...23...

705 15 3
                                    

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[23]

[Sumaimah a mahangar gani]

Shinkafa da miyah nayi niyyar yi,saboda nayi amfani da naman da goje yasaka aka kawo,tun safe yaron da Tunga ya hadani dashi yazo yayimin siyayyar duk abinda nakeso..
Sai wajen shaɗaya kafin na ɗora abincin,wanke wankenmu dan kaɗan ne,tun safe na wanke komai na kwanukan da muka bata,shara kuwa in na share ƙofar inna shikenan saita goje.
Bayan na gama shuru nayi ina kallon abincin dana zuba a cikin kulolin,na tafi tunani naji muryar inna a sama na.
"Wani abune ya faru naga kinyi shuru uhm"
Ashe tana kallon tun ɗazu,so nake da ya fita daga ƙofar tasa saina kai abincin,amma yaƙi fita gashi azahar tana shirin,banaso najene ya gwaleni ya koroni,korar dayayimin ranar danazo gidan har yanzu bata bar cikin kaina ba ina tunowa.
"Inna uhm kina ganin zai yarda yaci kuwa? Baice mu dinga yi dashi ba abincin?"
Dariyar dattawa tayi min kafin tace.
"Karki damu Sumaimah Inshaallah zai karba,kuma abincin yayi daɗi sosai da sosai,Ba kowane zai kauda kai baiciba,musamman ma kinsan maza da son abinci kuwa?? Idan kinga yafara ci saikiyi masa maganar komawarki islamiyya da kika fadamin kinji,amma fah kada ki fada sai kinga yana cikin yanayi mai kyau,kin gane koh?"
Ɗaga kai nayi amma kuma saina tuna naga jiya tace zata fadamasa nakoma islamiyyar  meyasa ta sanja ra'ayi.
"Amma inna kince fah zakiyi masa maganar karatunnawa?"
"Uhm uhm da nayi niyyar yimasa maganar,amma inaga kiyi masa maganar da kanki zaifi,ta hakane zaku samu fahimta da kusanci a tsakaninku,sannan in kina tambayarsa da kanki hakan zaisaka ya ƙara gane cewa ke ɗin haƙƙinsa ce kuma kina ƙarƙashinsa"
Maganar da tayin ya gamsar dani sosai,yanda take yimin wasu abubuwan har mantawa nake da itah surukata ce.
Ɗaukar abincin nayi akan tire cikin sanyin jiki na nufi hanyar ƙofar tasa. Tun dawowar innan bamu tab'a yin abinci dashi ba,saboda baya zama a gidan sam,ko mai yakeyi oho. Jiyane dawowar sa yasaka yaro yashigo mana da nama kaman ranar farko.
Na buɗe baki zanyi sallama sai kuma naji yana wata magana...
.......Me kake nufi ne wai,jiya fah na dawo yace na fasa fita aikin,kuma yanzu kace wai na sake dawowa,hakan bazai yiyu ba sam.akwai wani aikin danake so nayi,ba iya waccanne aikina ba. Idan yin fashin ko satar daɗine shiya je yayi mana,in kuɗinkune saina dawo muku da kayanku yana nan ban taba ba.......
Sata fashi..nashiga uku dama fashi yake zuwa idan yayi wannan tafiyar...yaushe yafara fashi?.
"Me kikeyi a tsaye a nan,ko bayan rashin kunyar harda lab'e kika fara yimin"
Saurin tura ƙyauren nayi na shiga ɗakin ina rarraba ido.
A tsakiyar ɗakin na tsugunna tareda ajiye tiren kayan abincin. Da kallo ya bini yana zaune daga shi sai singlet ruwan toka,da kuma baƙin gajeren wando. Ta gefen idona na kulada shigar da take jikinsa,hakanne yasa naƙi ɗaga ido na,fatar bakina rawa take amma kuma na kasa cewa komai.
Matsowa yayi ya dawo bakin katifar yana ƙareni da kallo.
"Ɗago fuskarki ki kalleni"
Bin umarninsa nayi ta hanyar ɗago idanuwannawa,akan ginannen ƙirjinsa na ajiye idanuwana,ban ƙarisa izuwa fuskarsa ba,magana naji yafarayi,saidai ba irin muryar danaji yana yiwa mutumin dayake waya dashi bace.
"Me kikaji ina faɗa a waya?"
"Uhm....uhm zancen fashi kuke da sata"
"Dakyau dama na tsani ayimin ƙarya,to kada ki kuskura inna taji wannan zancen"
"Tohh bazata jiba"
Ɗaga kai yayi alamar ya gamsu da abinda nace. Shuru ne ya gibta,ganin baice komai ba yasa na fara bude kular abincin,a raina ina cewa karka hanani karka ce ka ƙoshi.
Ohh Allah ya amshi Addu'a ta kuwa harna gama zubawa baice komai ba,amma inajin idanuwansa a kaina. Cokali na saka a kan plate ɗin na miƙa masa. Kar'ba yayi ba musu yafara garwaya gabansa yana kaiwa baki.
Ruwa na zuba masa a kofin jug ɗin danazo dashi na sake mika masa gabansa,hannunsa ya kawo zai ɗauka nikuma ban zare hannuna,hannunmu ne ya haɗu dana juna,da sauri na zare nawa ina sake sunkuyar dakai.
"Akwai magana a bakinki meyasa bazaki furta ba,kina bani mamaki,har yanzu na kasa gane kanki,lokacin da banyimiki komai ba kina tsorona,da nayi niyyar yimiki kuma sai kika maida martani"
"Uhm kayi haƙuri a loka......"
"Ahah bance saikin bani dalilinki nayin hakan ba,me yake tafe dake yanzun?"
Dama yana magana haka ta lumana irinna sauran mutane? Tun lokacin dana ke ganinsa a gari kafin zanen ƙaddarata ya ɗinke da nasa ,nayi zaton idan an zo kusadashi kashe mutane yake. Tsaida tunanin danake nayi tareda sanar masa buƙata tah.
"Uhm dama inason komawa makarantar islamiyyah ne,amma ta matan aure"
"Tsawon sanda nake cin karo dake a lokacin baya da kayan makaranta nake ganinki kafin kifara talle,har yanzu bakiyi ya isheki ba?"
Da yayi maganar bansan lokacin dana ɗaga ido na kalleshi ba,dama yasanni yana kallona.
Kaman yagane abinda nake saƙawa a raina,murmushi yayi amma ba mai tsayi ba yace.
"Ohh a zatonki bana kulada mutane ne idan suka ga zamu haɗa hanya suka juya da gudu,ina kulada ke duk sanda muka haɗa ido komawa kike da gudu kibi da wata hanyar,abin yana bani dariya da kuma nishaɗi idan naga mutane suna gudu"
"Babu ɗaɗi da kuma nishaɗi ace kana ɗan adam ƴan adam ƴan uwanka suna gudunka,alamar maƙiyine a gujeshi,kana kuma alamar masoyine a kusanceshi a duk inda ya gifta"
Wuuff nasaka hannuna na rufe bakina ina jijjiga kai,Sumaimah kinga ta kanki meya kaiki fadamasa waɗannan kalaman.
Runtse idona nayi,na ɗanyi wani lokaci,jin bai dakamin tsawa ba ko mari yasa na buɗe idona,murmushi naga yanayimin....wannan bawan Allah menene yashiga jikinsa.
"Yanzu ma kin sake bani mamaki,kece mutum ta farko data fara faɗamin irin waɗannan kalaman bayan inna,zuciyata ta kasu kashi biyu a halin yanzu.....ki tattare kayannan maza ki fitah,batun makarantar kuma zan duba nagani"
Tashi nayi da hanzarina ba bata lokaci na tattare kayan dana shigo na dasu zan fitah,har nazo bakin ƙofa naji muryarsa,inba nasan muryarsa ba bazan ce bane.
"Abincinki yayi daɗi,nagode"
Ehh juyawa nayi duk da yacemin na tafin,kallonsa nayi ya saka hannayensa akan kunnuwansa,idanuwansa kuma a runtse kaman yana cikin ciwo,meyasa lokaci ɗaya yakoma haka saikace bashi ba?
Nidai fitah nayi daga ɗakin zuciyata cikeda mamakin ganin sabbin halayen gojen.

SANADIN CACAحيث تعيش القصص. اكتشف الآن