KAMA DA WANE....(Completed)

By Seemahwrites

13.2K 1.8K 210

even though they look alike that doesn't mean they should have same goals, their life is filled with regret... More

chapter 1
chapter 2
chapter 3
chapter 4
chapter 5
chapter 6
chapter 7
chapter 8
chapter 9
chapter 10
chapter 12
chapter 11
chapter 13
chapter 14
chapter 15
chapter 16
chapter 17
chapter 18
chapter 19
chapter 20
chapter 21
chapter 22
chapter 23
Apology
chapter 24
chapter 25
chapter 26
chapter 27
chapter 29
chapter 30
chapter 31
chapter 32
chapter 33
chapter 34
chapter 35
chapter 36
chapter 37
chapter 38
chapter 39
chapter 40
chapter 41
chapter 42
chapter 43
chapter 44
chapter 45
chapter 46
chapter 47
chapter 48
chapter 49
FINAL
Trailer

chapter 28

244 34 2
By Seemahwrites

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
  🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
                          BATA WANE👩🏻‍🦱
   💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *Na*
        *UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Special gift to *Muhammad Karim*
       *And Fenarh matar Soja*

28👯
Qoqarin bude qofar motan tayi taji shi a rufe, ta juya tana kallon Sa'ood dake kwance jikin seat idanuwan sa a lumshe, kwabe fuska tayi kaman zatayi kuka tace
"Ka bude min na fita Dan Allah"

Still idanun sa a rufe yace "idan Kika fita Ina zakije?"
"Nima ban sani ba kawai ka bude min na fita"

"shhhh please sleep bani son hayaniya'

" Ni wallahi bazan iya kwana a mota ba, yanzu idan safiya tayi mutane suka zo suka ganmu a haka fa"

Tashi yayi ya zauna yace "ok yanzu kin yarda mu tafi Kenan"

Gyada mishi Kai tayi, ya gyara seat dinshi hade da kunna motan yayi reverse suka ci gaba da tafiya, har sun danyi nisa tace "nifa bazan koma wancan gidan ba"

Baice da ita komai ba ya sake reverse ya juya Kan motan suka koma hanyar hotel,
"Wallahi fa ni bazan kwana a hotel ba ka barni na tafi kawai"

A hasale Sa'ood yaja wani wawan burki ya yunquro kaman zai shaqe ta Yana zare Mata manyan idanuwan shi,
"Kinsan Allah zanci Miki mutunci niba bawan ki bane da Zaki dinga juyani Yanda Kika so, ki kalli lokaci 12 harda 'yan kai Amman kin Hana ni barci kin saka ni galantoyi a Kan titi wallahi ki Shiga hankalin ki dani"

Ya sake zugan motan da 'dan iskan gudu suka Kama hanyar gida duk da haka bakin Leesa bai mutu ba sai qananun maganganu takeyi Yana Jin ta Amman Bai ce Mata komai ba, da abun ya ishe shi ne ya dauki kwalin tissue paper ya wurge ta dashi,

"Kai,kai,Kai! Me na maka da zaka ci Zali na?"

"So nakeyi kina maganar da qarfi saboda Ina Jin abinda kike fada"

" Amman ai ban Kira sunan ka ba ko?"
" Kima Kira ki ga Yanda zan dagargaza Miki baki"

Yamutsa fuska tayi cikin qunquni tace "wa ma zai Kira sunan ka, suna babu fasali Wai sakhh...sakhod Allah da nine aka saka min wannan sunan sai na yanka rago na canza"

Girgiza Kai kawai Sa'ood yayi ya fita harqan ta idan ba haka ba yasan Haleesa zata iya maidashi qaramin mahaukaci idan ya biye Mata, suna Shiga cikin gidan ya bada umarni wa Mai gadi ya rufe gate kada ya Bari kowa ya fita sannan yayi parking motan ya fita ya barta a ciki,

**********

Yana zaune a saman gadon ita Kuma ta kifa kanta da jikin gadon tana kuka Mai tsuma zuciya, dago jajeyen idanun ta Nabeela tayi ta kalli Idris shima gaba Daya a dame yake,

"Amor ba na fada maka ba? Duk abinda aka saka Masa Rana indai da Rai sai yazo, gashi yanzu lokacin alqawarin da ka dauka yayi dole ka cika shi, idan wani abun ya same ka ni da yara na bamusan Yaya zamuyi ba, idan ka miqa kanka ga hukuma zamuyi rayuwan qunci da kadaici cikin Mailafiya family,"

" I'm sorry Reina nasan na zalince ku na zalinci twins amman idan nayi confessing abubuwa zasu zo Mana da sauqi zan dawo gare ku very soon Dan nasan idan nayi shiru ma asiri na zai tonu dan Sa'eed bazai bar cin mutuncin da akayi Masa haka ba"

" Nima bazan Bari Kuma kayi ha'inci ba ba Amor, ya Allah kaga halin da muke ciki ka shige Mana gaba"

Sauqowa yayi daga gadon ya daga ta ya kwantar da ita sannan ya ja Mata bargo ya rufe ta
"Kiyi ta min addu'a kawai Reina insha Allah komai zai zo Mana da sauqi go to sleep now"

**********
7:22am

Sun taru a parlo ana breakfast don dining table din gidan bazai dauke su ba, as usual Salee ta tashi da zazzabi shiyasa cin abinci ya gagareta, kowa sai ririta ta yakeyi da safiyan Idris ya fita ya Nemo Mata abinci a waje, Nabeela ma nata special dish din daban tayi Mata ga oga Sa'eed ya zage sai tattala ta yakeyi dan ta samu ta saka wani Abu a cikin ta ya zauna,

Ana cikin haka Leesa ta fito tana binsu da kallon hadarin kaji, kaman Bata so ta gaida su sama_sama suka amsa yaran su ma suka gaishe ta daman Leesa da son girma kaman gyambo ballantana tana ganin wannan zabga zabgan samari da 'yammatan suna gaishe ta Nan ta fara wani Fadi ta koma can gefe ta zauna,

har inda take Nabeela takai Mata breakfast, amsa tayi ta Mata godiya Dan duk cikin su ita kadai ta kwanta Mata a rai ta lura Bata da munafurci kaman Sa'eed kuma Bata da baqin Hali kaman Sa'ood shiyasa take ganin zasuyi mutunci dukda a shekare ta aife ta,

"Haleesa idan kin Gama Yaya Sa'ood yace ki shirya Zaku fita"

Yamutsa fuska tayi tana qare ma fuskar Nabeela kallo tace "waye Kuma Yaya Sa'ood?"

Gaba Daya parlorn Saida suka juyo suna kallon ta dan tambayar da qarfi tayi shi, duk cikin su kuma an rasa Mai Bata amsa dan sun lura abin nata rainin hankali ne,
"Ohh! wannan 'dan ta'addan?, To wallahi ni babu inda zan bishi ban sani ba ma ko siyar dani zaiyi ba"

Cike da takaici Salee tace haba "Leesa me yasa kike irin haka ne? Yayan ki ne fa ni bansan lokacin da kika zamo Mara da'a ba, kwata_kwata yanzu kin canza halayen ki"

" Dakata malama, kada ki sake ce Masa Yaya na idan ke yayanki ne to babu abin da ya hadani dashi, da'a Kuma Wanda na siya da kudi na ya qare su Kuma ba siyamin wani sukayi ba bare nayi amfani dashi"

Duk abinda sukeyi Sa'ood na kallon su baice komai ba, abin na Leesa yanzu ya fara wuce gona da iri shi kanshi shaida ne da halinta ba haka yake ba, don lokacin da suka zauna tare Bata ko yawan surutu ita dai barta da yawan tambaya Amman yanzu duk kunyarta ta ajiye ta dauki wani dabi'ar banza na raina mutane,

Juyawa kawai yayi ya fita breakfast din da baiyi ba Kenan yayi wanka ya shirya sannan ya fito da key din mota a hannun shi ya shigo parlorn gidan, a Yanda ya barta haka yazo ya same ta bata tashin ba ballantana tayi wanka ta shirya,

Qarasawa inda take yayi ya tsaya hade da fadin "ke, tashi mu tafi"

"Dagowa tayi tace " Ina?"

"Muje koma Ina ne Zaki gani"
"Ni bazan je ba"

" Please kada kisa in aikata haramun Dan wallahi idan Baki tashi ba zan daga ki da qarfin tsiya bani son musu"

Tana ture_turen Baki ta tashi tace ya jirata sai tayi wanka,

Tsawon 3 hours Sa'ood ya dauka Yana jira babu Leesa babu alamanta Ashe kwanciyar ta tayi a daki ta Sha barci Saida ya tura Sajida tukunna ta tada ta, yayi niyyan idan bata fito da wuri ba da kanshi zai Shiga ya dauko ta,

Tana fitowa Bai tsaya Bata lokaci ba ya tunkuda qeyar ta suka Shiga mota yaja Basu tsaya ko Ina ba sai asibiti, har sun Shiga reception ya jawo hijab dinta suka fito waje sannan ya nuna ta da yatsa yace

"Na lura kina fama da wani rashin kunya to wallahi kiyi ma kowa Zaki Sha amman idan kikayi ma uwar mu ba zamu barki ba, ki nutsu kisan abinda kikeyi ko Kuma na koya Miki hankali wallahi"

" Sarkin rantsuwa na duniya, yanzu Haka ma ana binka azumin kaffara na kashe wancan mayaudarin Sa'eed din da ka rantse zakayi ku..."

Bata qarasa magana ba ya saka yatsar shi na tsakiya ya dane Mata Baki Saida tayi saurin Kai hannun ta ta rufe wurin tare da runtse Ido tana fitar da sautin cikin azaba,

"Kutt! Mai na maka kake son fasa min Baki? To Allah ya Isa ban yafe ba baqin azzalumi kawai"

Tana kaiwa Nan ta nemi hanyar guduwa yayi saurin take yatsun qafafun ta Yana bin ta da wani kallon cikin Ido,
"Point of correction! Farin azzalumi zakice ba baqi ba, because I believe na fiki haske, wawiya kawai shige mu tafi"

Ya angiza qeyar ta har cikin dakin mamanmu, tana zaune da qur'ani a hannun ta tana karatu cikin muryar ta Mai zaqi irin ta Salee suka shigo, Saida ta Kai Aya sannan ta rufe qur'anin ta dago da murmushi Wanda ya bayyana fararen haqwaranta tana kallon su a tare sunyi matuqar dacewa da juna,

Qarasawa kusa da ita Sa'ood yayi cikin girmamawa ya rusuna sannan ya gaida ta hade da yi Mata Yaya jiki, tana shafa gashin kanshi ta amsa da "lafiya chéri jiki da sauqi sosai"

Leesa kuwa na tsaye a gefe qeqam tana kallon su, ganin irin hararar da Sa'ood yake watsa Mata da Kuma Yanda mahaifiyarta ta ma marairaice fuska hoping that 'yarta zata girmama ta yasa ta Dan rusuna kadan sannan tace
"Ina kwana"

"Lafiya qlau my daughter, if you don't mind inason magana da ke please"

Kafin tayi wani magana Sa'ood yayi saurin miqewa yace
"Bari na 'dan gangara restaurant kafin ku gama Ina Jin yunwa ne sosai cariño"

Dan murmushi ta sake Dan ta Gane nufin sa so yakeyi ya Basu wuri su samu Daman zantawa, tace
" Ba damuwa sai ka dawo"

Yana fita ta nuna ma Leesa kujera "please ki zauna"

Tunda ta zauna ta kasa dago idonta ta kalleta sai Jin muryar ta tayi tana tambayar ta
"Kin taba yin wani Abu da ba dai_dai ba a rayuwar ki? Wanda kike tunanin ya kauce ma Sharia?"

Dagowa Leesa tayi tana kallon ta sannan ta sake sunkuyawa ta Shiga qirgawa da yatsun hannun ta dan bata tunanin zasu qirgu, muryan mama ne ya sake katse ta "a cikin su wanne ne kike tunanin Allah ba zai yafe Miki ba?"

Dagowa tayi tana Mata kallon tunuma a ranta tana kokwanton irin tambayoyin da take Mata, shin tana so ta Sha cikin ta ne ko Kuma tozarta ta takeson yi?

"I'm sorry ba wani abu nake nufi ba, maganar da nake son yi dale Yana da alaqa da wannan tambayar da nayi Miki ne shiyasa"

" Guduwa da nayi daga tsohon gidan mu ba tare da sanin shugaba ba bayan ban cika Mata alqawarin da na dauka na Bata sarqa na idan na samu iyaye na ba, sai Kuma hakkin qawata Ameerah da na Shiga da Kuma kudin Sa'ood da na sata"

" Please Yaya Sa'ood Zaki dinga Kiran shi Kinga ya girme ki kiyi qoqari ki bashi girman shi kinji?"

Gyada Kai tayi mama tace "yauwa tunda Allah bazai yafe Miki wa'innan laifukan ba wa kike tunanin zai yafe Miki su?"

"Wanda na zalinta"

" To Nima haka Allah bazai taba yafemin zalintar ku da nayi ba idan har ba ku kuka yafe min da kanku ba, Saleeha ta Riga ta yafe min please find a place in your heart to forgive me Haleesa,

Duk abubuwan da suka faru ba a son ranmu bane qaddara ce babu Yanda muka iya dole mu rungume ta, Ina sanku sosai, Ina matuqar qaunar ki fiye da rayuwa ta Banga dalilin da zai saka na zubar daku ba,

Ni marainiya ce, na tashi Cikin kadaici sosai daga ku sai mahaifin ku da Kuma yayan ku Idris kuka zamo nawa Wanda duk duniya zan kalla nayi alfaharin kasancewar ku jini na,

An so ku a cikin Mailafiya family tun kafin ku zo duniya, ku masu gata ne gaba da baya, rashin ku kadai a tare da mu ya jawo rugujewar duk wani farinciki da annashuwa a tsakanin mu,

Dan Allah Haleesa kiyi haquri ki zauna tare da mu nayi alqawarin ba Wanda zai takura ki kiyi abinda Baki so but please co-operate mu dawo da walwala cikin familyn mu ni Kuma nayi Miki alqawarin duk abin da kike so zanyi Miki"

Furzar da numfashi Mai zafi tayi tana Jin zuciyar ta Yana sanyi a hankali yanzu Kam tana Jin zata iya haqura ta yafe ma mahaifiyar ta don ta fisu abin tausayi Amman maganarta ta qarshe ya daure Mata Kai,

"Tayaya Kuma hadin Kai na zai dawo da walwala cikin familyn ku?"

"Saboda mahadin dukiyar mu tana jikin ki ke da 'yar uwarki,"

"kaman Yaya?"

" Ki jira Sa'ood chéri ya dawo Zaki ga koma menene"

Babu laifi daga qarshe Leesa ta Dan sake Mata Sun 'dan taba hira dukda yawanci tambayoyi ne Akan Yanda tayi rayuwar ta cikin gidan karuwai tare da Salee, mamanmu Tasha kuka sosai zuciyar ta na tafasa cike da baqin ciki a Haka har Sa'ood ya dawo,

Da qyar suka samu suka lallabata tabar kuka sannan tace ma Sa'ood ya Bata sarqan Salee da tasa ya karbo, miqa Mata yayi ta juya wurin Leesa tace "hadin Kan da Zaki bamu shine sarqan wuyan ki"

Ita dai mamaki ya Kama ta menene amfanin sarqan da suka bi suka damu dashi, tana Bata sarqan ta cire pendant din a jikin chain sannan ta cusa na Salee cikin Ramin na Leesa ta miqa ma Sa'ood,

"Wannan shine makullin vault dake cikin Mailafiya mansion duk wasu Takardu na mallakin dukiya na ciki, password Kuma shine fortune ma'anan Sarwa Kenan da turanci inaso a yau 'dinnan kaje ka fito da su.............🧚

#vote
#share
#comment

Continue Reading

You'll Also Like

5K 442 40
love is a strange feeling but also a very strong connection that will either be your strength or your weakness it all depends on who you've to be wit...
228K 16.8K 21
Avantika Aadish Rajawat Aadi, with his fiery nature, adds intensity and excitement to their relationship, igniting a spark in Avni. Avni, like the ca...
120K 13.2K 32
COMPLETED English/Hausa For someone who has never had it easy in life, Labiba believed her world has finally come to an end when she was practically...
18.6K 2.1K 37
STRANGE LOVE (THE FULANI BRIDE 2)... Yes! It's strange for a thirteen year old girl to find herself tied in marriage with someone she never knew...ho...