KAMA DA WANE....(Completed)

Por Seemahwrites

13.2K 1.8K 210

even though they look alike that doesn't mean they should have same goals, their life is filled with regret... Más

chapter 1
chapter 2
chapter 3
chapter 4
chapter 5
chapter 6
chapter 7
chapter 8
chapter 9
chapter 10
chapter 12
chapter 11
chapter 13
chapter 14
chapter 15
chapter 16
chapter 17
chapter 18
chapter 19
chapter 20
chapter 21
chapter 22
chapter 23
Apology
chapter 25
chapter 26
chapter 27
chapter 28
chapter 29
chapter 30
chapter 31
chapter 32
chapter 33
chapter 34
chapter 35
chapter 36
chapter 37
chapter 38
chapter 39
chapter 40
chapter 41
chapter 42
chapter 43
chapter 44
chapter 45
chapter 46
chapter 47
chapter 48
chapter 49
FINAL
Trailer

chapter 24

220 31 0
Por Seemahwrites

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)
🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
BATA WANE👩🏻‍🦱
💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*Na*
*UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Special gift to *Muhammad Karim*
*And Fenarh matar Soja*

24👯
"Haleesa" ta sake furtawa a hankali tana Jin kaman ba ita tayi maganar ba,

Nurse dake zaune can gefe tana faman chatting ta dago dan tabbatar ma kanta magana taji patient dinsu tanayi, da gudu ta fita ta Kira doctor suka shigo tare a rikice take nuna ta da yatsa
"Doctor wallahi da kunne na naji tayi magana ka qarasa kusa kaji"

" Me kikaji ta fada?"

" Haleesa! Haleesa ta Kira har sau biyu"

Hamdala doctor yayi "finally Allah ya fara kawo Mata sauqi Bayan 17 years ta samu ikon magana wannan labarin Mai dadi dole a sanar da Sa'ood, ya qarasa wurin ta ya dudduba ta saidai taqi sake furta ko kalma daya dukda tana son yin hakan, duk tambayoyin da doctor yayi Mata bai samu amsan su ba saima kawar da kanta gefe da tayi tana tsiyayar hawaye,

A hakade ya qarasa gwaje_gwajen sa ya fita, washe gari da sassafe ya Kira Sa'ood da Idris ya sanar musu abinda ya faru, Sa'ood singlet da three quarter ne kawai a jikinshi ya daura jallabiya a gaggauce ya fito ko Leesa Bata San ya fita ba, Yana Isa asibitin yaga motan Idris alaman ya riga shi zuwa, da sauri ya wuce dakin ta ya hangota kwance kamar ko yaushe ga Idris a gefen ta Yana ta faman magana babu amsa,

Qarasawa yayi ya ture Idris gefe, hannun ta ya riqo cikin nashi ya fara mata magana
"cariño is it true? Dan Allah Nima kiyi min magana naji Ina tsananin son Jin muryar ki, please say something"

Bata kula Sa'ood ba ta fara leqa gefen shi ko zata hango Leesa Amman bata nan, bude bakin ta tayi tana so ta tambaye shi Ina Haleesa Amman maganar ya maqale a maqoshin ta takasa fitar dashi,

Qura ma Sa'ood Ido tayi hawaye na zuba a Idon ta she wished zai iya fahimtar abinda take nema ba tare da da ta furta ba, tana ji a jikinta Leesa 'yarta ce dukda ita kadaice Bata tare da Saleeha Amman tasan she is somewhere around, tana so Sa'eed ya dawo Mata da wancan Haleesan tana so ya fada Mata inda ya samo ta Kuma menene alaqansu but she just can't talk,

Hannun shi yasa Yana share Mata Hawaye "stop crying cariño just speak duk abinda kike buqata zanyi Miki ni buri na kawai kiyi min magana"

Runtse idanuwan ta tayi kukan ta na qara tsananta, hakan ya qara tada hankalin Sa'ood ya juya wurin doctor yace
"Kunce jiya tayi magana Amman yanzu taqi what's happening?"

"Tukunna dai wacece Haleesa? Dan Bayan ta farka sunan da ta Kira Kenan Haleesa,"

" Haleesa 'yarta ce Amman ta 'bata gaskiya bamu san inda take ba yanzu"

" Ok kuzo office dina akwai maganar da zanyi daku" Yana fadar haka ya juya suka bishi a baya,
Basu wuri yayi suka zauna shima ya zauna sannan ya fara kwararo musu bayani,

Ban sani ba ko mafarkin yarinyar tayi ko Kuma wani Abu da ya dangance ta tagani, saboda a binciken da mukayi shock ko anxiety su suka kawo ta samu canji a cikin yanayin ta don cikin halin da take bata buqatar hakan saboda zai iya kawo negative changes instead of positive one's shiyasa ma ba kasafai muke Bari ana ziyartan ta ba saboda hakan dole mubi komai a sannu saboda mu samu ta warke kada aikin mu ya dawo sabo"

" Ban gane ba doctor Amman jiya da ka Kira mu cewa kayi maganar ta ya dawo yanzu Kuma kana son canza magana?" Cewar Idris

" Please understand, da ace da tayi na farko taci gaba da magana normally ne I can guarantee you sauqi ya samu Amman kaman Yanda na fada wannan ba komai bane illa sign na distress, yanxu abin da nake so daku kudan dauke qafa ku daina zuwa gurin ta sosai insha Allah mu Kuma zamuyi qoqari wajen ganin muryar ta ya dawo tunda yanzu muna da yaqinin zata iya magana"

Sa'ood dai bai ce komai ba ya tashi ya fita daga office din ya koma dakin ta, tsungunawa yayi a Kan guiwowin shi sannan ya hada hannuwan shi hawaye na zuba a idanun shi,

"Kin yarda dani Amman na ruguza wannan yardan cariño, duk Daman da Kika bani na watsar dasu ban jajirce wurin neman Sarwa ba da tuntuni na same su tunda nasan ba zasu tsallake Nigeria ba, nayi alqawari cariño in Allah ya yarda a cikin watan Nan ba Haleesa kadai ba harda Saleeha zan hada na kawo Miki su nidai buri na kawai ki samu lafiya please,"

**********
Share hawayen dake idanun ta tayi ta matso kusa dashi ta riqo hannun sa da yake gyara button din rigan shi dashi tace
"Miel wallahi inajin tsoro, bansan me zai faru ba idan Ya Sa'ood ya samu labarin kaje wurin baba alhaji zai iya cutar da Kai tunda ya dau alwashin hakan"

"ki kwantar da hankalin ki insha Allah babu abinda zai faru, ya zamo min dole na kawo qarshen qiyayyan dake tsakanin mu kafin ya shafi rayuwar yaran mu, zanje in fada mishi Sarwa nake aure nasan idan shine yayi magana ma Sa'ood zai iya ajiye makaman yaqin shi"

" Amman duk credentials Dinka na wurin Sa'ood ta Yaya zaka iya tafiya babu passport babu Visa?"

" Don't worry mi Alma, tunda na Shiga wannan yanayin ban taba neman taimakon wani ba Koda kuwa 'yan uwana ne amman wannan karon Ina da Wanda zan nemi taimakon su, zan karbi aron kudade a wurin su, su zasu tsare bayanai na da zuwa wurin Sa'ood and I surely will get a new passport, ko kin manta lokacin baya muke da garin ne? Kuma Nan da kawa 4 zuwa 5 zan Isa wurin baba alhaji komai zai dawo Kaman ba'ayi ba, just trust me,

Sannan ki tuna amanar Saleeha na baki idan wani Abu ya same ta matsalolin mu ba zasu taba qarewa ba, zamanta lafiya shine komawar mu cikin Mailafiya family shine dawowar matsayin mu da dukiyar mu kaman yanda kike mafarki, kimun addu'an sa'a sai na dawo Miki da labari Mai Dadi"

Qarasa gyara zaman rigan shi yayi ya dauki Jakarsa ya rataya sannan ya fita zarah ta bishi da kuka, ita tasan muddin Sa'ood yasan Sa'eed ya tafi Mexico tofa saide wani ba Shiba,

Yana fita yaci Karo da Salee ta jingina da qofar dakin ta tana riqe da hannun Islam kallo Daya yayi Mata yasan hankalin ta bayi jikinta 'to tunanin me takeyi?' ya tambayi kanshi,

Qarasawa kusa da ita yayi ya 'dan taba ta kadan, firgigit tayi ta dago tana kallon shi lokaci daya tana sakin murmushi,
"Har ka fito?"

Gyada Kai yayi yace
"Eh zan wuce sai Allah ya qaddara saduwan mu"

" To Allah tsare ya kiyaye hanya Amman idan kaje kanon kwanaki nawa zakayi?"

" Bazai wuce 6 ba insha Allah sannan idan zan dawo zan zo Miki da labari Mai dadi zakiyi farinciki sosai, kuyi tamin addu'a har naje na dawo sannan ki kulamin da kanki please inaso Inga canji a yanayin ki saboda mutanen da zan kaisu wurin ki suji dadin ganin ki"

"Wasu mutane Kenan dadyn al'amin?"

"murmushi ya sake Mata yace idan na dawo zakisan koma suwaye, na tafi bani son nayi dare a hanya"

Har qofa sukayi mishi rakiya suna mishi Allah ya kiyaye, ya musu peck a cheeks sannan ya wuce,

Zarah kuwa Bata iya fita ba sai kulle kanta tayi a dakin ta tana kuka Mai ban tausayi fargaba da tsoro Kashi biyu sun mamaye zuciyan ta, idan Sa'eed Bai ci nasara ba tana tsoron abun da Sa'ood zai iya mishi, idan Kuma yaci nasara tana tsoron rayuwar da zata Shiga Nan gaba a Mailafiya family saboda Sarwa,

**********

Kwanaki sun ja, yau kwana 14 da tafiyan Sa'eed Amman har yanzu Bai dawo ba, saboda tsaiko da ya samu don abubuwa basu zo Masa da sauqi Yanda yayi tsammani ba, saidai alhamdulillah ya samu ganin baba alhaji Kuma yayi Masa bayani sosai Yanda ya fahimce shi,

Daman tun asali shi ba Mai kafiya da matsa ma yara bane shiyasa ya amince zai sasanta tsakanin shi da Sa'ood, Amman yace ya Bari sai ya Gama abinda yake yi su dawo tare,

Dukda Sa'eed na matuqar dame Kan rashin lafiyar Salee Amman haka ya zauna don maslahan da yake nema yanzu yafi Masa komai,

Yana qoqari kullum ya Kira Zarah ya fada Mata halin da ake ciki, Kuma babu laifi tana kula da Salee iyakar iyawanta kamar Yanda tayi alqawari, itama kullum Zarah tana Bata wayar su gaisa duk a tunanin ta Yana Kano ne dan Bata taba riqe waya ba ballantana ta banbance international number,

Bangaren Sa'ood kuwa Garba TK ya tattare su sun tafi Lagos Dan shirye_shirye da training da zasuyi kafin su fita operation, ya bar Leesa ita kadai a cikin gidan sai yaran sa dake faman Mata hidima,

Ba qaramin dadin tafiyan shi Leesa taji ba don yanzu ta samu Daman da ta dade tana nema zata samu hanyar tserewa cikin sauqi taje ta dauki Salee su tafi,

Tun washe garin tafiyar Sa'ood taje ta tattara komai da ya dangance shi da familyn su gaba daya, tun daga Kan family picture, picturen Shi dashi da Sa'eed, ID cards, passport,birth certificate, indigent, da duk wani Abu da ya dangance shi harda na Sa'eed da ta gani a dakin shi ta saka cikin jakan kayan ta,

Sannan ta bude drawern da yake ajiye bindigogi ta dauki daya qarama ta saka bullets ta jefa a jaka, tana cikin tattare kayan ta taga kudi masu yawa da ya ajiye bundles na dubu_dubu, da kaman ba zata dauka ba Amman Dole tana buqatar kudin mota da na abinci kafin suyi settling a wurin da zasu sauqa Kuma Bata da damar komawa gidan alhaji Habib ta dauko jakar ta shiyasa kawai tayi shahada ta dauki 20k a ciki,

Dare nayi ta saiti hanyar guduwa Amman ba kaman Yanda tayi tsammani ba ko Ina na cikin gidan a rufe yake harda dakin da ta dauko ladder rannan, Haka ta koma ta cigaba da zama kullum sai Sa'ood ya Kira waya an Bata yaji lafiyar ta Kuma kullum sai tayi yunqurin guduwa babu nasara,

Sa'ood ya saye Rabin yaran Garba TK da kudin shi da yake sata ba tare da sanin shi ba, saidai ya rasa Yanda zaiyi ya qaddamar da qudurin shi kafin ranar da zasu salwantar da dubban mutane ya cika, dole idan ya kashe TK bazai samu Daman tserewa lafiya ba idan Kuma hakan ta faru Yaya batun alqawarin da ya dauka ma mamanmu?,

Iya yarda ya samu Garba ya yarda dashi a yanzu babu Wanda ya fishi kusanci dashi shiyasa yayi amfani da wannan Daman tun sauran kwana 4 tafiyar su ya fara poisoning dinshi da guba Mai kisa a hankali, a sannu yake bin jinin jikin Shi Yana raunata shi tun Yana iya tsayuwa har ya dawo zama daga qarshe Kuma sai kwanciya,

Lokacin da ya tura Sa'ood ya dauko likita yaje ya samo wani abokin su cikin tsoffin doctors din Mailafiya hospital Wanda a Kan idon su aka kashe dady Aliyyu, a maimakon ya duba shi sai yayi wasu 'yan dibi dibi ya qara Masa alluran guba sannan ya basu fake results Kan cewa hawan jini ne ya hadu mishi da diabetes,

Cikin kwana 2 Garba TK ya Gama rikirkicewa numfashi ma kaman a karba ayi mishi,da dare yayi yasa aka Kira Sa'ood zai mishi wasiyya ya jagoranci tawagar shi dan Yanda take Jin jikin shi Yana tunanin baze Kai gobe ba,

Ran Sa'ood fari qall ya Shiga dakin da TK yake kwance ya Danna ma dakin kwado sannan ya jawo stool ya daura qafar shi 'daya yana qare mishi kallo da 'dan qaramin murmushi a Kan fuskar shi,

Garba ya bude Baki zai fara magana yayi saurin dakatar dashi
"Wait!!wait! You know kwata_kwata banji dadin ganin ka cikin wannan yanayin ba saboda ba haka na so ba, naso na ganka cikin jini na kashe ka na farka cikin ka kayi irin mutuwar wulaqacin da yafi na dady Aliyyu"

Murya na rawa TK yace " wa...wa...waye..k..Kai"

"Kada ka damu da sani na don tun asali baka sanni ba, Amman kasan doctor Aliyyu, Mailafiya hospital, 23rd April, ranar da kuka je kukayi tabargazan da ya rusa Kan iyalin mu gaba daya randa ka rasa mushen mahaifin ka Tukur,

Cikakken sunana Sa'ood khalifa Mailafiya, ni qani ne wurin Dr Sa'eed kuma 'da wurin Dr Aliyyu Wanda sukayi ma mahaifin ka aiki a wannan Rana"

Sauqe numfashi yayi, ya gyara tsayuwar shi yana zaga tsakiyar dakin sannan yaci gaba da magana,

"Nasan zakayi mamaki Amman Ina Nan lokacin da hakan ta faru na Kai qanne na twins vaccination na measles da yellow fever, Bayan an Gama musu ne mukaje office din mahaifin su Dr Aliyyu muka zauna har qanina Sa'eed ya same mu a wurin muka zauna aka ci gaba da Hira,

Har Saida aka Kira sallan la'asar kafin muka badasu ma nurse mukaje masallaci, dawowar mu Bada dadewa ba mukaji qaran harbi lokaci daya yanayin asibitin ya canza, daddy Aliyyu da Sa'eed suka fita duba abin da yake faruwa ni Kuma na zauna tare da twins,

Daga fitar su suka samu Kun shigo da mahaifin ka cikin jini ka miqa ma daddy Aliyyu shi kace Dole yayi Rai ko ka kashe likitocin asibitin gaba daya, tsoro ya Kama Sa'eed sosai musamman da yaji Kun kashe guards kafin ku shigo shiyasa ma Bai qarasa wurin ku ba Amman da kallo 'daya zakayi min kaga tsananin Kama da muke dashi,

Daddy Aliyyu Bai 'bata lokaci ba ya Shiga da mahaifin ka theatre room suka fara qoqarin Yanda zasu ceto rayuwar shi harda 'dan uwana Sa'eed da Kuna wasu doctors guda biyu da nurses,

Bansan Yaya akayi ba saboda rudewa Sa'eed ya canza alluran da za'ayi ma mahaifinka yayi mishi Wanda yasa jinin sa tsinkewa unfortunately ya mutu a lokacin, Sa'eed ya Shiga tsananin firgicin da ya wuce misali har idanun shi sun fara hango mishi irin mutuwar da zaiyi idan kasan shine sanadin mutuwar tukur shiyasa dady Aliyyu yayi kasadan sanar maka cewa ba'ayi nasara ba Kuma ya umarci doctors din su fita ta dayan qofar dake ta baya,

sannan yace duk Yanda za'ayi mu fitar da Sarwa daga asibitin kada mu kaisu gida saboda munsan zaka iya binmu har can ka tada rigima ba tare da Mun shirya ba, akwai wata tsohuwar care taker dake aiki a orphanage Wanda itace ta raini mahaifiyar su, sai yace a kaisu wurin ta a qauye daga baya zai je ya dauko su,

Sa'eed na fita yazo wurina yace na bashi su ya fita dasu ni kuma naqi dan ko kadan bani son abinda zai taba Sarwa inajin su har cikin zuciyata, takurawa yayi na barshi ya tafi da su a cewar shi ta fire exit zai fitar dasu................🧚

#vote
#share
#comment

Seguir leyendo

También te gustarán

Alina Por ihidethisapp

Ficción General

1.5M 37.3K 75
The Lombardi family is the most notorious group in the crime world. They rule both the American and Italian mafias and have many others bowing at the...
448K 32.1K 43
ပဲပြုတ်သည်ငပြူးနဲ့ ဆိုက်ကားဆရာငလူးတို့ရဲ့ story လေးတစ်ပုဒ်
18.6K 2.1K 37
STRANGE LOVE (THE FULANI BRIDE 2)... Yes! It's strange for a thirteen year old girl to find herself tied in marriage with someone she never knew...ho...
8.6K 975 10
The heart is a confusing, altering thing no state of bliss lasts forever and no state of pain does either. A nice easy going girl, a temperamental a...