KAMA DA WANE....(Completed)

By Seemahwrites

13.2K 1.8K 210

even though they look alike that doesn't mean they should have same goals, their life is filled with regret... More

chapter 1
chapter 2
chapter 3
chapter 4
chapter 5
chapter 6
chapter 7
chapter 8
chapter 9
chapter 10
chapter 12
chapter 11
chapter 13
chapter 14
chapter 15
chapter 16
chapter 17
chapter 18
chapter 19
chapter 20
chapter 21
chapter 22
chapter 23
Apology
chapter 24
chapter 25
chapter 26
chapter 27
chapter 28
chapter 29
chapter 30
chapter 32
chapter 33
chapter 34
chapter 35
chapter 36
chapter 37
chapter 38
chapter 39
chapter 40
chapter 41
chapter 42
chapter 43
chapter 44
chapter 45
chapter 46
chapter 47
chapter 48
chapter 49
FINAL
Trailer

chapter 31

231 40 5
By Seemahwrites

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)
🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
BATA WANE👩🏻‍🦱
💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Blog : prowritersnovels.blogspot.com

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*Na*
*UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Special gift to *Muhammad Karim*
*And Fenarh matar Soja*

31👯
Matso da cameran wayar shi yayi daidai fuskar ta Yana dariya yace "kici a hankali Mana sister, abincin ba guduwa zaiyi ba idan ma ya qare zan saka a qaro Miki wani kiyi ta dirka"

Tsayawa da cin abincin tayi ta dago tana kallon shi
"Meye haka ya Sa'ood? Yaya zaka dinga shooting dina Ina cin abinci"

" Because you are eating like a horse, hakan kuma ya dace dake kina wasu abubuwan kamar Mai tabin hankali Amman daga baya kizo kinayi wa mutane iyayi"

" Koma Yaya ne Kai ka jawo, gashi saboda Kai tun safiya ni ba azumi nakeyi ba Amman babu abinda naci"

" Wannan kuma laifin ki ne saboda rashin hankali da na sauqe ki a hanya sai ki tafi wani wurin?"

" To Yaya kake so nayi?"

" Ki nemi abin Hawa ki koma gida mana! Raina ya baci ne a lokacin shiyasa nayi Miki haka"

" Na koma gida saboda ka qara Mara zuciya a Kan zagin mahaukaciya da Mara tarbiyya da kake min? Bani da wani wuri da zan Kira da gida Bayan inda na fito, ni ban Saba da rikici ba ko a gidan karuwai ba'a rikicin da kukeyi, I always have freedom sai abinda naso zanci sai abinda naso zan saka Kuma wurin da nayi niyya kawai nake zuwa babu wanda ya taba min dole da katsalandan cikin al'amura na bayan Kai, ka gama Isa ta inaso nayi nesaa dakai sosai ya Sa'ood I don't like you"

Shiru Sa'ood yayi Yana kallon Leesa gaba daya jikin shi yayi sanyi, baiyi tunanin akwai ranar da wata zata Budi Baki tace ta washe shi ba musamman ma daga cikin Sarwa, Yana tuna lokacin da suke jarirai Yana kula da su burin Shi bai wuce su Sami kusanci dashi kaman Yanda ya samu da mahaifiyar su ba, he loved and cherished the girls so much Amman bayi hango Koda shaquwa ne tsakanin su, ba'a maganar Saleeha ma don ko kallon shi na mintuna 5 Bata taba tsayawa tayi ba ko yaushe tana manne jikin Sa'eed,

Daukan tissue tayi ta goge hannun ta sannan ta koma cin abincin da spoon tana diban kadan_kadan tana ci a hankali, Bata qara yafi spoon biyar ba ta tashi tace su tafi ta qoshi, kallon plate din abincin yayi yaga da saita da yawa a Yanda ta fara ci yayi tunanin zata iya cinyewa har ta nemi qari,

"Baki Gama cin abincin kin ba fa Haleesa, ki zauna ki qarasa zan jira ki"

" No thanks, I'm full I don't want to continue eating like a horse"

Kallon ta yayi a kaikaice hade da lanqwasa murya yace "ke shirmammiya I was just joking, ki zauna Dan Allah ki qarasa cin abincin ki, I'm sorry Kinga ma zan goge videon"

" Babu buqatar hakan ya Sa'ood kawai mu tafi" taje ta wanke hannun ta yayi settling bills din suka tafi,

Cikin mota kuwa shirun da Leesa tayi ya dami Sa'ood yafi so yaji ko yaushe tana jero tambayoyin ta da Basu qarewa dan hakan ne kawai yake tabbatar Masa Bata cikin wata damuwa,

Juyowa yayi Yana kallon fuskar ta dake daure tana kallon window yace "are you ok?"

Bata juyoba tace "yes I'm fine"

Shiru ne ya ratsa tsakanin su kafin Sa'ood ya sake jefa Mata tambaya "wani makaranta Kika yi?"

" Govt comprehensive secondary School"

"Ajin ki nawa yanzu?"

"Ina ss2"

Gyada Kai yayi yace ok "Amman waye yake daukan nauyin karatun ku?"

"Why do you care?"

" Kin gani ko Haleesa bani don tsaurin idon kin nan at least kina girmama manyan ki, ni yayanki ne Kuma dukda akwai Idris a gaba na Amman nine guardian dinki, ko auren ki aka zo nema ni zan bayar duk wani Abu da ya shafe ki da 'yar uwarki nine jagora shiyasa nake son na San komai a Kan rayuwar da kukayi lokacin Baku tare da mu"

Tabe baki Leesa tayi tace "ok guardian angel ka sauqe ni a shago akwai abun da nake so na siya"

Gaba kadan suka qara yayi parking a gaban wani store "kiyi sauri ki gama mu tafi Kinga dare yayi sosai"

" To ya Sa'ood da wani kudi zan sayi abin? Sani kanka ne bani da ko sisi a jikina"

"Fadi menene naje na siyo Miki kada ki Bata min lokaci"

Hannun ta dake Kan cinyarta ta fara was dashi ta riqo bakin hijab dinta tana nannadawa jikin yatsar ta guda daya, hakan ya bama Sa'ood daman qarewa cinyoyin ta kallo a Karo na farko Dan skirt din dake jikinta ya dan Kamata,

Wani irin mugun Abu yaji Yana bi tun daga yatsar qafarshi har zuwa tsakiyan kansa da sauri ya balle marfin motan ya fita ba tare da ya tsaya ta fada mishi abun da take so ba don ya riga yasan koma menene,

Shiga store din yayi ya Mata shopping sosai duk dan ya samu ya dauki lokaci kafin ya koma saboda abinda yake ji ya sauqa,

Har suka Isa gidan Idris Bai sake ce Mata komai ba ko magana tayi daga yace Mata "umm" sai "uhm_uhm" haka itama ta gaji da tayi shiru,

Rakiya yayi Mata har qofar main parlor sannan ya Ciro shopping bags daga back seat ya miqa Mata " gashi duka naki ne, and one more thing na riga da na sanar ma sauran kema ki shirya insha Allah gobe zamu koma gidan mu za'a sallami mamanmu da Kuma Salee daga asibiti, I promise bazan tada wani rikici ba tunda kince baki so Kuma akwai abun da nake so na sanar dake Amman ba yanzu ba sai komai ya daidaita tukunna"

Gyada Kai tayi fuska ba yabo ba fallasa tace "ok Allah ya kaimu, thank you"

Zaro Ido yayi kaman Wanda yaga wani abun tsoro yace
"Daman kin iya godiya? Na dauka ai ba Zaki taba Yana abin da wani zai Miki ba musamman ma ni Wanda Kika wasa"

Murmushi Mai sauti tayi Dan abun da yayi ya Bata dariya " ya Sa'ood Kenan har yanzu baka San wacece Haleesa ba tunda har ka iya bada haquri me zai hana ni yin godiya?"

"Haka ne, zanso insane wacece Haleesa saboda na tabbatar da abin da nake ji, yanzu dai barci nake ji Saida safe"

" Ok Allah ya tashe mu lafiya"

Da "ameen" ya amsa sai Kuma ya ja ya tsaya,

" Ka tafi Mana yaya Sa'ood ko ka daina Jin barcin ne?"

Girgiza Kai yayi yace " no inaso ki fara Shiga ciki ne tukunna"

Sallama ta sake yi mishi ta juya ta shige ciki tana waiwayen shi, sauqe ajiyan zuciya yayi ya wuce dakin da yake kwana ya zuba a Kan gado, har yanzu kuzarin shi Bai dawo ba Yana so yayi wanka kafin ya kwanta Amman a yanayin da yake ji bayi tunanin zai iya daga Koda cokali ne kuwa,

Juyi yakeyi bisa gadon Yana tunani, Yana son Saleeha Kuma Yana burin auren ta ga Kuma wata dama ta same shi cikin Sa'eed dake jikinta ya zuba yasan cikin sauqi zai iya maida ita nashi Amman Kuma idan hakan ta faru yayi ma yarinyar adalci?

Yana ganin zallar so da takeyi ma Sa'eed yasan idan har ya raba ta dashi zai cutar da ita dan zuciyar ta ya riga ya Gama narkewa da wutan son 'dan uwanshi tunda gashi shine sanadin mutuwar jaririn ta Amman batayi fushi dashi ba, zuciyar ta me tsafta ne sosai ba kaman na Haleesa ba yasan da ita ne hakan ya faru da ita za'a kwashi drama,

Yana Jin wani Abu game da Haleesa Amman ba soyayya bace it's something else, dukda tana da taurin Kai da rashin da'a Amman qwarin guiwar ta yana burge shi tana tsayuwa tsayin daka Akan al'amuran ta harma da na Saleeha shiyasa har zuwa wannan lokacin rayuwar su Bata lalace ba Amman shi ba irin matar da take so ba Kenan,

Yafi son mace Wanda take kamar mahaifiyar su, very nice, calm and silent Yanda ko wani namiji zai iya tankwara ta ya juya ta Yanda yake so, Yana son uwa ta gari ma 'ya'yan shi amman bayi da tabbacin Haleesa zata iya zamowa haka saidai Bayan Saleeha ita kadaice zabin da ta rage mishi gashi Kuma da bakinta ta fada mishi ta washe shi ba zai iya auren macen da Bata son shi ba,

Da qyar ya iya tattaro sauran kuzarin shi ya rage kayan jikin shi sannan ya Shiga bathroom hade da sake ma kanshi ruwa, Yana qoqarin kawar da tunanin Haleesa daga ranshi ya fara tsaya Yanda Shirin komawa cikin familyn sa zai kasance,

**********
7:33am

Sa'eed ya shigo dakin da aka kwantar da Salee ya samu tana breakfast gashi dan kwana Daya da wuni da tayi ba tare da cikin a jikin ta ba har wani haiba ya sata dan ta samu hutu sosai, da lokacin baya ne bazai gane was kanta ba da safen Nan har sai Rana ta fara zafi kafin ta dawo dai_dai,

Murmushi ya sakar Mata yace "good morning babe"

Da "morning" ta amsa tana qoqarin matsa Masa ya samu wurin da zai zauna, matso da fuskar shi daff da nata yayi Yana qoqarin kissing dinta da sauri ta matsa baya tana gyaran murya, sai lokacin ya lura da Zarah tana tsaye tana kallon su,

Tashi yayi cikin basarwa ya qaraso wurin da take tsaye suka gaisa sai inda_inda yakeyi da ta lura da hakan sai ta fake da zata je duba mamanmu ta fita daga dakin Dan Basu wuri su gana ba zata iya Hana Sa'eed abin da yake muradi ba, she can clearly see that yafi son Salee a kanta,

Tana fita daga dakin ta fashe da kuka, Babu shakka yanzu ta Riga da ta zama bora tun jiya kowa take ta murnan Shirin komawa mansion Amman a maimakon haka ita baqin ciki takeyi tasan wannan haduwar Kan na Mailafiya family ba zai zamo alkhairi a gare ta ba Amman Babu Yanda ta iya, tata qaddarar Kenan,

Kafin Sa'eed ya fita daga dakin ma su Sa'ood da sauran mutanen gidan sun qaraso harda momy da uncle Ishaq da maman Zarah da Sumayya da mahaifiyar ta dama sauran members na family, Haka suka cika asibitin Nan Damm kaman do in su aka yi shi,

Sa'ood da Sa'eed ne suka tafi police headquarter sukayi duk wasu cike_cike tare da safe hannu Akan takardan dake dauke da alqawarin idan suka Shiga cikin mansion dinsu zasu fito da takardun gidan da sauran kadarorin su dake riqe a hannun hukuma sannan suka kwashi zugan police suka tafi,

Wannan karon Koda sukaje bude vault din basuyi fada ko tashin hankali ba domin da Idris a tsakanin su suna fara hayaniya zai dakatar dasu,

Cikin nasara makullin da password da mamanmu ta fada yayi daidai suka tattaro takardun akayi duk wani abun da ya dace sannan suka wuce banki daga wurin ,

Abinka da masu shi cikin qanqanin lokaci aka bude musu account dinsu da akayi freezing credit cards dinsu da akayi declining suka dawo aiki lokaci Daya mutanen da a jiya suke ba komai ba suka dawo wasu,

Nan attention din media ya dawo kansu ko wani news headline na tv da gidan radio maganar su akeyi familyn da suka rasa komai shekaru 17 da suka wuce gashi Rana daya sunyi regaining propertyn su,

murna wurin mutanen dake da alaqa da su da masu aiki a qarqashin su ba'a magana, dan ko wani ma'aikaci a ranar ya koma bakin aikin sa ba tare da sun jira umarni daga iyayen gidan su ba aka fara gyare ko Ina...............🧚

#vote
#share
#comment

Continue Reading

You'll Also Like

119K 13.2K 32
COMPLETED English/Hausa For someone who has never had it easy in life, Labiba believed her world has finally come to an end when she was practically...
590K 27.1K 42
Needs editing [ the destiny series #1] 𝑻𝒉𝒆 𝒇𝒂𝒕𝒆 𝒑𝒖𝒔𝒉𝒆𝒅 π’•π’‰π’†π’Ž 𝒂𝒑𝒂𝒓𝒕 𝒃𝒖𝒕 π’…π’†π’”π’•π’Šπ’π’š π’‚π’ˆπ’‚π’Šπ’ 𝒑𝒖𝒍𝒍𝒆𝒅 π’•π’‰π’†π’Ž π’•π’π’ˆ...
3.9K 451 18
If there is any part of you that makes you think I will ever fall for you then that part ........"shhhh" he said cutting her shut, pressing his index...
74.5K 7.9K 45
Two sisters given birth But separated Find out more in the novel!!!