...11...

483 14 0
                                    

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[12]


Hamma yayi kana yasake kishingiɗewa a kan gadon ammin,kallonsa tayi da mamaki kana tace.
"Yau bakada wajen zuwane tun ɗazu kake kwance anan?"
"Uhm to kusan,in ma inada shi fah? Inna fita kuce bana zama a gidan,yau kuma na zauna kinamin kora da hali"
"Ohh baban ubaidu yaushe nayi maka kora da hali dan......."
Asiyah ce ta bankaɗo labulen ɗakin ta shigo kanta tsaye babu alamar dakatawa,duk da kuwa taga takalmin babannasu a ƙofar ɗakin.
(Abinda akasari yake faruwa a gidaje kenan,musamman gida irinnamu na hausawa,kaɗan suke kiyaye wannan. Sai kaga yaro ya shigo ɗaki da gudu kuma iyayensa suna ciki,shin kozai iya arba da abinda bai kamata ya gani ba duk bai dameshi ba sam. Allah yasa mu gyara.)
Fasa cigaba da maganar tayi tana kallon Asiyah.
"Kekuma menene kika shigo kan mutane kaman doki?"
"Uhm wai ana sallama da baba a waje"
"Waye ko halliru mai gerone,dan munyi dashi dama zaizo ya karbi guntun kuɗinsa"
"Ahah bashi bane,wannan wani bafulatani ne da wata yarinya"
Hantar cikin uwaisu ce takaɗa dayaji ance yarinyah,yau kwana huɗu kenan da faruwar lamarin tskaninsa da jauro,tun yana tsammanin ganinsa washagarin ranar har ya daina,kwatsam sai gashi.
"Baban ubaidu ƙalau kake kuwa,yanaga kayi wani fayau kaman wanda yaga fatalwa?"
"Ahah bakomai barinaje naji damai yazo"
Daga haka bai sake cewa komai ba ya fita daga ɗakin.
Cikin sanɗa kaman wanda kura ke jiransa a zauren yake tafiyah har ya isa ƙofar gidan.
Da jauro suka haɗa ido,saikuma wata yarinya a bayansa butu butu da ita kaman ƴar tashe,wani wandone a jikinta mai kamada ƙanzo,sai wata yagyagygyiyar riga,kanta kuwa ba kitso ba,wani irin gashine kaman sumar mahaukaci.
Ƙiru idonsa ya sauƙa akan ta,aikuwa lokaci guda ta sauya kallon idonta,kamar girarta zata haɗe,wani gurnani take fitarwa daga maƙogaronta kamar kare,ga haƙoranta kamar na kifi saboda tsini. Yanda ubannata yafaɗa kuwa hancin saikace na 'baunar,dan a manne yaka a tsakiyar kumatunta.
Wani jirrr uwaisu yaji daya daɗe yana kallonta,ransa kam baya hango masa alkhairi a jikin wannan halittar.
"Kai hauka kakeyi,caca mukayi zaka bani ƴar ka ba wannan aljanar ba,dan haka tun dare bayyi maka ba ka tattara ta ku koma inda kuka fito"
Har uwaisu ya juyah zai koma gida jauro ya biyoshi cikin gidan. A filin da matan gidan suke taruwa suka tsaya,da anata hayaniya kowa sai yayi shuru yana kallon uwaisu da kuma ɗab fulani wanda ya biyoshi,ga kuma yarinya a gefensu.
"Dakata uwaisu,mun riga munyi yarjejeniya dakai,kanason ɗiyata in kaci cacah,nikuma zaka bani gona idan naci. Yanzu kuma kace bakashon ɗiyah,wannan zancen bazai yiyu ba. Ga ɗiya nan na kawo maka,koka so kokuma ka so anan zata zauna. Tacemin tanaso ta zauna yanzu koni ban isa fiddata cikin gidanna ba"
Sakin baki uwaisu yayi yana kallon jauro cikeda takaici.
"Ohh a zatonka wannan abun zan aure kenan"
"Niban ce maka ka aureta ba,amma yanzu a wajenka zata zauna,itama dukiyarka ce daka ciyo a cacah. Sannan saida zan faɗamaka tanada matsala na aljanu ,ba rayu a cikin mutane ba,amma kace bakason jin komai daga bakina. Yanzu kuma nakawo maka ɗiya kace ba haka ba?".
Faɗane ya kaure tsakanin jauro,yana sai ya tafi uwaisu yace saidai ya tafi da ƴar daya kawo.
Gurnani sukaji a bayansu irin wanda uwaisu yaji Deejah tayi ɗazu a waje.
Kowa idonsa kanta ya koma,in ka ɗauke uwaisu da jauro sauran mutanen gidan basu san ma itace tayi ba,saida suka ga tana buɗe baki,idonta akan kazar inna rammah,wacce aka kawo mata a haihuwar danta na ƙarshe,maimakon ta yanka taci saita barta tana yimata ƴaƴa.
Wata super Deejah tayi akan kazar ta tumurmusheta a ƙasa,kaza tana ihu tana komai haka ta saka bakinta ta tusge kanta,jini faca ya 'bata gaban rigarta.
Jefah kazar tayi a ƙasa tana kallon tana dariyah,wuta ce buuu ta fara babbake kazar. Bayan ta gama babbakewa daukarta tayi ta murmushe gashin jikin,sai turiri take amma ko zafi bataji. Yagar cinyar kazar tayi ta zuge a bakinta,suna nan tsaye suna kallonta har ta gaigaye jikin kazar ta jefar da kayan cikin.
A lokaci ƙalilan Deejah tagama da kazar inna ramman,kowa a gidan ya sandare a tsaye yana kallonta,iya jauro ne kawai abin bai dameshi ba.
"Ke bani ruwa"
Tafaɗa tana kallon inna ramman,dan dama itace ta kusada ita a zaune. Bata yi motsi ba kana batace komai ba,dan har yanzu abinda ya faru baigama jeruwa a cikin kanta ba.
"Nace ki bani ruwa na sha,ko kema saina babbakeki na cinye kai,wannan ƙaramin naman ba wani ƙoshi nayi ba dama,baba ne yace zai kaini gidan sabon babana shiyasa ban fita farauta ba"
Maganar cikin msifah take yinta kaman tana ganin hanjin mutum.
Da rawar jiki inna ramma ta tashi ta nufi ransa ɗebo mata ruwan,baƙin ciki biyu,an kashe mata kazarta da ko korarta mutum yayi sai taji haushi,ga kuma ƴar ƙaramar ifiritiyar yarinya tana aikanta.
Fizge ruwan Deejah tayi daga hannun inna rammah bayan ta kawo mata,ƙwatt ƙwat take zubawa a cikin harta shanye shi.
Miƙa tayi kafin ta kuma sake kallon inna ramman.
"To kaini ɗakinki zanyi bacci,kece mamata daga yau,ina son mutum mungu naga wani baƙin ɗauri yana bin ruhinki,dan haka ke munguwa ce"
Zaro ido inna rammah tayi,wai anya kuwa ba mafarki take ba,wannan wacce irin aljanace,duk biye biyenta bata taba tunanin zata gamu da aljani ba a ido da ido sai yanzu.
"Bazaki kaini ɗakinnaki bane da kanki,zatonki inna bi baƙin zarenki bazan gano inda kike kwana bane,na miki mutuncine danace ki kaini dakanki"
Sake razana inna rammah tayi da tsawar da Deejah ta daka mata,wuce gaba tayi tana binta har suka je shige ƙofar tasu.
Kowa sauƙe ajiyar zuciya yayi,yayinda kallo kuma yakoma kan jauro,wanda shine silar kawo musu wannan masifah. Ammi ce tayi ƙarfin halin yin magana ganin kowa yarasa bakin cewa uffan.
"Baban ubaidu mai yake faruwa ne,wannan bafulatanin fah,sannan itama waccar aljanar wacece"
Shuru uwaisu yayi yana kallon ƙasa,ta ina zai fara kenan?
Ganin bashida tacewa yasa jauro gyara murya ya jiye musu labarin abinda ya faru,tundaga A har Z,sannan kuma ya ƙara da cewa.
"Da yayi zaton wayo yayi min,ni daka ganni nan nasan caca fiyeda yanda kake zato,da nayi niyyar cinyeka na ɗau gonarka,amma daka naji ɗiyata kakeso da aure saina gano bawai cacar ce a ranka ba,so kake ka cuceni. Nikuwa saina barka kayi nasara saboda na rabu da Deejah. Tunda aka haifeta bamu taba hutawa ba,saboda tsabar ta lokaci guda na tashi naga innarta ta gudu,matar dana auro ma daga baya tace zata zauna,ganin abin yafi ƙarfinta itama ta gudu. Ko yaushe cikin gina bukka muke,bama bacci sabo kar takasa mana wutah,nasha guduwa na barta idan ta shiga daji,amma dayake aljanunta ne suke taimaka mata take tsiya saidai kawai na ganta ta biyoni. To yanzu tunda tace zata zauna a wajenka watan hutawa ta yakama,zanje na ɗau matata da ƴaƴana mucigaba da zama"
Yana gama faɗar haka yafita daga gidan hankalinsa kwance.
Cikeda takaici ammi ta kalli uwaisu bayan jauro ya tafi.
"Yanzu wagari ya waya baban ubaidu,munyi munyi dakai ka daina wannan cacar,manyan unguwa sun yi maka magana,amma kaƙi ji sam. Wato da ƴar kyakykyawace ɗiyar fulani saidai muji zaka aure ya koh,a sanadiyyar cacar nan ka ɗauki ƴar ka ka bawa wancan shashan,kaikuma da a tunaninka saika auro wacce ranka yakeso? Saboda kai kanaso kaga daidai?"
Haɗiye wani abin baƙinciki tayi bayan tayi masa kallon takaici tabar wajen.

Cikeda borin kore kunya ya kaɗa rigar sa yabar gidan,amma kana ganin fuskarsa kam kasan abin ya dameshi.
(Hmm baka ga komai bama)
Ammi tana shiga ƙofar tasu taji ihun inna rammah a ɗaki.
Ƙarisawa ɗakinnata tayi da sauri dan ganin mai yafaru.
Leƙawa tayi ta samu aljanar da aka ƙira da Deejah ta kafa haƙoranta a cinyar inna ramm,irin wanda tayiwa kazarta ɗazu.
Ammi ce tashiga ɗakin ta janye ta daga jikinta,jini sai zuba yake a wajen.
"Wayyo na shiga uku,cinyeni zatayi nima kaman yanda ta cinye kazata,wlh bazan zauna ba uwaisu ya kawo abinda zai halaka ni ya halaka ƴaƴana"
A bangaren Deejah kuwa ammi tana banbareta daga jikin rammah ta koma kan gadonnata tasake kwanciyah luff kaman ba ita tayi ba.
"Rammah mai kika mata ta cije ki?"
"Ammi ganemin wannan masifar,tace a ɗakina zata zauna na kawota,wai kawai dan taga ɗana akan gado saita jefoshi.Aradu badan na cafkeshi ba a ƙasa zai faɗi,haushin hakanne yasa na mareta,aikuwa tafara wannan gurnanin,wai ba'a dukanta,kannaceme naji ta maƙare a jikina tana yakushi na. Muna haka zanina ya kunce,tana ganin cinyata ta gasa min cizo.Wani zafine ya jiyarceni shiyasa na zuba ihu. Dan Allah Ammi ki taimakeni na fitar da ita a ɗakina"
Deejah tana jin abinda rammah ta faɗa ta ɗago idonta.
"Idan kukayi yunƙurin ta'bani saina bunkawa ɗakinann wuta na babbakeshi,ke kuma idan kika sake shiga in muna fada to ɗakinki zan koma da zama. Zanyi bacci kafin na tashi ku sama min abinci,idan ba haka ba kaza ta gaba ce abincin na,sannan duk ɗan daya shigo ina bacci saina karya ƙafarsa".
Tana gama faɗin haka ta koma ta kwanta.
"Kinji koh ammi dan Allah........"
"Ahah dakata bakyajin abinda tacene,ko bakiga yanda tayiwa kazarki ba kai,bazaki ɗau darasi daga haka ba. Ni kinga tafiya ta ba dani ba.
Takaicine ya ishi rammah,hakanne yasa ta fito filin ƙofar tasu tana safa da marwa,burinta kawai uwaisu ya shigo gidan ta direshi da masifah,a jima ta leƙa ɗakinnata,duk sanda ta hango Deejah a kwance tana birgima akan gadonta sai wani takaici ya jiyarce ta.
Tun tana tsammanin jiran uwaisu shuru shuru har yamma tayi,bata manta ba kuwa yana shigowa tasha gabansa.
"Allah ya shigo dakai,maza kasan yadda zakayi ka fitarmin da waccar halittar daga ɗakina,dan wallahi bazan zauna da itaba,saidai na bar gidannan akan haka"
"To yanzu ykk so nayimiki kenan,shigowata kenan tun fitata,baki bani abinci ba kuma kece da abinci"
"Abinci zancen abinci ma kake kenan,to ni tunda ka kawo wannan masifar ko ruwa ban saka a bakina ba,kanace wasa nake koh,koka fita da ita kokuma nayi gidanmu. Kalli inda ta cijeni fah har yanzu jini bai tsaya ba"
Masifa rammah take kan gari ya gari,akan koya fitarda Deejah a ɗakinta kokuma ta tafi gidansu.
Ganin abinnata bana sanyi ne nan kusa ba yasa uwaisu ƙirna mazan gidan akan su fito da Deejah a cikin ɗakin.
Ubaidu aka ƙira yaran gidan maza kaman su biyar akan su fito da itah.
"Haba baba kace yarinya ce ƴar shekara sha biyu,miye kuma sai an ƙiramu kusan mu biyar,saikace wani gardi"
Ubaidu yafaɗa da sanda a hannunsa yana dariya rainin hankali"
"Uhm uhm ubaidu kudayyi a hankali,bakuga yanda tayiwa kazar rammah bane ɗazu,nan da nan fah ta cinyeta a gabanmu,kuma itama kanta ramman data cijeta saida fatar da ɗaye"
Ammi tafaɗa cikeda tsoro.
Duk cikin mazan babu wanda ya yarda  da zancen ammi,amma dai basu ajiye sandan ba suka shiga dashi.
Deejah tana ganin shigowar mazan da sanda ɗakin ta tashi ta zauna.
Kallonsu take kafin idonta ya sauƙa kan rammah da uwaisu waɗanda suka shigo daga baya.
"Mazakuyimin da waɗannan sandunan,ke kika turo su ko dan kawai zan zauna a ɗakinki? Kaikuma dan kawai nace na yarda ka zama ubana na biyu shine zaka saka a dakeni"
Cikeda mamaki bawai na tsoro ba take kallon su dukka,baƙincikine yasake shaƙar rammah,musamman data gano inda dejah ta kwanta,tajiƙe wajen jaraff da fitsari,hmm dama yaushe za'a raba wannan da fitsari,da batayi kashi bama.

Yakuke ganin shin Deejah zata fita daga ɗakin ramma kuwa????

Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan
09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan
09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

SANADIN CACAWhere stories live. Discover now