa a raina ina zare ido.
"Kona daɗa miki ne,kukuma saboda kun rainani nasakaku aiki maimakon kuyi shine kuka tsaya kuna zage zage koh,ku faɗamin Nida na sakaku kuke zagi kokuma itah. Duk ina sane da abinda kuka aikata bananan,har kayana kuka ɗauka kuka saka a wajen kashin shanu ko?....daga kyau aikin gidannan kaff nasake ganin wanda yasakata tayimasa,saina cire masa ƙafafu da hannaye,in yaso ayi masa aikin da dalili"
Ƙwafah yayi mai ƙarfi yafita waje yana huci.
Oh ni inaganin ta kaina a gidannan,ko ina ba sauƙi.
Ɗaki na wuce na barsu a wajen,duk yadda zasuyi ma suyi.
Can wajen goman dare har nayi bacci naji ana buga ƙofar tawa.
Buɗewa nayi muka haɗa ido dashi,ledar dayake hannunsa ya miƙomin,hannu nasaka na karba ya bar wajen..
Bayan na koma ɗakin zama nayi na buɗe ledar,soyayyar doya ce da ƙwai sai balangu,ikon Allah mai ya shiga kan gojene yake siyomin waɗannan abubuwan.
Bandai sake kawo tambaya tabiyu ba nafara kaiwa cikina.

        ___***___

*Overall military security headquarter division in barrack*

...ABUJA...

Tashi yayi tsaye cikin bacin rai ya buga hannunsa akan desk ɗin,wani tafarfasa zuciyarsa takeyi na bacin rai. Ga girma yazo masa amma common case ɗaya ya gagara gamawa dashi ya huta?.
Runtse ido yayi tareda cije fatar bakinsa ta ƙasa..
Kallon Gen Saeed yayi wanda yake gabansa a Tsaye.
"Kana nufin kacemin har yanzu baku gano sansanin Wannan ƙungiyar BC ba"
"Eh ranka ya daɗe,har yanzu bamu gano daga inda suke ba,Banida cikekken bayani sosai akan su har yanzu,gashi cibiyar tsaro ta ƙasa Civil security headquarter tana buƙatar karban aikin,saboda wannan a harinnasu na ƙarshe a gwagwalada sunyi babban ta'adi sosai"
"Ta bincike akan su yana tafiyah normal,meyasa yanzu ake samun matsala akai?"
"Ranka ya daɗe kafin na karba Gen Ahmad Aliyu Hamma ne yake jan ragamar binciken,to tunda ya rasu kuma......"
Shuru yayi yana kallon fuskar Air mershall Aliyu Hamma,saboda ambaton ɗan sa dayayi kar abin ya kasance cikin matsala,saidai kuma ya kula hankalinsa baya kansa sam.
"Shirya min koma gida David,kafin na dawo Ka tabbatar kaida jami'anka kun samo wani abu gameda su,domin banason wanann aikin yabar Military ko kaɗan,Civil security bazasu iyah da wannan abinba sam,zan nemi yin magana da president akan lamarin"
Yana gama faɗin hakan ya dashi ya fitah. Babban mutum ne yafara manyanta,amma kuma kasancewar a ƙuruciya ba'a zauna ba,jikin yana nan kaman bana dattijai ba,duk da daman bawai tsoho bane ba.
Combo ɗin motocine a ƙofar office ɗinnsa,yana fitowa ta tsakiyan ya shiga,suka ja zuwa gida.
Babu nisa gidannsa dan haka da wuri ya isa katafaren  gidannsa wanda yake da kwarjininsa kaman an jefoshi.

Motocinsa suna shiga gidan na Mrs Aliyu Hamma wato Hajiyah Maryam kuma suna shirin zasu fita daga gidan.
Har an tada motar da take cikin suka tsaya,fitowa tayi daga cikin motar tana kallon A.M aliyu ta cikin farin glass ɗin idonta.
Farace tass ƙirar fulani,sannan kuma tanada kamammen jiki,duk da ta ɗan ga jiyah amma jikinta sam bai nuna ba,kana kallonta batayi kama da iyayen da za'a ƙirasu masu sanyin rai ba,dan ko a gidan kowa yasani hatta barrak ɗin,daka shiga shirgin Hajiya Maryam kwanta kaje da kanka ka faɗa hallaka,domin bata barin kota kwana,kowa abinda taga dama take fesa masa,ciki kuwa har shi kansa mijinnata bai isa ba.
Ƴaƴan ta huɗune a gidan Saleem Da Sameer ƴan biyune,saikuma Maimuna da fatima itace ƴar auta. Duk duniya su kaɗai take gani da gashi a rayuwarta,duk da cewar basune kaɗai ƴaƴan A.M Aliyu Hamma ba,yanada wani ɗan Wato Ahmad Aliyu Hamma,shine babban dansa kuma mahaifiyarsa ta rasu. Saidai shima ya rasu sanadiyyar hatsarin mota,shekara biyar dasuka wuce. Wasu sunce a garin ba hatsari bane haɗashi aka akayi,saidai babu wanda ya isa ya ɗago zancen har a yanzu....
Sameer soja ne kaman Ahmad sanda yakesa rai,saidai shi ba'a bangaren bincike yake aiki ba.
Saleem kuma Medical lab scientist ne,yanada sha'awar nazari akan abinda ya shafi bincike,musamman abinda ya haɗa da yanayin rayuwar mutane.
Sai kuma Maimuna lawyer ce,saidai ita ba wani cikyakykyiyar lafiya ce da ita ba,tayi aure amma batayi sa'ar miji ba,Allah ya haɗata da shashasha,gata da sanyin hali itada Saleem. Ita kuma fatima wacce ake ƙira da fatee,karatu takeyi,sannan ita halinsu ɗaya da sameer wajen zafin rai,sune suka iyo mahaifiyar tasu wato hajiya Maryam........
Ƙwasƙwas take tafiyah harta iso kusada shi.
"Abban fatee yana ganka ka dawo da wuri haka?"
Shuru yayi baice komai,dan indai abune daya shafi tsaronsa bayayin maganar da itah,saboda shi kansa yasan bai yadda da itah ba sam.Kawar da tambayartata yayi ta hanyar cewa.
"Ina zaki bayan Mammamah batada lafiyah"
"Taro zanje na manyan matan ƙasa,yanada muhimmanci,kar kace komai dan bazan fasa tafiyah ba ma,sai kace kana magana da ƙaramar yarinya,zazzabi ne fah zata iyah kulada kanta ai"
Tana gama faɗin hakan bata tsaya tambayar mai ya dawo dashi ba ta yi gaba.
Jijjiga kai yayi ya ƙarisa cikin gidan,shima dama yasan dole sai tayi maganar banza ga mahaifiyar tasa,yarasa meyasa taƙi jinin Mahaifiyarsa,bayan ita kuma kullum cikin son Maryam ɗin take,duk sanda yayi yunƙurin sakinta itace take hanashi har aka kawo wannan lokacin,tun abin yana damunsa har ya daina ma.
Ba sashensa ya nufah ba,sashen mahaifiyar tasa ya nufah,daɗin yanada uwa kenan,tunda mata bazatayi aikinta ba....

Sorry amin afuwa kunji labari yayi tsallen kurege ko?? Karku damu zan haɗashi waje ɗaya,kuma da sannu zaku gane......

Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan
09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan
09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

SANADIN CACAWhere stories live. Discover now