KAMA DA WANE....(Completed)

By Seemahwrites

13.2K 1.8K 210

even though they look alike that doesn't mean they should have same goals, their life is filled with regret... More

chapter 1
chapter 2
chapter 3
chapter 4
chapter 5
chapter 6
chapter 7
chapter 8
chapter 9
chapter 10
chapter 12
chapter 11
chapter 13
chapter 14
chapter 15
chapter 16
chapter 17
chapter 18
chapter 20
chapter 21
chapter 22
chapter 23
Apology
chapter 24
chapter 25
chapter 26
chapter 27
chapter 28
chapter 29
chapter 30
chapter 31
chapter 32
chapter 33
chapter 34
chapter 35
chapter 36
chapter 37
chapter 38
chapter 39
chapter 40
chapter 41
chapter 42
chapter 43
chapter 44
chapter 45
chapter 46
chapter 47
chapter 48
chapter 49
FINAL
Trailer

chapter 19

237 32 0
By Seemahwrites

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)
🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
BATA WANE👩🏻‍🦱
💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*Na*
*UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Special gift to *Muhammad Karim*
*And Fenarh matar Soja*

19👯

Shigewar ta dakin shi tayi ta dudduba har cikin toilet wayam babu shi babu alamun shi ta fito sai faman tura Baki takeyi, ta qarasa wurin momy taja kujera ta zauna tayi shiruu dan tana 'danjin nauyin tambayar ta inda Sa'ood yake,

Murmushi momy tayi tace 'yammata babu gaisuwa ne? Ko dan baki samu mutumin naki bane kike fushi damu?

Murmushin Yaqe tayi tace "good morning momy"

"Morning my dear kin tashi lafiya"

A taqaice ta amsa da " Qlau, Dan Allah Ina ya Sa'ood ya Shiga ne? Na Shiga wurin shi ban same ba"

"Yanzun Nan ya fita ki duba wurin mamanku ko Zaki same shi"

Ai ko 2 minutes Bata qara ba ta fita ta saka a ranta yau idan ba kabari ya Shiga ba sai ya tsaya ya saurare ta dan tun shekaran Jiya yake Mata wasa da hankali sai yace ta jira shi Bari yana zuwa, to haka zata qaraci zamanta har ta gaji Bai zo din ba,

Saida Sa'eed yayi wanka ya shirya fess cikin army green suit sannan suka fito tare da Zarah Yana baza qamshi, parlor suka fita momy tayi Masa Allah ya Sanya albarka tayi Masa addu'an NASARA Akan aikin da zai fara dan yau zai fara Shiga office dinshi a asibiti,

Har mota Zarah ta mishi rakiya da kayan barcin ta ba tare da lullubi ba, ya Shiga passenger seat ya zauna Yana jiran zuwan Sa'ood su tafi,

Da qyar ya samu Sumayya ta rabu dashi ya fito, ya barta a part din mamanmu sai kuka takeyi Dan Kai tsaye Bayan ta Gama zazzage masa sirrin cikin ta yace shi bayi ciki,

Yana hango Zarah a jikin motar ya daure fuska kaman tunda yake a duniya Bai taba dariya ba, ya qarasa wurin da take tsaye suna magana da Sa'eed yace "Kee"

Da sauri ta juyo tana kallon shi
"Good morning ya Sa'ood" ta fada cikin sanyin murya,

" Kin wuce ciki ne ko saina tattaka ki a Nan wurin!"

Sidin_sidin Zarah ta wuce ciki don mugun tsoron shi takeyi, ta rasa Yaya akayi halinsu ya banbanta da Sa'eed dinta gashi kaman su daya Amman yanayi da halin kowa daban daban, tabbas KAMA DA WANE BATA WANE don tsauri irin na Sa'ood kaman wani qanin mala'ika,

ta kusan shigewa ya daga murya yace "Kuma na dawo na same ki da shigan arna kiga Yanda zanyi dake"

Zagawa yayi ya Shiga driver seat sannan ya tada motan aka wangale musu tangamemen gate din ya zugi motan da gudu, sunyi nisa da tafiya Sa'eed ya juyo Yana kallon kayan jikin shi,

Yana sanye da v neck shirt da jeans ya sha facing cap kunnen shi toshe da earpiece, zare daya Sa'eed yayi Yanda zai jishi da kyau yayi saurin mayarwa, bayi son Jin mitan Sa'eed yasan maganar Daya ce he doesn't look presentable,

Sake cire Masa yayi yace "jiya fa Saida aka maka magana ka saka Kaya masu ma'ana idan zamu je asibitin Nan, you have to look like a honourable person a true Mailafiya, kana matsayin babban magaji Amman kana Shiga irin na almajirai gaskiya baka kyauta min kwata_kwata, wani lokaci sai naji kaman na bare fuskar ka na saka maka wani daban saboda idan ka kwafsa nace banma San ka ba"

Cikin basarwa Sa'ood yace " Allah ko? Hakan nada kyau"

"Seriously brother ka daina irin wannan halin da ka dauka Bai dace da Kai ba kwata_kwata, Allah yayi maka baiwa da yawa, kyau, aji, kudi, Amman duk kaqi amfani dasu,

kaje party ka kwashi 'yammata ka kashe musu kudi su biya maka buqata, bance ka Sha giya ba ko kayan maye dan Nima bani Sha Amman kaji dadin duniya, kayi yarinta ma nutsuwa ka Bari idan ka girma ka haifi yara sai ka koma salihi saboda makomar rayuwar yaranka"

Murmushin gefen Baki Sa'ood yayi yace "saboda kada a 'bata min su ko? Amman ka taba tunani su yaran da kake qoqarin saka ni na lalata suma suna da iyaye kuma suna son su, abinda kake yi fa babban laifi ne wurin Allah shi yake jawo yawaitan zinace_zinace Wanda suna daga cikin manyan laifuka da Allah ya haramta Kuma yake fushi da me aikata su kaima yanzu bani da tabbacin baka taba aikatawa ba ,

Sa'eed please for once ka zauna kayi tunani ka tsara rayuwar ka Kan tafarkin addini Kan koyarwan manzon Allah (s.a.w) ka Kuma nema ma 'ya'yan ka uwa ta gari Dan wallahi Zarah ba matar aure bace kaji na fada maka,"

Da mamaki yake kallon shi,
" Ban gane Zarah ba matar aure bace, Idan ba ita ba wa kake so na aura? Ita din fa 'yar uwata ce and she is beautiful and classy nifa bazan iya auren macen da Bata iya soyayya ba bazata tarairaye ni kaman kwai ba, inason macen da zata kashe min lokacin ta tayi min duk abinda nake so Kuma ta nuna min so a Koda yaushe kaga Kuma Zarah tun yanzu ta gwada hakan"

"Kuma a Haka kake cewa tana da class? Ina wani class a Nan! Ka taba zama kayi tunani da maza nawa tayi wa wannan abun bayan Kai? Zarah ba sonka takeyi ba fa, my brother she is after your money! kudi kawai take so daga zaran ba kudi ba soyayya"

Tabe Baki Sa'eed yayi shi kwata_kwata wannan wa'azin yawan na Sa'ood ba dauka yake yi ba, shi yasan bayi son Zarah Amman bayi da macen da zai aura da yawuce ta, idan ta zamo matar shi tana Shiga ta alfarma ta rangada kwalliya ya dauke ta a gaban mota suna ratsa tsakanin abokai duk inda suka Shiga hankalin mutane ya dawo kansu shine zaisan yayi aure, Kuma Allah ya Basu rayuwa Mai yalwa ne don su more ta suji dadin su badan komai ba,

Har suka Isa asibiti Sa'eed Bai sake cewa komai ba ya bar Sa'ood sai zuba yake yi kaman kurna,

Basu dade da zuwa ba aka tara meeting na doctors din asibitin gaba Daya aka gabatar musu da Sa'eed a matsayin sabon likita sannan wata nurse kaishi office dinshi, suna gaba Sa'ood na binsu a baya, da shigar su office Sa'eed ya saka hannun shi Bayan qugun ta ya jawota jikin shi, Yana binta da wani mayen kallo,

"Hey beautiful! gaskiya bakiyi ma wata adalci ba da Kika fishi haskawa I've never seen any girl as beautiful as you are"

Murmushi nurse din tayi yau Kam kakanta ta yanke sa'a doctor Sa'eed is flirting with her, ta bude Baki zatayi magana sukaji muryan Sa'ood ta bayan su Yana fadin
"Ke zo ki fita"

Saketa Sa'eed yayi ta ratsa ta gefen shi ta fita, ya rufe qofar sannan ya ja kujera daya ya zauna,
"Wato Sa'eed duk abinda za'a fada maka Kai baka ji ko? Shikkenan wallahi sai ka gani a qwaryan cin tuwon ka, na tabbatar maka sai kayi nadama sai kayi dana sani wata Rana zaka ciza yatsa a Kan abun da kakeyi, maybe a lokacin bani tare da Kai Amman na tabbatar sai ka tuna da wannan maganar" Yana gama fadan haka ya tashi ya fita,

cikin satin Sa'eed yayi ma dady Aliyyu magana Kan zancen auren shi da zarah ba tare da wani Bata lokaci ba suka je aka you magana da iyayen ta suka Kai goro da sadaki aka saka rana Nan da watanni 3,

Rawan Kai a wurin zarah kuwa ba'a magana Kaman zata auri wani 'dan shugaban qasa Haka take ji, duk ranar Friday da dare sai sunyi bachelor's party Wanda Sa'eed da kanshi ke daukan nauyi, aje a girgije a aikata ko wani irin alfasha sai tsakar dare kowa ya koma gida,

Sunday
1:39pm

Gaba daya familyn an taru a parlon momy ana kallon kayan zarah akwatuna 24 Wanda za'a Kai da yamma, Sa'eed na zaune jikin hajiya suna ta faman tsokanar shi, Sa'ood Kuma na can gefe riqe da sajida first born din Nabeela Wanda itama a gidan marayun Idris yaje ya aurota,

Bayan sun gama ganin kayan aka tattara su aka saka su a mota kowa ya watse ya rage sauran mutane kadan a parlon Sa'ood na ganin haka ya miqa ma Nabeela babyn ta zai fita kaman daga sama Sumayya ta Fado a gaban shi ta fara kame_kame "umm...amm..y..Yaya Sa'ood nace yaushe ne za'ayi namu? Naga har yanzu baka ce komai ba"

Zaro idanu yayi kaman Wanda akayi Masa sharri yace "namu mene??"
"aure Mana"

Jinjina Kai yayi yace "to jirani Ina zuwa yanzun Nan" kafin tace mene ya saka Kai da sauri ya fice, part din mamanmu ya nufa ya same ta zaune tana Shan fruit salad da tsohon cikin ta qatoto.

Bai Bata lokaci ba ya dauko spoon ya saka a ciki ya cigaba da Loma, yana qananun mita, murmushi tayi tana kallon shi tace

"Sa'ood Chéri har yanzu gudun 'yammata kake yi?"

" Nifa ba gudun su nake yi ba cariña sun cika takuri ne wallahi kaman wasu qudaje subi su ishi mutum ko Dan class din Nan na big girls Basu dashi"

" To haka zakayi ta zama babu aure? Yanzu fa qanin ka auren shi sauran wata biyu da sati uku Amman Kai ko budurwa baka tsayar ba"

Cika bakin sa yayi da fruits Yana fadin
" share Sa'eed Dan wahala ne shi, ni 'yarki nake so na aura, ko babu komai zata dauko qualities dinki Kuma duk Mai halinki wallahi ta Dace duniya da lahira idan har kin amince idan Kika aifi 'ya mace Zaki bani ni Kuma nayi Miki alqawarin ita kadai zan aura, Bayan ita babu qari"

Murmushin Jin Dadi mamanmu tayi tace
" To idan ba kyakkyawa na aifa ba fa? Yaya za'ayi ta zamo matar prince charming dina?"

" I don't care, ko ita tafi kowace 'ya mace Muni a duniya a haka na gani nake so saidai idan za'ayi min rowa"

" Duk abinda nake dashi naka ne 'dana na baka ita halak malak Kai kadai ne mijin baby na, I'm so proud to have you as my son in-law.

Tashi yayi yana rufe fuskan shi da hulan hoody din jikin shi a dole Yana Jin kunyan ta, ya wuce dakin shi na part dinta ta bishi da kallo tana dariya, inama ace Yan matan dake binshi dasu zo suga abinda yake yi da wasu sai sun buga qasa sun rantse wannan ba Sa'ood bane.

Kwanciya yayi rigingine Yana lissafi, yanzu tunda an bashi Mata dole ya fara aiki dan ya ciyar da ita yayi Mata hidima da gumin shi, Yana so ya dauke ma iyayen ta dukkan dawainiyar ta tun daga ranar aihuwar ta har zuwa lokacin da zata cika shekarun da ya Kamata suyi aure,

To yanzu idan ba mace ta aifa ba fa? Haka zakayi ta zaman jira har sai ta sake aihuwa? Kuma likita yace ba Nan kusa ba maybe wannan ne aihuwan ta na qarshe a duniya ma, yaya zakayi Kenan? wani bari na zuciyar shi ya tambaye shi "no no no stay positive Sa'ood insha Allah mace zata aifa kawai kaje ka fara Shirin tarban amaryan ka" girgiza Kai yayi ya tashi ya fita dan yanzu baiga ta zama ba,

Cikin hukuncin Allah Bayan sati biyu mamanmu ta aihu ta samu 'yan biyu duka Mata, kada kuga murna wurin Sa'ood, farin cikin shi ya gaza boyuwa bakin shi har kunne, ya kasa ya tsare ya Hana kowa daukan su Wai bayi so a jagwalgwala mishi Mata basuyi qwari ba tukunna, babu Yanda suka iya saidai subi yaran da Ido suna San barka,

Tunda aka sallame su ya kasa samun sukunin zama shine wannan shine wancan harta diapers da aka saka ma yaran shi ya siya da kudin shi yace Bai yarda daddy Aliyyu yayi komai ba ya dauke mishi duk dawainiyar su,

Ranar suna akwati uku_uku yayi ma yara na uwar su Kuma guda biyu, yara sunci suna Haleesa da Saleeha, kowa Saida yayi mamakin rawar qafa irin na Sa'ood, tun daga lokacin ya dawo Mai raino Haka zai dauki yaran duka ya goya daya ya riqe daya Yana jijjiga su har suyi barci,

Idan sun bata jikin su ba tare da yaji qyama ba zai goge su ya sauya musu wani diapers ya Basu Madara, Haka ko office zaije idan ya Gama shiryawa zai tattare su har mota sai ze tafi tukunna nannyn su ta dawo dasu,

Komai Yana tafiya dai_dai a Mailafiya family twins nada watanni 2 da sati 1 aka daura auren Zarah da Sa'eed, ranar da aka saka ma twins Sarwa baba alhaji yasa akayi musu wasu sarqan gold na musamman Bayan shi da Hafsat sai Kuma Aliyyu babu Wanda yasan amfanin sarqan,

Zarah da Sa'eed suna zaman su lafiya qlau Banda harqan gayu da Jin dadin rayuwa babu abinda suka sa gaba Amman hakan bashi ya Hana shi bin 'yammatan waje ba domin abun ya riga yabi jikin shi,

Idris da iyalan shi da baba alhaji Kuma sun koma Mexico saboda rashin lafiyar da hajiya take fama dashi, bangaren mamanmu kuwa ta Shiga damuwa sosai da ta gano abun da dady aliyyu da Sa'eed suke aikatawa a asibiti, sun kafa babban center na abortion Wanda a kowani Rana ana barar da ciki na Mata 20 ko fiye da Haka,

Tayi Imani cewa Wannan shine musabbabin duk matsalolin da suke ciki na rashin aihuwa akai_akai Kuma tana tsoron wanda zasu iya Shiga a gaba dan tasan Allah bazai barsu haka ba tunda suka kasance cikin masu Saba mishi,

Tayi kuka, tayi wa'azi, tayi Magiya duk a banza idan ta matsa da magana amsa daya yake bata, shi ba kisan Kai yake yi ba tunda bashi yake jawo su dole ba, ra'ayin kansu yake kawo su shi aikin kudi kawai yakeyi,

Idan ta tuhumi Sa'eed shima maganar daya ne Dana daddy Aliyyu, aikin kudi sukeyi, ranar da twins suka cika watanni 9 a duniya iyayen su sukayi wani gagarumin fada Wanda yasa mamanmu neman saki daga wurin shi,

Fitowa yayi daga bedroom tana biye dashi a baya fuskar ta sharqaf da hawaye ta jawo riganshi cikin bacin rai ta fara magana
"Idan kana qaunar iyayenka ka rabu da ni Aliyyu, na daina hada ka da Allah tunda nasan ba tsoron shi kake ji ba wallahi inaji maka tsoron kamuwan shi bazakuji da dadi ba, ni bazanci gaba da zama da makashi ba idan Kuma kaqi saki na zan tafi na maka ka a kotu a rabamu ta qarfi"

Kama hannun da ta riqe shi dashi yayi, yana kallon Yanda tayi kicin_kicin ta bata rai,
"Hafsat me yasa Kika zama fitinanniya ne? Yanzu fa ke ba qaramar yarinya bace tun da Baki tsiro da wannan halayyan ba sai yanzu? Kina maganar rabuwa da jika fa a tsakanin mu ba ma 'ya'ya ba, idan kin tafi yanzu ma Baki da wurin zuwa Baki da kowa a duniyar Nan bayan ni, ni kadai ne gatan ki"

" Qarya kakeyi wallahi bani da wani gata a duniyar nan Bayan Allah, kullum Banda gori babu abin da nake samu daga wurin ka, jiya kadai Saida kuka sa iyaye biyu suka rayuwar su da abinda ke cikin su me zaku ce ma Allah ranar qiyama? Kun manta cewa akwai hisabi? Ko Kuna tunanin duk rayukan da kuka salwantar Allah zai manta yawan su ne? A matsayin ka na uba wurin Sa'eed Kai ya Kamata ka Hana shi Amma Kai kake mishi jagora kuji tsoron Allah fah!"

Bai sake ce Mata komai ba ya fita a zuciye ya Shiga mota driver ya ja suka wuce asibiti, Sa'ood na Shiga dakin ta da Salee a kafadar shi ya samu tana zaune ta zabga uban tagumi yanzu kukan ma ya gagara zuwa, tana ganin shi ta fara qoqarin boye damuwar ta tana faman murmushin Yaqe,

Kallon ta yayi a kaikaice yace "cariña me ya faru?"

Murmushi tayi tace "babu komai Sa'ood Chéri ta dame ka kuka ko?"

" No zamuje vaccine ne a shirya su sai a bani katin su mu tafi"

Karban Salee tayi ta Shiga da ita dakin su aka shirya su ta fito dasu ta bashi suka tafi,
________________

Tun daga wannan fitar ne daddy Aliyyu Bai sake dawowa ba sai gawan shi aka maida gida cikin jini anyi Masa kisan gilla kisan wulaqanci Sarwa ma ba'a sake ganin su ba har yau niman su muke tsawon shekaru 17 kenan Amman har yau babu labari gani na dasu na qarshe a Mailafiya hospital ne nayi iya bakin qoqarina na Nemo su Amman hakan Bai faru ba,

Gyara zama Leesa tayi dan ita labarin ba wani 'da'data da qasa yayi ba, qara tsanar iyayen ta da Mailafiya family gaba daya tayi, suna da arziqi da mutunci Amman suka zubar da ita da 'yar uwar ta kamar marasa gata? Ita a tunanin ta su shegu be shiyasa aka ya dasu Amman Ashe ba haka abun yake ba,

Bayan haka sai me ya faru? Bata yaran sukayi ko sace su akayi? Ita mahaifiyar su tana Ina Bata neme su da kanta ba? Waye ya kashe mahaifin sun?...............🧚

_kuyi haquri matsalan wuta muka samu Amman zuwa gobe zaku jini insha Allah_

Continue Reading

You'll Also Like

Alina By ihidethisapp

General Fiction

1.5M 37.3K 75
The Lombardi family is the most notorious group in the crime world. They rule both the American and Italian mafias and have many others bowing at the...
593K 27.1K 42
Needs editing [ the destiny series #1] 𝑻𝒉𝒆 𝒇𝒂𝒕𝒆 𝒑𝒖𝒔𝒉𝒆𝒅 π’•π’‰π’†π’Ž 𝒂𝒑𝒂𝒓𝒕 𝒃𝒖𝒕 π’…π’†π’”π’•π’Šπ’π’š π’‚π’ˆπ’‚π’Šπ’ 𝒑𝒖𝒍𝒍𝒆𝒅 π’•π’‰π’†π’Ž π’•π’π’ˆ...
1.6K 148 28
Ayzar hisham Alee a man who doesn't believe in love again was ordered to marry an ordinary girl. Najma khaleel a lady with good values. She is loving...
5K 442 40
love is a strange feeling but also a very strong connection that will either be your strength or your weakness it all depends on who you've to be wit...