__***__

[Sumaimah a mahangar gani]

Yau da wuri na tashi,ba kaman jiyaba da bacci ya ɗaukeni har rana ta fito na makara.
Kai tsaye bayan na gyara ɗakinnamu kamar kullum ƙofar su ammin na nufah.
Koko take zubawa yaran da suka kewaye ta a kofi.
Gaisheta nayi kafin na koma gefe na zauna,saida ta gama dasu tukunna,kafin ta zubamin nawa,jiya girkinta ne da kuma yau,gobe da jibi nasan na inna rammah ne,akwai rowar abinci kenan. Yanzu su biyune a ƙofar Aina'u amaryar baban tayi yaji bata nan,wannan kamma inaga auren tacan tacan,dan ita irin matannane masu shegen son abin hannun miji,idan akwai to da zama,amma idan babu saita ɗebi jaraba tai tayi babu gairah babu dalili. Shikuwa baba samunsa ɗaya idan yayo caca ta gara masa,inkuwa ba haka ba saidai kowa yasan ta kansa,dan kuɗin sana'ar tasa ma ta Aune Aunen kayan abinci dayake a kasuwa kullum su yayah Musbahu ne masu fama da cikaton uwar kuɗin ma ballantana kuma riba.
Hannun nasa na karbi kokon da ammi ta miƙomin,bayan na gama tunanin na yi faɗi ba'a tambayeki ba.
Bayan mun gama gyara wajen nayi kafin na hau kiciniyar ɗora abincin Siyarwa,yau kasuwar garimu ce,dan haka da wuri ake yi kuma yafi na kullum yawa.
Banason wannan ranar ta zagayo,saboda nafi daɗewa a wajen tallen,ga tarin marasa ɗa'a a wajen,saidai kuma ta wani wajen nafi sonta,dan nima inayin wani abun nawa natafi dashi,inna samu riba na saka a asusu.Kuma itama ammi tana sallamata idan na dawo.
Bayan abincin ya kammalu shiryawa nayi nazo ɗauka zuwa kasuwar,shinkafa da miya ce da kuma waje,sai kabeji.
Nida Asiyah muka tafi,dan tunda aurena za'ayi dole itama tafara zuwa dan ta gane kan siyar da abincin.
Kodaɗɗun kayana ne a jikina normal na tsakar gida atampa,sai barin hijabin dana saka,wanda yafara mutuwa ta sama saboda tsufah. Ba wai kayane aka wareni ba'ayimin ba,dama gidaje dayawa masu irin ƙarfinmu daga shekara sai shekara suke ganin ɗinki,hakan ma atampar roba ce. Sauran yara kowa uwarsa na ƙoƙarin ganin tasake masa,wanda kuma ƴan mata ne sun fara hira samarinsu suyi musu. To ni kuwa ciki wannene nakeda shi ɗaya,shiyasa a gidannamu nafi kowa ƙarancin suturar sakawa,hana rantsuwa nema Yah Musbahu yayimin ankon ƴan matan gidan da akayi wata shida dasuka wuce,shine na samu nake ado dashi ranar juma'a.
Kasancewar kasuwar da ɗan tazara tsakaninta da gidanmu,shiyasa saida muka dan taka kafin muka isa.
Wajen rumfata ta kullum na ajiye kayan,itama Asiyah na sauƙe mata nata,yarinyar ba wata babba bace a shekaru,amma nan idan anjima in tafara magana da masu siyan abinci samari,sai ka ɗauka wata hamshaƙiyar budurwa ce,abin yana bani mamaki yanda muhallinnamu gaba ɗaya ya koma haka.
Jejjera komai nayi a muhallinsa na fara zubawa wanda suka zo siyah,wanda dama costomominmmu ne na kullum,sai kuma waɗanda ba'a rasawa.
Hankalina ya tafi wajen zuba abincin,buƙatata na sallami wadanda suka rufemin kai,ohh abin babu daɗi idan aka rufeka kana zuba abincin,wai a hakanma Asiyah na taimakona da zuba miyah,da haka zanyi tayi ni kaɗai,tunda naso ta dunga rakoni amma ammi bata maida hankali da zancen ba,sai yanzu da tasan dole zan bar gidan ai gashinan ta haɗani da ita koh.
Jinayi an yafato hijabi nah ta gefe,dama kuma naji hayaniya a kasuwar,dan dai bana ganin mai yake faruwa ne saboda mutanen dasuke kaina.
Juyowa nayi na kalli indo wacce muke zama rumfah ɗaya,saidai ita gwaten doya take kawowa.
Idanunta a zazzare take nunamin wani waje da yatsunta.
"Ke Sumaimah kalli gacan goje agonki zai sokawa wani wuƙa"
Wani dummm gabana ya bugah,cikin firgici na kalli inda hannunnata ya nuna. Daidai kuwa lokacin da ya burma wuƙar a cikin dattijon daya cakwane wuyan rigarsa a tsakiyar kasuwar.
Wani kaɗawa hantar cikina tayi take na fara jijjiga kai kaman wata ƙadangaruwa,ba fah kuma mafarki nake ba koh,dagaskene wani a kashe a gabana akan idona.
Jini ne yafara feshi daga cikin mutumin ya wanke hannun gojen wanda yake riƙeda wuƙar a hannunsa,kowa yaga abinda ya faru,amma kuma tsoro da firgici bazai bar mutum ɗaukar mataki ba.
Bayan ya sakeshi ya faɗi kafin mutane suka riƙoshi aka nufi asibiti dashi.
Hannunsa ya yarfe yanda jini ya wankeshi sharkaf,wani ne daga gefensa ya miƙomasa tsumma,shima da alama ɗan iskanne kuma yaron sane,dan kansa sai kace gonar ayah,anyi wanann abin da suke cewa dadah.
Jikin wata katanga ya samu a gefensa ya zauna tamkar bashine ya ɗauki rayuwar wani ba,ko nace lafiyar wani.
Tabar wiwi aka miƙomasa ,wani kuma ya kunna masa ashana,buuuu hayaƙi ya turnuke fuskar tasa,baka ganin komai sai gashin kansa mai kama da ciyawa a tsatstsaye.
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,ai a zaune take wani satin i yanzu ƙasa ta rufemin ido,gwanda ma tun daga yanzu nafara bankwana da mutane ina neman gafarar su,danna san ana kaini gidan wannan azara'ilun duniyar tofah saidai sunana kawai dazai saura a doron duniyah.
Indo ce ta watsamin ruwa a kan fuskata,sai sannan tayi firgit na kalleta.
"Wayyo Sumaimah lafiyar ki kuwa,tun ɗazu nake tabaki amma ko motsi bakyayi,saida na zuba miki ruwa kafin kika dawo hayyacinki"
"Iyee ...uhm inaga suman zaune nayi,me...uhmmm"
Kasa ma ƙarisa maganar nayi,dama kuma bansan bai zance ɗin ba,dan gabaɗaya notin kaina ya kwance.
"Nasan mai yake yawo a cikin kanki,amma ki kwantar da hankalinki,bazai taba kasheki ba sai kwananki ya ƙare,wancan ba naji ance wai cunensa yayi ga cibiyar tsaro cewar dashi a fashin da akayiwa gidan gwamnati,amma in bahaka ba bai cika kisa akai akai ba,nina sanshi ai anguwar mu ɗayah"
"Hmmmm indo kenan,so kike nace na yarda da maganarki ko mai,kawai dai kina faɗane dan na kwantar da hankalina,saidai wannan batun babu ma shi,dan raina ya daɗe da tashi ya tsaya,inaga kuwa bazai taba sake komawa ya kwanta ba har zai sanda azara'ilu ya zare shi"
"Haba Sumaimah kar kice haka mana,ba kyau mutum yayi ta zatawa kansa mutuwa fah"
In jinta tana ta daɗin bakinta amma ban bata amsa ba,idona nasake mayarwa wajen da goje yake shida mutanensa,dan bana tunanin zansake sakewa nayi abinda ya kawoni,jikina ma yayi sanyi da zuba abincin,Asiyah ce take ta zuba Musu,dan in sunyi magana ma ba jinsu nake ba,saidai nace uhm uhmuhm.
Har zuwa yanzu tabar hayaƙin yake shaƙa bai daina ba,saidai babu hayaƙin kaman na ɗazu,dan kana iya gano dodanniyar fuskarsa ma daga nesa.
Karaff kaman abin rashin sa'a muka haɗa ido tashi.
Wayyo bammasan mai nakeji a cikin zuciyata ba a lokacin,gashi kaman abun tsafi kokuma nace ya riƙemin idanuwa na gagara ɗaukewa,wani irin hargitsi nake ganowa a cikin idon da babu ɗigon salama a cikinsu,raina banda kuwwar neman tsira babu abinda yake.
Wata ƴar jarumtace ta gifta mun,wacce tasakani saurin ɗauke idona daga cikin nasa,wayyo nasan shikenan sai ya yanka ni,wayyo wayyo shikenan ya kamani ina kallonsa,nasan irin wadannan mutanen kuwa basaso a kallesu shikenan tawa ta ƙare.
"Sumaimah kingani yaronsa Tunga yana tahowa nan wajen,kuma da alama wajenki zaizo,dan ke yake kallo wlh".
Meee shikenan ta faru ta ƙare,indo ke tauraro mai wutsiya ce,bakya faɗan abin alkhairi.
Zuwa zayyi ya fizgeni yakaini wajensa,nima ya yankamin hanjin ciki kaman wancan mutumin.
Da ƙasan ido nake kallon wanda aka ƙira da Tunga ɗin,kuma dagaske inda nake yake nufowa babu makawa........




Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan
09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

SANADIN CACAWhere stories live. Discover now