...24...

580 9 2
                                    

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[24]


[Sumaimah a mahangar gani]

Cikeda murna da tsalle na fada kan inna,tana tsugunne tana alwalar azahar.
"Ahah ahah Sumaimah lafiya mai ya faru?"
"Inna makaranta,inna zan koma makaranta,inna a Albayan ya sakani wai,zan iya cigaba harda na boko nah inna"
"Mashaallah na tayaki murna Allah yasa kiyi ilimi mai yawa mai amfani,yanzu saki nutsu ki rubuta komai"
"Yanzu ma kuwa zan cika ai,wayyo daɗi"
Ɗakin innan na faɗa ina tsalle,a yau goje yayimin abinda ko a mafarki bana kawoshi,saboda nasan bazan samu ba,sai gashina samu,zan koma makaranta,hakanma mai kyau.
Form din nabi daki daki cikin nutsuwa na cikasu,na islamiyyah ne da kuma na boko,itah a SS 2 nasaka su sakani,duk da nasan kasada ce amma inason yin kasadar,tunda ina ji a jikina zan dage nayi karatun bilhakki,islamiyyah kuwa dama nayi sauƙa dan haka ajin tafsir da sauran litattafai na hukunce hukunce na saka. Ranar ko baccin kirki da kyar ya daukeni,nayita jiran goje nayi masa godiyah,amma har nayi bacci bai dawo ba.
Washagari da safe da wuri na tashi na gama komai,indomie na dafa sai kwai akai,saboda karma nayi mai nauyi ya bata min lokaci,a tsatstsaye naci nada yawa ba nayi hnayar ɗakin gojen,inna dai banda bina da kallo babu abinda take,in abin yayi yawa tace uhmm kokuma ta jijjiga kai.
Da sallama ƙatuwa na isa bakin ɗakinnasa,hannuna riƙeda plate nakifah wani akai.
Jin bai amsa ba yasa najuya zan koma,motsin tafiyarsa naji,ina juyowa muka hada ido dashi,fuskarsa ɗauke da alamar bacci.
Kinshiga uku Sumaimah kaddai tashinsa nayi a bacci kai..
Inda inda nafara ina neman mai zan kama na faɗa,inda sabo na saba ma.
"Uhm uhm dama....kodayake barina koma tun....."
"Shigo"
Haka kawai yacemin tareda komawa ciki,binsa nayi a baya kaina a ƙasa na ajiye plate ɗin .
Kambu ashe ba riga a jikinsa ma,sai a sannan yake sakawa,kai ya jikinsa fari amma fuskarsa baƙa....koda yake da wannan uban gashin fuskar wazai ɗorar kamarsa dama,dan ma narage tsoransa yanzu,amma nasan sauran mutane kam wasu yanzu suka fara.
Nikaɗai dai nake zantukana har yagama yazo ya zauna,gaisheshi nayi kaman ko yaushe ya amsa a taƙaice.
"Zan tafi makarantar yanzu?"
"Saikin dawo,duba zif ɗin jakata ki ɗauki ɗari biyar"
To nace tareda da ɗauka kaman yanda buƙata na fita daga gidan cikeda zumuɗi.
Office ɗin shugabar makarantar naje muka gama magana dashi,kaman yanda na nema sun barni a SS 2 ɗin,wanda nasan dan suna tsoron gojene,amma sun gargaɗeni na dage. Wata malama ce ta gwadani akan zuwa yamma za'a kawomin kayan makarantar da kuma litattafai da duk abinda nake buƙata. Nidai da toh nake binsu har suka gama yimin bayani. Dukka da safene zuwa ɗaya na rana,sai islamiyyah Asabar da lahadi shima daga safe zuwa sha biyu.
Bayan mungama nayi zaton gida zan dawo,amma sai suka cemin zan iya shiga aji kawai.
Hakan yasa kawai na nufi aji,Allah ya taimakeni ma a farkon shekara suke.
Bayan an tashi tafiyah nake ina jan ƙafah,nagaji tulus abinka da wacce ta daɗe batayi ba. Duk zumuɗinnawa yakoma ciki,nafara farfaɗowa daga mafarkina yanzu zan tsunduma zahirin karatu tunda na samu dama.
Lokacin dana isa gida an daɗe dayin azahar,na samu inna tayi abinci,gaji ma ta miƙo mana awara,dan tunda taga muna abinci intayi ko bazamuci ba saita sakomana,saboda muma mu saka mata,har wai hirar dare take zuwa ayi ta zance,ni dariya ma take bani,ko kunya ace mutum bayaji....kai Allah ya kyauta.

Da yamma kuwa kaman yanda shugaban makarantar yafaɗa,ya aikomin kayana uniform da kuma jaka ɗauke da litattafai,na rubutu da kuma na karatu,harda ƙur'ani izu sittin aciki..
Nikamma dan daɗi narasa bakin magana,ko ƴaƴan gata albarka,babu abinda yarage sai karatu kawai..

         __***__

"Deejah ki ɗauki ruwannan kiyi wanka kizo ki tafi makaranta,kinsan fah abinda yayanku ya faɗa"
"Bazan jeba,nace bazanje ɗin ba,ki faɗamasa idan yazo yaga banje ba ya kasheni nace ya kasheni,littafinma......"
Bata ƙarisa maganar ba ta rabashi gidan biyu fiyattt.
Kallonta ammi take da takaici,komai yasa Musbahu yakeson bata kuɗinsa akan wannan halittar oho,a zatonsa wai hankali zatayi irin na sauran mutane idan ya kaita makaranta?
"Deejah kika yaga littafin makarantar?"
"Ehh ɗin na yaga kuma......."
Bata ƙarisa maganar ba sukayi ido huɗu da Musbahu,wanda yake tsaye a bakin shiga ƙofar tasu,ya saƙala hannunsa a kirjinsa yana kallonta,fuskarsa cikeda bacin rai.
"Ya mukayi dake,me kika cemin jiyah"
"Ehh ni cewa nace zanje makarantar inna je kuma zanyi karatu,idan na ƙiyi a dakani"
"To me yasa daga zuwanki ɗaya jiya kikace bazaki sake zuwa,wato irin duk abinda zanyi nayi harda yaga littafin koh,ana kije kiyi wanka kina cewa bazakiyi ba"
"Ahah ni bance baxanyi wanka ba,sannann kuma littafin bani na yagaba fatalwar tunkiyar rammah ce"
"Ohh bayan kin soke tunkiyar ma kaman wata raƙuma bai isheki ba saikin bita kinyi mata sharri,ki dai faɗi gaskiya abinda yahanaki komawa makarantar,kin fasawa malami goshi ai dole kice bazaki jeba"
"Ke rammah dagaske ta rotse kan malami,a ina kikaji?"
Ammi ta tambaya tana riƙe haba.
Wata harara Deejah ta watsawa rammah tareda cewa.
"Nasan wadda ta faɗamiki,wato duk da gargaɗin danayi mata bataji ba koh,hmmmm"
Bulala Musbahu ya zara zaiyi kan Deejah,amma kururuwar da uwaisu yakeyi ta tsayar dashi.
Daga ɗakinsa yafito yana kururuwa,banda ambaton kuɗinsa babu abinda yakeyi.
Kowa tsayawa yayi yana kallonsa a wajen.
"Kuɗina wanene ya ɗebemin kuɗina,wayyo shikenan kun lahantani wane shegenne ya bankaɗemin ajiya yamin sata waye?"
Haɗa ido sukayi da Deejah wacce take tsaye a bakin banɗaki,saboda gudun da tayi daga wajen Musbahu.
Gwaliyo tayiwa uwaisu tareda kashe ido,aikuwa nan ya gane mai take nufi.
"Zo shegiyar yarinya zo nan, tunda kika kasheni ai sai ki bar gidannan,ki faɗamin inda kika kaimin kuɗina"
Kowa yanxu kallo wajen Deejah ya koma,wacce take kallon mutanen wajen idonta a tsatstsaye kaman nono maza..
"Niba kuɗi na ɗauka ba takardu na ɗauka,jiya fah aka tambayeka a gida za'ayi abinci kace bakada kuɗi,to ni taya zanga kuɗi a ɗakinka bayan kace bakada kuɗi,takardu na ɗauka,kuma nayi makamashi dasu"
Tafaɗa hankalinta kwance kaman batasan mai ta aikata ba,bayan kuma tana sane rashin mutuncine kawai. Dan yanzu ta daina wannan gurnanin,tsiya take shukawa a gidan cikin hankalinta.
Kama ƙirjin uwaisu yayi numfashinsa yana yin sama sama,kafin Musbahu ya tafi da sauri ya taroshi har yakai ƙasa..
Ihu da kururuwa mutane gidan suka saka,aka nufi asibiti dashi.
Banda Deejah waccce ta shiga wanka zata tafi makarantar da tace bazata ba.
Ammi ce ta kalleta wacce tazo ɗaukar mayafi zasu tafi asibitin.
"Amma wannan yarinyar bakya cikin mutane inaga,yanzu kiga abinda kika aikata masa amma bai dameki ba?."
"Ahh to ubana ne dazan damu,kuke wani kukan munafurci naga kuma ba damuwar kukayi dashi ba,shima kuma ba damuwa daku yayi ba,yanada kuɗin jiya ya kawo ayi tuwo yace wani bashida kuɗi,kuma yanzu yafito yana faɗuwa wai an ɗauke masa kuɗi,harda za'aji haushina ma ai na banza ne,kuɗi suna amsa sunansu kuɗi idan za'a kashe ,inku aka ajiyesu da bunu ne.
Nina tafi makaranta naga yanda zamu ƙare da wancan shima wani uwaisun hmmm,aishima in bai kiyayeni ba saina figewa wannan ƴar tasa mai suffar agwagi ƙafafu"
Surutun take tana tafiyha harta bar gidan,ita kuma ammi ta tari acaba zuwa asibitin.
Lokacin da ammi ta isa asibitin har an saka masa ruwa yana kwance,yayi shuru da alama bacci yakeyi.
Musbahu ne a jingine a jikin bangon ɗakin,sai rammah a gefensa a zaune,magana yafarayi kaman zautacce..
"Kuɗina kuɗina dana tara,da ƙonamin kuɗina mai kuma ya sauramin tunda na kuɗina"
"Baban ubadu dan Allah kabar zancennan,wai yau kafara rasa kuɗinka ne,naga kusan ko yaushe kaje caca sai ka rasa kuɗinnaka,har ƴar ka ka rasa abin bai dameka ba,amma yanzu akan kuɗi kana ta tadawa mutane hankali"
Ammi ce tafaɗa cikeda takaici,dan itama kaman Deejah abinda kuma yafara bata haushi..
"Dallah rufemin baki,kinsan kuwa kuɗinnan na menene,duk sanda nayi caca tayi kyau zuwa nake na tara su,hatta kuɗin gonata ma ta hayi tana siyar suna ciki,kuɗinnan su nake gani nakejin daɗi,saboda yanda sukeda muhimmanci a wajena,kuɗin sadakin Sumaimah ma suna ciki,harda kuɗaɗenku da in ansiyar dabbobi nake cewa sun faɗi......"
"Kambuuuu kace har kuɗin tunkiyata ma data kasa narasa su suna wajenka kenan"
"Ke dallah dana ɗauka ma ai ba cinyewa nayi ba ajiyewa nayi,bare kice nayi miki sata"
Faɗa ne ya kaure tsakanin uwaisu da matannasa,kowa tana faɗin albarkacin bakinsa..
Musbahu bayan ya kallesu na ɗan lokaci ɗauke idonsa yayi yana jijjiga kai,shikamma inaga barin gidannan zayyi yayi nesa dashi kozai hutah,ace kullum sai wani abu ya bullo a gidan. A irin wannan rigimar tasa yake ya ɗakko wata hatsabibiyar yarinya,tausayin halinda take ciki da kuma ganin nauyinta yana kan ubansa shiyasa ya fara kulada lamuranta,domin ko kaɗan bayaso a kuma yarinya wacce zata maimaita rayuwa irin ta Sumaimah a gidan,amma kash ba'a ma farashi ba wata ta bullo. Dan da alama kuɗaɗensu da abubuwansu da uwaisu ya ɗebe ya ajiye na tsawon lokaci sun faɗa,wanda hakan yana shirin mayar da shi suru suru.
Juyar da kansa yayi bakin ƙofah suka haɗa ido da Sumaimah,sanye take da kayan uniform na Albayan,yaushe tashiga makaranta..
Hijabinta ya kusa zuwa ƙasa,da sandal da safa a ƙafarta,sai babbar jakar makarantar data rataya,tayi fari tai kyau kaman ba itah ba..
Shuru kakejin su rammah sunyi,dan suma a tare sukaga Sumaimah tashigo ɗin,babu wanda zai kalleta yace Itace yarinyar da aka kai gidan miji watanni uku da suka wuce.
Tayi kyau haskenta yasake fitowa,tunda ta tafi kowa ya manta da babinta saboda sabon abinda ya kunno musu kai.
A hankali take tafiyah harta isa inda uwaisun yake kwance.
"Baba mai yafaru haka,yanzunnan nadawo daga makaranta na shiga ta gida,anan suke cewa wai kuna asibiti"
Tausayinta ne yakama Musbahu,inaga bazayyi ƙarya ba idan yace kaff cikin ƴaƴan gidan babu wanda yakaita tausayin ubannasu,koda yake ita matsayinsa take bashi cikeda ilimi da kuma sanin darajarsa a wajenta,sabanin sauran yaran gidan da suke masa kallon ba komai ba,irin yanda iyayensu suka nuna musu. Ƙasa yayi dakai yarasa ma mai zai ce mata,da alama kunyarta ne yakamashi.
"Uhm uhm bakomai Sumaimah,yakk a gidan naki dai?"
Ɗan murmushi tayi tareda cewa.
"Bakomai baba muna zaune lafiyah,yanda ake zatonsa ma ashe ba haka yakeba,kalli fah yasakani a makaranta,shine ya kaini makaranta ma yau dazai bi ta wajen,inna ma ta ɗaukeni tamkar ƴar ta"
"Ahh to to abu yayi kyau Allah ya taimaka,kinga tashi maza ki tafi gidanki,inyaso wani lokacin sai kizo gidan koh"
"Amma baba mai yasameka aka kawoka asibiti"
"Ke fah dama kin faye magana,to tunda so koke kiji waccar hatsabibiyar yarijyar ce ta ƙonamin kuɗaɗena,kai wannan ƴa na rasa yanda zanyi da itah,ace ƴaƴan ka basu takura maka ba sai can wata bare?"
Sumaimah bata tambayi wa yake nufi ba,saboda tagano da Deejah yake.kuɗi ta ciro kaman dubu Biyar ta ajiye masa a gabansa.
"Gashi baba toh ka riƙe wannan,yace nayi siyayya ne to banyi ba saboda naji kuna asibiti,sai a siyamaka abinda zai gina jiki. Ammi da inna rammah ni barina wuce toh saina sake zuwa"
Babu kunya tunkafin ta gama bayanin uwaisu yasaka hannun ya fizge kuɗin tareda sakawa a cikin rigarsa,babu zancen siyan wani abu kenan.
Ammi ce kawai tayi mata a sauƙa lafiyah,rammah kam ɗauke kanta ma tayi.Fuskarta ƙarara bata boye baƙincikin da take ciki.
Tashi tayi zata tafi,a nan ta kulada Musbahu wanda yake tsaye,gabaɗaya ma inaga bata ganshi ba ɗazu.
"Lahh yah Musbahu banganka ba,barka da rana ya mai jiki?"
"Yawwa sannu Sumaimah,akwai maganar danake so muyi dake,in lokacin yazo zan sanar dake,wata alfarma nakeso kiyimin kinji?"
"To shikenan yaya karka damu Allah ya kaimu lokacin"
Cikin farinciki da murna tabar asibitin zuwa gidanta,dukkan su kowa sai binta da kallon mamaki yakeyi,kaman ba ita. Wasu sunyi farincikin sauyawarta,wasu kuma babu yabo ba fallasa,yayinda wasu kuma zuciyarsu take tafarfasa.


Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan
09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan
09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

SANADIN CACATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang