KAMA DA WANE....(Completed)

By Seemahwrites

13.2K 1.8K 210

even though they look alike that doesn't mean they should have same goals, their life is filled with regret... More

chapter 1
chapter 2
chapter 3
chapter 4
chapter 5
chapter 6
chapter 7
chapter 8
chapter 9
chapter 10
chapter 12
chapter 11
chapter 13
chapter 14
chapter 15
chapter 16
chapter 17
chapter 18
chapter 19
chapter 20
chapter 21
chapter 22
chapter 23
Apology
chapter 24
chapter 25
chapter 26
chapter 27
chapter 28
chapter 30
chapter 31
chapter 32
chapter 33
chapter 34
chapter 35
chapter 36
chapter 37
chapter 38
chapter 39
chapter 40
chapter 41
chapter 42
chapter 43
chapter 44
chapter 45
chapter 46
chapter 47
chapter 48
chapter 49
FINAL
Trailer

chapter 29

246 33 3
By Seemahwrites

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)
🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
BATA WANE👩🏻‍🦱
💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*Na*
*UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Special gift to *Muhammad Karim*
*And Fenarh matar Soja*

29👯
"Fortune?" Haleesa ta maimaita cikin sigar tambaya, "Amman Mai yasa suka saka Mana makullin a jikin mu kasancewar mu qananan yara a lokacin?"

Murmushi tayi tace
" Because they have faith in me Haleesa, sun yarda cewa wani cutarwa bazai taba samun dukiyar su ba indai Yana tare dani shiyasa suka danqa min shi, babu abinda yafi daga min hankali lokacin da kuka bata kaman salwancewar dukiyar Mailafiya family I somehow believe wata rana Zaku dawo gareni Amman bani da tabbacin Zaku dawo tare da sarqan ku, shiyasa kwata_kwata ba'a son ku rabu Dan Rabin makullin bazai taba amfani ba saida daya bangaren"

Maida duban ta wurin Sa'ood tayi tace "Chéri please take your brothers along, inaso kayi qoqari ka kawo qarshen qiyayyan dake tsakanin ka da 'dan uwanka yanzu komai ya gyaru kaje ka sameshi kuyi sulhu Dan a irin wannan lokacin Kuna buqatar juna"

Juyar da kanshi gefe yayi cikin bacin rai yace " ba zan iya ba cariño Sa'eed yaci Amana ta ya yaudare ni, ya cutar Dani da yawa bani Jin zan iya yafe mishi idan Bai rabu da Saleeha ba, kawai ya saketa sai a zauna lafiya"

"Ashe akwai ranar da zata zo na roqi alfarma a wurinka kaqi min Sa'ood? Banyi tunanin canzawar da kayi har ya taba tarbiyyan ka ba, inda haka rayuwa take baka yafe was na kusa da Kai da ban yafe maka kisan Garba TK da kayi da sunan daukan fansa ma kawun KU ba Dan ban buqaci hakan daga gareka ba, da tuntuni na miqa ka ma hukuma kaman Yanda kayi ma 'dan uwan ka"

Baice da ita komai ba ya juya zai fita yana jin zuciyar shi yayi mishi nauyi, tabbas Yana son Sa'eed kasancewar shi jinin shi Amman Yana son Salee ma tun Bata tare dasu yayi qoqarin Gina zuciyar shi a Kan soyayyar ta, ta Yaya lokaci Daya Sa'eed zai kwace Masa ita Haka nan Kuma ya haqura?"

Sanin halin shi yasa ta Kira sunan shi ganin zai tafi Kuma alamu sun nuna Bai dauki maganar ta ba, Juyowa yayi Yana kallon ta

"Dan Allah Chéri reconcile with Sa'eed ba Dan ni ba sai Dan qalubalen da Zaku fiskanta wurin maido Mana da kadarorin mu, har yanzu case din hospital Bai qare ba sun kulle Sa'eed na shekaru da yawa Amman nayi Imani ba shi ya shigo da banned drugs da yayi amfani dashi mutane suka jigata ba it was all a setup, ka ceci martaban zuri'an mu dan Allah ka bankado sirrin Wanda ya Bata Mana suna"

" Insha Allah cariño nayi Miki alqawari duk Wanda ya aikata wannan danyen aikin sai na gurfanar dashi a gaban kotu, sai ya wulaqanta kaman Yanda ya wulaqanta 'dan uwana bazan Baki kunya ba, Amman idan komai ya qare sai ya rabu da matata Dan wallahi bazan bar Masa Saleeha ba"

Yana kaiwa Nan ya bude qofar ya fita dan bayison ma a sake tada maganar tunda yace yanaso to sai ya samu ko ta halin yaya ne, da gudu Leesa ta bishi a baya ba tare da tayi wa mamanta sallama ba,

Shan gaban shi tayi tana haki ta dago tana kallon shi ya zuba Mata Ido yaji yanzu Kuma da me tazo,
"Tafiya zakayi ka barni Bayan kasan bani da Wanda zai maida ni gida?"

" Ok da so kikeyi inzo kunnen ki na musamman ince Miki ki tashi mu tafi? Ai ke ba makauniya bace dake buqatar 'dan jagora" ya raba ta gefen ta ya wuce,

Qwafa tayi ta bishi a baya suka Shiga cikin motar shi ya tada suka bar haraban asibitin,
Sun danyi tafiya Mai nisa taga zaman shirun Nan bazai fishshe ta ba, Juyowa tayi tace
"Wai me kuka dauki 'yar uwata ce?"

Saida ya dan yi shiru sannan yace "Wata 'yar uwan taki?

" Inada wata 'yar uwa ce Bayan Saleeha Kun maida ta kaman wani qwallo sai passing_passing kukeyi da ita da Kai da wancan Sa'eed din ko ance Muku ita dabba ce da Bata da 'yanci Wanda kowa zai mallaketa a duk lokacin da yaso?"

Murtuqe fuska yayi ya ci gaba da driving ba tare da ya tanka ta ba cikin ranshi Yana takaicin rashin da'a da ita fitar da magana da Haleesa ta daukar ma kanta kwanannan, Jin yayi shiru yasa ta sake cewa

"Magana nakeyi da Kai fa baka bani amsa ta ba"

Sauqa yayi daga Kan hanya yayi parking sannan ya juyo yace Mata "fita min a mota"

"Saboda me?"

"Saboda haka nace, Zaki fita ne ko sai na fitar dake?"

A zuciye ta bude marfin motan ta fita hade da banging dinshi ta juya zatayi hanyar da ta gani ta hannun damar ta, Saida ya qarasa daff da ita ya sauqe glass Yana kallon Yanda take cika tana batsewa yace "mahaukaciya Mara tarbiyya kawai idan har kinason in zauna lafiya tare dake sai kin koyo manners"

Leesa Bata San lokacin da hawaye ya fara zarya a kumatun ta ba, maganar da Sa'ood ya jefeta dashi ya cakke ta har cikin zuciyarta meyasa zai kirata Mara tarbiyya? Duk iya qoqarin da fadi tashin da tayi Basu gani Kenan? Ai idan ta zamo Mara tarbiyya ma ba laifin ta bane laifin su ne gaba daya dan hakkin Basu tarbiyya a kansu yake,

Tafiya takeyi tana share hawaye ta tsani wa'innan 'yan biyun da suka zo suka wargaza Mata tsarin rayuwar ta sun raba ta da Salee sun Sanya ta cikin kadaici na HAR ABADA tasan indai Sa'eed na raye Salee ba zata taba goya mata baya ba yanzu haka zata ci gaba da gwagwarmaya ita kadai Dan ba zata taba komawa wancan gidan ba never!

**********

Kafin Sa'ood ya Isa gida sai da ya Kira Idris ya fada mishi saqon mamanmu Akan yazo ya same shi a gida daga nan sai su tafi tare, ya dade zaune a cikin mota Yana tunanin Yanda za'ayi ya samu Sa'eed bayison yayi tsammanin ya yafe mishi yaudaran shi da yayi,

Ana Haka sai ga hydar yazo wucewa da ball a hannun shi zuge glass yayi ya Kira shi,
"Daddy zo Nan"

Da gudun shi ya qaraso Yana washe haqwara " gani uncle"

"Uncle Sa'eed Yana gida?"

" Eh Yana Nan" " ok kace Ina neman shi Kuma yayi sauri"

Da "okay" ya amsa ya sake kwasan gudu yayi ciki ba'a dade ba Sa'eed ya fito ya zaga passenger seat ya zauna sannan ya juyo Yana fuskantar Sa'ood da murmushi dauke a fuskar shi,
"Brother gani kace Wai kana nemana ko?"

Da kaman ba zaiyi magana ba sai Kuma yace "bani nake nemanka ba mama ce tace aje a fito da takardun kadarorin mu,ta bani sarqan Sarwa shine makullin vault din sannan ta fada min password dinshi Kuma umarnin ta ne mu tafi tare yanzu sai ka jira brother ya qaraso mu wuce"

Gaba daya jikin Sa'eed yayi sanyi ganin Yanda yake magana ma ko kallon shi bayi yi, da hydar ya fada mishi Sa'ood na neman shi yayi tunanin shiryawa zasuyi Amman kaman har yanzu Bai yafe mishi ba,

Murya a sanyaye yace "brother har yanzu fushi kakeyi da ni? Dan Allah kayi haquri ka yafemin inason komai ya dawo Kaman da musamman yanzu da zamu koma cikin mansion dinmu bani son yaranmu su fiskanci halin da muke ciki "

" Hmm Sa'eed Kenan I'm not surprised don ka dade da zama babban maqaryaci tunda har kake cewa kana son abubuwa su koma kaman da Bayan baka shirya bani abinda na nema daga wurin ka ba after all she is mine, kana rabuwa da Saleeha ni da Kai zamu koma kamar bamu taba samun wata matsala ba Amman nasan ba zakayi hakan ba dole sai na karba da qarfi"

" Haba brother ta Yaya kakeso na rabu da uwar 'dana ko'yata? Saleeha is pregnant with my child kaje ka auri Haleesa Mana Dan Allah, komai nasu iri daya ne Bayan murya babu abinda ya banbanta su....."

" Sai Kuma ruhi da halayya, ni Saleeha nakeso ba fiskan ta ba, Kuma ma Banga dalilin da zaisa ka hada ni da Haleesa ba fitsararriyar yarinya Mara kunya, tun a baya kasan tsarina bani son fallalliyar mace shiyasa nayi ta zaman jiran Sarwa su girma dan nasan idan suka dauko mahaifiyar su zasu dace da irin matar da nake son aura Amman Haleesa Bata dauko hali Mai kyau ba"

" So yanzu ba zaka haqura ka fita harqan iyalina ba Kenan?"

"idan kayi tunanin zan canza shawara to ka yaudari kanka don ni idan na dauki so bani taba ajiyewa"

" Wannan Karon ya zamo maka dole ka ajiye dan wallahi sai inda qarfi na ya qare a Kan iyalina zan Kare Saleeha da rayuwata ba zan taba Bari wani cutarwa ya iso gareta ba"

" Daman na riga na Sani duk iya qoqarina in Kai zuciyata nesa sai ka qureni Sa'eed mu zuba mu gani ni da Kai waye zai ci nasara Koda kuwa zan rasa rayuwata sai na maida Saleeha ta zamo tawa"

"jahilin banza kawai wataran taurin kanka sai ya kaika jahannama tunda an riga an fada maka babu aure a tsakanin ku Amman ka dage sai ka aikata Haram"

Da mugun mamaki Sa'ood ya kalli Sa'eed Yana nuna kanshi hade da fadin "ni ka Kira jahili Sa'eed?"

"Kana tantama ne? Ai abinda kake Shirin aikatawa yafi qarfin jahilci saidai a Kira shi da hauka"

Daga qarshe cacan bakin gagaran su yayi a cikin mota sai da suka fito waje suna hargowq kaman zasu bugi juna, Jin hayaniyan su yasa mutanen gidan fitowa suka zuba ma sarautan Allah Ido Dan babu Mai iya rabon wanna gagarumin fadan a cikin su gashi Idris bayi Nan,

Salee ne tayi qarfin halin qarasawa wurin su tana janye Sa'eed da 'dan qarfin da ya rage Mata, badan kalan kayan su ya banbanta ba Kuma tasan kayan dake jikin Sa'eed kafin ya fito ba ba lallai ta iya gane shi ba Dan Yanda yake tada jijiyoyin wuya har yafi Sa'ood dinma, Bata taba sanin Hala take da zafin rai ba sai yau,

"Abban Al'amin dan Allah kubari abinda kukeyi Bai Kamata ba"

" I don't care nidai babu Wanda ya Isa yace zai raba ni dake duk duniyar nan wallahi ko wanene sai yaga bacin rai na"

Gyada Kai tayi tana Qara janye shi gefe tace "naji babu Wanda zai rabamu, mu tafi ciki Dan Allah fada Bai kamace ku ba"

Murmushin gefen Baki Sa'ood yayi Yana girgiza Kai "ka Gama duk abinda zakayi Sa'eed Amman ka sani ko me zai faru I must make Saleeha mine saina raba ka da ita I promise you that"

Wani kukan kura Sa'eed yayi ya cukumo wuyan rigan Sa'ood Yana zare Masa idanu jijiyoyin jikin shi sun tashi rada_rada har wani karkarwa yake saboda bacin rai,

Billahil Azeem baka Isa ba ina son matata Kuma baka Isa ka rabani da ita ba Sa'ood, zan iya bari maka komai a duniya Amman Banda Saleeha Ina sonta Ina qaunar ta sannan ya zamo min dole na zauna tare da ita Kuma babu abinda zaka iya a Kai,

Ganin fada na son barkewa a tsakanin su yasa hankalin Salee a tashe ta Shiga tsakanin su tana qwace riqon da sukayi ma juna da qarfi Sa'eed ya ture ta gefe sai da tayi baya ta bugu da bango sannan ta zube a qasa tana sakin wani razanannen qara,

"How dare you touch him? Shi ba mijinki bane nine kadai mijinki kada ki kuskura ki sake qoqarin taba jikin shi"

Salee kanma ba Jin abinda take fada takeyi ba saboda wani azaba da taji bayanta da ta buga Yana Mata ga ciwo da cikin ta da qwanqwason ta ya kama lokaci daya, dafe bayan tayi tana kuka sai a lokacin qwaqwalwar Sa'eed ya hasko mishi barnan da ya aikata da sauri shi da Sa'ood sukayi kanta suna qoqarin daga ta ya buge shi Yana gwada shi da yatsa,

"Kada ka kuskura hannun ka ya taba min Mata kaji na gaya maka" sannan ya ciccibeta Yana kallon Yanda jini ya Bata wurin da ta Fadi, Jin kaman an dake marar ta da guduma yasa ta sake sakin wani razanannen qara,

Ihu take qwalawa da ita qarfin ta tana yarfa hannuwa Jin zafin yafi qarfin Yanda take tsammani ga jini dake gangarowa daga qasan ta, gaba Daya Sa'eed ya rikice yana rungume da ita a jikin shi, sai yayi kaman zai Shiga ciki sai Kuma ya dawo,

Sa'ood ne yayi azancin Shiga mota ya kunna sannan ya qaraso inda suke tsaye ya bude musu back seat Yace su Shiga, suna Shiga yaja motar da gudu suka bar gidan sai asibiti, suna fita motar Idris na shigowa Nabeela tana mishi bayanin abinda ya faru yace ta Shiga motan suka bisu a baya,

Sake tattaran ta Sa'eed yayi suka Shiga cikin asibiti babu Bata lokaci akayi admitting Salee aka fara Bata agajin gaggawa, yayi duk wasu cike_cike da ya Kamata sannan suka zauna zaman jira, shi likita ne yanaso ya taimaka wa matarshi sosai yake tausayin Salee Kuma Yana nadamar abin da yayi Mata Yana so ya Shiga yaga halin da take ciki but he is a doctor without license ba zai samu wannan Daman ba,

har qarfe 3 suna zaune a wurin babu Wanda yayi sallan azahar a cikin su day qyar Nabeela da zarah suka kora su Wanda itama Bata Dade da zuwa ba,

Suna dawowa daga masallaci suka samu doctor ta fito daga wurin ta da sauri sukayi kanta suna tambayar ta lafiyar Salee, qare musu kallo tayi dukan su uku sannan ta tambaye su wanene mijinta?

Nuna kanshi Sa'eed yayi yace "gani Nan"

" Alhamdulillah matar ka tana cikin qoshin lafiya but I'm sorry to say we lost the baby sakamakon buguwan da tayi yasa cikin zubewa saboda mahaifar ta bayi da qarfi, yanzu dai munyi Mata alluran barci saboda ta samu hutu idan ta farka Zaku iya Shiga ki ganta, excuse me" ta ratsa ta gefen su ta wuce,

Komawa da baya Sa'eed yayi ya zauna dabas a waiting chair hade da dafe kanshi Yana maimaita Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un, he can't believe ya kashe babyn shi da hannun shi mai yasa ya Bari fushi yayi tasiri a kanshi gashi ya raba Saleeha da abinda tafi so a duniyar Nan ya Kuma sake kisan Kai ,

Baisan lokacin da hawaye ya fara zarya a idanun shi ba sai yanzu yaji abinda iyaye sukeji idan sun rasa 'ya'yan su baisan me zai fada was Salee ba idan ta farka,

bai qarasa tunani ba yaji muryan Idris na fadin
"Daman nasan duk Daren dadewa sai hakan ta faru, ba zaka taba canza halinka ba Sa'eed ko yaushe kanka ka sani son zuciyar ka yayi yawa, bansan Mai kake nema ba wannan karon Amman na roqe ka Dan Allah Kar ka cutar da qanwata batayi maka komai ba"

Dagowa jajayen rinannun idanun shi yayi Yana kallon shi, ya ma rasa me zaice mishi,

Sa'ood ne ya amshe da " Dan Allah brother kafin yarinyar na ta farka ka sawwaqe Mata she will be broken if she knows that you murdered her child babu uwar da zata iya yafe wa makashin 'd......"

A tsawace yace " Haba dan Allah wace irin masifa ce? Ku barni naji da Abu daya Mana ki baku san qaddara bane? Kada ku manta wannan babyn nawa ne and I love it!! babu Yanda za'ayi na illata shi" ya harde hannuwan shi alaman roqo "please allow me to breath"

**********

Tunda Sa'ood ya sauqi Leesa take tafiya itama Bata San takamammen inda zata je ba, Kano ba jigawa bane wurare tsirararru ta sani Kuma Bata da ikon zuwa, har akayi sallan azahar akayi la'asar tana zaune a gefen titi ta hade Kai da guiwa tana kuka, mutanen da sukayi tunanin bara takeyi har sun ajiye Mata sadaka suyi tafiyar su,

Ganin idan batayi wani yunquri ba zata iya kwana a Kan titi yasa ta tashi tayi ball da kudin da aka zuba Mata ta Kama hanyar gidan su Ameerah da qafa tana tafiya tana tambayar hanyar da ze kaita unguwar, tasan da with su karbe ta amman Bata da wani zabin zata jure duk wani wulaqancin da zata fiskanta har ta Tara kudin da zata koma jigawa gidan shugaba dan ta saka a ranta ko mutuwa zatayi ba zata koma gida ba,

Tafiya Mai tsayi Mai tarin gajiya Leesa tayi kafin ta Isa dukawa, tafi 20 minutes tsaye qofar gidan su Ameerah tana tunanin irin tarban da zata samu idan ta Shiga da qyar tayi qarfin halin tura qofar ta shige hade da you sallama,

Daga daki maman Ameerah ta amsa hade da tambayansa "wayene?"

Hadiyan wani mugun yawu tayi tace "Haleesa ce"

Da sauri baban Ameerah ya fito ko Riga babu a jikin shi yace "wata Haleesan?"

Tsugunawa tayi cikin girmamawa tace "Ina wuni baba, qawar Ameerah ce"

"Kafin ranki ya bachi ki fita min a gida shegiya Mai baqin qafa, zaman ki a wuri masifa ne kinfi shedan kaidi wallahi, saboda ke har auren 'yata an janye Mun zamo abin zagi da nunawa a gari ko majalisa bani iya zuwa saboda tsegumi ana cewa an dauki 'yata an gama abinda za'ayi da ita kafin aka maido Mana ita, ni dai tskaka ni na dake Allah ya Isa ne kawai Haleesa bazan taba yafe Miki ba shedaniya"

Maman Ameerah tana leqen su ta window tana kuka ganin Haleesa zube a Kan guiwowin ta tana roqon mahaifin Ameerah Allah Annabi ya barta tayi Koda kwana Daya ne Amman yaqi, ita yanzu Haleesa ma tsoro take Bata dan ganin ta da tayi Saida ya tuna Mata ranar da aka shigo har uwar dakin su aka saka musu bindiga su Fadi I da Haleesa take,

Haka baban Ameerah yayi ma Haleesa Koran Kare ya rufe qofa ta Shiga lungun dake gefen gidan ta zauna tana kuka,

**********

Da shigar shi ya samu Salee ta dunqule jikin ta wuri 'daya tana sharban Kuma kaman ranta zai fita, juyawa yayi ya rufe qofar sannan ya qaraso kusa da ita ya zauna,

Ja da baya ta fara yi tana girgiza Kai jikinta na kyarma tace "I'm sorry ya Sa'eed, bazan sake ba please don't hit me Allah bazan sake ba"

Jawota yayi ya rungume ta a jikin shi Yana tsiyayar hawaye "bazan Miki komai ba babe, babu abinda Kika min there is nothing to be sorry for"

"To kace musu su dawo min da baby na, babu abinda ya Sami baby na kawai su dawo min dashi wallahi Dana Bai mutu ba.............🧚

#vote
#share
#comment

Continue Reading

You'll Also Like

33.6K 2.9K 27
အချစ်ရူးနှင့်တော်၀င်ပန်း
102K 9.5K 51
Boddo is a Fulani girl, who will be married at young age of 13yrs to the man who she never knew or saw in her life who is also educated.....how will...
Alina By ihidethisapp

General Fiction

1.5M 37.3K 75
The Lombardi family is the most notorious group in the crime world. They rule both the American and Italian mafias and have many others bowing at the...
Gentle touch By K

General Fiction

49.6K 1.1K 32
It had been mere months after her eighteen birthday, when she was pulled from the safe haven of her life and forced into the fantasy the women had cr...