KAMA DA WANE....(Completed)

By Seemahwrites

14.5K 1.9K 210

even though they look alike that doesn't mean they should have same goals, their life is filled with regret... More

chapter 1
chapter 2
chapter 3
chapter 4
chapter 5
chapter 6
chapter 7
chapter 8
chapter 9
chapter 10
chapter 12
chapter 11
chapter 13
chapter 14
chapter 15
chapter 16
chapter 17
chapter 18
chapter 19
chapter 20
chapter 21
chapter 22
chapter 23
Apology
chapter 24
chapter 25
chapter 26
chapter 27
chapter 28
chapter 29
chapter 30
chapter 31
chapter 32
chapter 33
chapter 34
chapter 35
chapter 36
chapter 37
chapter 38
chapter 39
chapter 40
chapter 41
chapter 42
chapter 43
chapter 44
chapter 45
chapter 46
chapter 48
chapter 49
FINAL
Trailer

chapter 47

220 35 7
By Seemahwrites

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
  🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
                          BATA WANE👩🏻‍🦱
   💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *Na*
        *UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Special gift to *Muhammad Karim*
       *And Fenarh matar Soja*

47👯
Ko wani 'dan Adam da kike gani Cikin duniyar Nan da tashi kalan qaddarar, Kuma Bayan wuya sai Dadi tun lokacin da nasan labarin ku na gane akwai wata babbar qaddarar dake bibiyar rayuwar ku, Allah yasa ayi a sa'a ya Baku zaman lafiya na Taya ki murna sosai Haleesa Kuma insha Allah zamu zo gaba dayanmu har gida mu gaisa da iyayen ku"

"Na gode sosai mama Kuma Dan Allah kuyi haquri da matsalar da na saka ku ciki ban samu damar dawowa na cece ku ba saboda Nima Ina cikin tsaka Mai wuya a lokacin, alhaji Habib ba mutumin kirki bane kwata_kwata ya nemi keta min haddi shiyasa ni Kuma nayi amfani da dama ta na ceci kaina na tsere daga gidan, ban taba tunanin abin zai dawo kanku ba Amman ku yarda dani wallahi banzo gidan Nan da niyar cutar daku ba"

Gwada Mata hanyar daki maman Ameerah tayi da hannun ta tace " hirar namu a bakin qofa zamu qarashe ta ne ba Zaki Shiga ciki ba?"

Murmushi Wanda ya bayyana haqwaran ta Leesa tayi ta Gane Bata qullace ta da komai ba, taja hannun Ameerah suka Shiga ciki Amman Bata zauna ba ta ajiye handbag dinta ta fito tayi alwala tayi Sallah Saida suka zuba Mata tuwon masara da miyan kuka ta zauna taci Tama manta da zancen oga Sa'ood a waje,

Bangaren baba kuwa ya zage sai zuba ma Sa'ood fadanci yake yi saboda tsan_tsan ladabi ko hada Ido yaqi suyi, yasan tunda wannan alhajin yazo qofar gidan shi shida sana'ar tuqi sunyi hannun riga arziqi ne yayi mishi sallama dolen shi ya amsa,

Dan dolen shi a tare sukaje sukayi sallan la'asar suka dawo ya shimfida musu tabarma Yana Masa hiran duniya dukda Sa'ood ba wani saurara yakeyi ba ballantana ya amsa don har yanzu Bai manta irin Koran Karen da baban Ameeran yayi ma Haleesa ba ranar da Saleeha tayi 'bari,

Ganin ta dauki lokaci Bata fito ba yasa ya fara Kiran ta a waya Amman tana gani tayi biris abinta ta saka kwanon tuwo a gaba sai narka takeyi Tama manta da sunyi yarjejeniya ba zata ci abinci a waje ba,

Saida Haleesa tayi tamm sannan ta wanke hannunta ta Sabi jakar ta su maman Ameerah sukayi Mata rakiya har waje, da fitar su Sa'ood ya qaraso inda suke tsaye har qasa ya tsunguna ya gaida maman Ameerah cikin girmamawa irin tsungunon da baban Ameerah yayi mishi, sannan yayi musu kyauta ta ban mamaki kusan irin Wanda yayi ma shugaba ya dauki amaryar San suka Kama hanyar gidan Dan gaba daya ya gaji,

Rage speed din motar yayi Yana qare Mata kallo Yanda take ta faman murmushi ita daya, dukda ta wahala da tafiyar da sukayi a tsatsatsaye Amman yau tana cikin annashuwa sosai,

"Novio shi wannan farin cikin Kuma na menene?"

Dan Juyowa tayi ta kalle shi sannan ta juya tana qara fadada murumushin ta
"Ya Sa'ood yau ji nakeyi kaman an sauqe min wani nauyi dake Kan qirji na tunda na rabu da mutanen Nan, they owe me a lot dukkan su na Shiga cikin rayuwar su kuma na fita lokaci Daya ba tare da wata qwaqqwaran sallama ba sai yau Allah ya dawo Dani na gyara kura kuraina mukayi sallama suna murmushi, I feel relieved, and all the credits goes to you thank you so much ya Sa'ood"

" Ba sai kin gode min ba Haleesa, wannan abun nauyi ne a kaina na sauqe duk wani abun da ya danganci mamanmu na riga nayi alqawarin daukan nauyin Sarwa bazan taba karya wannan alqawarin ba musamman yanzu da Kika zama farin ciki na Kuma kike Shirin zama abokiyar rayuwata,

nasan baki da masaniya a kan irin son da nake miki Amman inason jaddada Miki Ina sonki Kuma ban taba muradin kasancewa tare da wata ba Bayan Sarwa Kuma cikin sarwan sai Allah ya zaba min ke and I'm so happy with that, I love you so much Haleesa"

Duk wannan bayanin da yake yi hankalin shi Yana Kan titi Amman kallo Daya zakayi mishi ka fahimci kalaman daga cikin zuciyar shi suke fitowa, baiyi tsammanin zai samu amsa daga gare ta ba Amman da mamaki sai ji yayi tace

"Nima Ina sonka ya Sa'ood, sosai!!"

Da mamaki ya juyo Yana kallon ta Yama kasa magana Dan baisan mafarki yakeyi ko gaskiya ba wannan 'yar taurin Kan ne take fada mishi tana son shi, sake jaddada mishi tayi

"Yess ya Sa'ood, Ina sonka sosai da sosai Kuma Ina godiya ma Allah da yasa Zan kasance tare da Kai nasan tabbas nayi dacen abokin rayuwa"

_A gaggauce pls_

yau ta Kama Friday akayi waliman amarya su shugaba da muqarraban ta an nutse cikin hijab, jinta takeyi wani banbara qwai rabon ta da saka hijab ai tafi shekaru 30 Dan Sallah ma Saida Sa'ood yayi musu walfare suka fara yi,

yanzu an kashe gidan karuwaan shugaba ana ta ginin masallaci a wurin su Kuma 'yam matan wurin harda ita kanta shugaban duk ya sama musu aiki a orphanage da albashi Mai gwabi ga ci da Sha harda sutura masu kyau tuni aka yada rayuwar bariki"

Bilkisu da sauran ma'aikatan da sukayi aiki tare da Leesa a gidan alhaji Habib ma Sa'ood ya Basu aiki a orphanage din dan Bayan zuwan su jigawa da kwana 3 ya turo hukuma suka garqame alhaji Habib da sauran burbudin laifin Garba TK Wanda yawanci bilkisu ne da kanta ta kawo evidence da aka Kama shi da laifuka masu tarin yawa Wanda idan ya Shiga prison Hala bazai fito ba har qarshen rayuwar sa,

Matar sa kuwa duk izzar ta da Isa haka ta dawo abin tausayi domin ita ba 'yar kowa bane iyayen ta ma Basu raye, tashin ghetto area near kawai yasa ta dawo wata haka, uwar gidan shi kuwa tattaran yaranta tayi suka koma gidan iyayenta, daga qarshe dai itama a qarqashin su Leesa ta samu aiki,

31st Oct 2020
Saturday
11:00am

Dumbin mutane suka shaida daurin auren
*Sa'ood khalifa Mailafiya*
Da amaryar San
*Haleesa Aliyyu Mailafiya*
Wanda ya samu halartan manyan mutane masu fada aji da Kuma manyan qusoshi dake Nigeria da kewaye

Suna Shiga part din momy suka buga wani shewa ana snapping pics dinshi ta ko Ina ga 'yan uwa sun cika parlorn da qyar ya kutsa ya shiga dakin shi dake part din dan yanzu mamanmu ta zamo surkuwa,

Zolaya irin nasu na abokai suka fara mishi gaba daya sun Hana shi sakat musamman ma barrister Adam, kowa a dakin Yana ta hayaniya Banda mutum daya, yake Chan quryan gado ya rungumi wayan shi kamar wata mace,

Da qarfi Adam yayi sufa ta gefen shi Yana bugun shi da kafada, siririn tsaki yaja ya sake matsawa baice mishi komai ba,
"Future KD governor, shugaba Babu iyali Kenan Kai see yaushe zakayi aure ne? Daman ku biyu kadai kuka rage Mana Kuma yau SD ya fita daga cikin list"

Sake Jan wani tsakin yayi ya dago Yana hararar barrister Adam "malam da'alla ka tashi ka bani wuri, ka matseni da yawa"

Sa'eed ne ya dawo ta gaban shi ya tsuguna Yana bashi gaba daya hankalin shi kaman zasuyi maganar arziqi,

"Allah Ameer idan kana so zamu nema maka santaleliyar budurwa sabon jini from 17 to 20 a cikin familyn Nan, wallahi auren su Dadi ka taba kaji Ina fada maka sai ka gode min daga baya"

Da sauri Sa'ood ya ajiye babban rigan shi da ya cire shima ya qaraso inda suke zaune Yana girgiza yatsa
"Aa wallahi, kull ban yarda ba ko 'yammata zasu kashe mu a gidan Nan ba zamu bada ko 'daya ma Ameer ba tunda baisan darajar su ba, haka kawai mu bashi yarinya a ranar ya maida Mana ita bazawara? Imposibble kawai ka tambaye shi yaushe zaiyi aure zamuyi mishi Kara muje kafin ya sake yin abin kunya"

" Kaima kasan ko da kudi aka bani yarinya bazance inaso ba ballantana ku tallata min qannen ku wanda sukayi kwantai, sanin kanku ne bani aure saidai ayi min yanzu Haka ma sun saka Rana Nan da wata 5 masu zuwa Kuma abin mamakin shine ko taba ganin yarinyar banyi ba Kuma bani fatan na ganta"

Nuna shi da yatsa Adam yayi ya hade fuska cikin zolaya yace "wannan Kuma ruwan ka, ko ka ganta ko kada ka ganta duk Daya Amman ka kuskura ka sake cutar da 'yar mutane ni da kaina zanyi tsaya Mata sai na jefa ka a kurkuku qaton gwabro kawai"

Ku Taya ni da addu'a please yau na tashi da ciwon Ido daya sosai🤕

#vote
#share
#comment

Continue Reading

You'll Also Like

2.3K 56 5
Koharu, after dying of Truck-kun Koharu find yourself in the void having no body. After a few decades drifting in the void a god took notice of your...
15K 1.5K 20
The romance between two high school sweethearts. Two people who have hurt each other so much and yet want no one else but one another. Munayah is a s...
499K 36.7K 38
Avantika Aadish Rajawat Aadi, with his fiery nature, adds intensity and excitement to their relationship, igniting a spark in Avni. Avni, like the ca...
219K 17.1K 22
On Hold Wanna visit rajasthan than read this special book about my love Rajasthan 💗