KAMA DA WANE....(Completed)

Por Seemahwrites

13.2K 1.8K 210

even though they look alike that doesn't mean they should have same goals, their life is filled with regret... M谩s

chapter 1
chapter 2
chapter 3
chapter 4
chapter 5
chapter 6
chapter 7
chapter 8
chapter 10
chapter 12
chapter 11
chapter 13
chapter 14
chapter 15
chapter 16
chapter 17
chapter 18
chapter 19
chapter 20
chapter 21
chapter 22
chapter 23
Apology
chapter 24
chapter 25
chapter 26
chapter 27
chapter 28
chapter 29
chapter 30
chapter 31
chapter 32
chapter 33
chapter 34
chapter 35
chapter 36
chapter 37
chapter 38
chapter 39
chapter 40
chapter 41
chapter 42
chapter 43
chapter 44
chapter 45
chapter 46
chapter 47
chapter 48
chapter 49
FINAL
Trailer

chapter 9

287 32 1
Por Seemahwrites

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)
🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
BATA WANE👩🏻‍🦱
💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*Na*
*UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

*Wannan shafin naku ne*
*thanks for the love ummu najma fans*😘😘😘😘

Messages dinku masu tarin yawa da ake forwarding suna isowa gareni nagode Muku matuqa 💗 *Allah yabar qauna* 😍

*Wannan shafin naku ne*

*Ummu ahmad, ummu Albany, asmiee, sis Nadiya, hajiya larai, maman walida, maman Fatima, tyma shams, aunty raihana, my xuby, Ummin yusrah, habiba sani,auta ikilimat,Mrs abk,Mrs s. Hafseey husna Musa, maman nuseiba, ummu fu'ad pinky darling, fadila Mubarak*
Love you so much ❤️❤️❤️

09👯
Dafe goshin shi yayi Yana Jin wani takaici da haushin Salee na taso Masa, ya dauka matsalolin shi sun kusa zuwa qarshe tunda ya riga ya Sami Sarwa Amman wannan matsalan da Salee ta baro Masa baisan hanyar gyarawa ba,

Yanzu Yaya zaiyi ya samo Leesa? Yasan idan har ya maida Salee it's kadai ma Sa'ood to rayuwar shi ne da na iyalin shi zai shiga garari, already Sa'ood yayi warning dinshi idan ya sake Sarwa suka rabu to shima ya shirya rabuwa da 'ya'yan shi, for how long zai boye Sarwa daga mailafiya family saboda safetyn shi da na familyn shi?

Ko yayi abandoning Salee ne kawai tunda Bayan shi babu Wanda yasan sune Sarwa? To idan ya barta a gidan karuwai wani a u ya same ta fa tunda yanzu Bata da Mai tsaya Mata? Ko ya maida it wurin mamanmu ne tasan yaran ta suna Raye babu abinda ya same su?

Amman me zaice musu idan suka tambayi inda Leesa take?,

Muryan Salee ne ya katse Masa tunani
"Nace ko baka Sona ne malam Sa'eed?"

A zuciye ya sake daka Mata wata tsawa "could you please stop talking about love and help me find your sister?"

" Wallahi bansan Yanda taje ba, bamuda wasu Wanda muka sani a wani wurin ballantana nayi tunanin ko wurinsu taje, Kuma ta fadamun ba zata dawo ba har sai ta dauki fansa"

"Fansar me Kuma?"

" Iyayen mu take son hallakawa kaman Yanda suka hallaka rayuwar mu nasan kafiya irin na Leesa ba zata dawo ba sai ta cika burina ta, please malam Sa'eed kada ka tafi ka barni ni kadai a Nan duk duniya babu Wanda nake dashi Bayan Leesa Kuma ta tafi ta barni dan Allah kada ka guje ni"

Sauqe numfashi yayi Yana qoqarin daidaita fushin sa ganin Yanda take kuka kaman ranta zai fita, tausayin ta sosai ya Kama shi yarinyar da take da gata gaba da baya Kai harda hagu da dama Wai itace yau take living irin wannan rayuwa Mai kadaici da asara duniya Kenan,

"Kina da Wanda zasu bada auren ki?" Taji maganar shi ya doki dodon kunnen ta,

A hankali ta girgiza kai

Yace "ok nasan abinda zanyi, ki fara shirye_shirye qarshen watan Nan za'a daura mana aure" yana Gama fadan haka ya juya ya tafi Yana Jin Maganganun da ya fitar kaman wata guba ce Wanda zai lahanta rayuwar 'dan uwana shi,

Sa'ood ne ya fara rainon Sarwa lokacin da suka fara tasowa, Amman hankalin shi yafi karkata wurin Salee don ita yake burin ta zamo matar shi idan ta girma, Amman gashi qaddara ta jawo zai auri burin 'dan uwan sa,

'da zaran ka Samu Leesa sai ka saki Salee ya maidata ma Sa'ood' yaji zuciyar shi ta bashi wannan shawaran,

"Yauwa, perfect idea hakan shine kawai maganin masifan da nake ciki"

**********
4:00pm
Suka fito daga gidan su Ameerah suka nufi rijiyar Zaki gidan wata hajiya Wanda take nemawa Mata aikatau ko na cikin gida ki na shago.

Mata da yawa suka samu a cikin gidan Saida suka you zaman jira kafin tazo kansu, suka gaisa da maman Ameerah Leesa ma ta gaishe ta kafin mama ta fara you Mata bayani
"Daman yarinya ce muka kawota a sama Mata aiki gata Nan" ta fada tana nuna Leesa.

" Ina iyayen ta ko Wanda zai tsaya Mata idan wani Abu ya taso?"

" Gwaggon ta ne ni hajiya ni zan tsaya Mata babu wani matsala"

" To shikkenan, ke tashi na ganki da kyau"
Miqewa Leesa tayi matan ta qare Mata kallo tukunna tace ta zauna.

"Gaskiya yanzu aikin da muke dashi a hannu duk na shago ne, Dana restaurant da na saloon Kuma wancan yarinyan da kike gani na riga na hadata da Mai shagon saloon din har anyi ciniki, wannan Kuma tayi qarama ma aikin restaurant din dan babba suka ce suke so, ta Bari zuwa jibi sai ta dawo ko ba tare dake ba tunda an riga an Saba zuwa lokacin hala an samu aikin"

Dan marairaice fuska maman Ameerah tayi tace
"Har jibi hajiya? Dan Allah kidan yi Mana wani qoqari tana buqatar aikin da gaggawa ne"

" Na zama kuke so ko jeka ka dawo? Dan gaskiya yanzu na zama kawai nake dashi a hannu"

" Na zaman muke so hajiya"

" To shikkenan ta dawo gobe qarfe 2 sai muje gidan Amman tazo fa Akan lokaci Dan bamuson aiki da masu latti"

" Kafin biyun ma zata zo hajiya, Mun gode qwarai da gaske sai anjima"

Fita sukayi daga gidan ran Leesa fari Tass itama yanzu ta samu 'yancin kanta, dukda Bata San gidan wa za'a kaita ba Amman tana farin ciki sosai ta rabu da gidan karuwai,

Godiya ta dinga jero ma maman Ameerah babu adadi tana Jin Dadi sosai matan tayi Mata karamci dukda ba wani sanin ta tayi sosai ba Amman ta tallafi rayuwar ta.

**********
Sa'eed na tashi daga kasuwa yabi gidan Idris, yasan ba zaiyi supporting dinshi ba Amman shi kadai ne yake da connection da Sa'ood da Kuma baba alhaji,

Saida yayi addu'an neman tsari sosai kafin yayi knocking gate Mai gadi ya bude Masa suka gaisa ya wuce ciki.

Sallama yayi khalifa ya shiga dashi, ya samu Nabeela zaune da sauran yaran suna kallo, sajida ta tura ta kawo ma Sa'eed abin motsa Baki Khalifa Kuma ya shiga Kiran abban shi,

Idris na fitowa ya jashi zuwa parlorn shi sannan suka zauna, Saida Sa'eed yaja wani dogon numfashi ya furzar yace
"Brother na gaji da halin Zarah Yara na suna cikin mawuyacin hali dani kaina ma, bazan ci gaba da zuba Ido Ina kallon tana maida ni kaman wani sakarai ba don haka dole na dauki mataki Kuma kasan saki bayi daga cikin tsari na"

" To yanzu menene dalilin zuwan ka ka fada min matsalan cikin gidan ka, ai Kaine kake da alqadarin gyarawa"

" Nasan da haka brother, yanzu day baba alhaji nake son ka fada mishi aure nake son ya nema min Kuma cikin gaggawa nake son ayi don Zarah ta gane kuranta"

Gyara zama Idris ya tallafe cheek dinshi Yana kallon Sa'eed fuskar shi dauke da 'dan qaramin murmushi yace
"You are not serious Sa'eed, baka samu Sarwa ba har kana zancen wani aure? Kasan kuwa idan Sa'ood ya samu labari wallahi na lahira ma sai ya fika Jin dadi"

"Please brother Kar ka fada mishi nayi maka alqawarin zanyi iya bakin qoqarina na Nemo Sarwa Amman kada Sa'ood yasan wannan maganar ka taimaki 'dan uwanka musulmi Dan Allah"

" Shikkenan naji zan taimake ka ne kawai don nasan irin rashin da'an da Zarah take maka, Amman idan ka sake Jan dogon lokaci baka dawo da Sarwa ba wani Abu ya Sami mamanmu believe me ba auren ka ba har madaurin auren ka saina kashe"

Da sauri yace "na yarda" Dan Yana da yaqinin very soon Leesa zata dawo ba zata iya nesa da 'yar uwar ta na dogon lokaci ba.

Saida suka Gama sasantawa da Idris kafin ya koma gida Yana tunanin yanzu ya Gama kashe wuta daya sauran neman mutanen da zasu tsaya ma Salee a matsayin iyaye don ko da was Bai Isa ya fada ma momy cewa daga gidan karuwai take ba.
**********

Washe gari qarfe 1 Leesa ta Gama shiryawa cikin 'yar atamfanta rubber dinkin riga da skirt, da qyar ta yarda Ameerah ta fesa Mata turare kadan ta dau medium hijab dinta ta saka sannan ta dauki kayan ta gaba Daya 'yan gidan suka Mata rakiya har bakin qofa.

Har sunyi sallama zata fita mama ta riqo hannun ta
" Haleesa dukda nasan kinsan duk wani qalubale da jarrabawan rayuwa saboda irin gidan da Kika fito, Amman zan qara baki shawara ki Kama kanki komai na duniyar Nan Mai qarewa ne wata Rana sai labari"

Murmushi Leesa tayi tace "insha Allah mama, na gode sosai kinmin karramawan da babu Wanda ya taba min irin shi na gode sosai Allah ya saka Miki da alkhairi"

" Ameeen Leesa sannan duk ranar juma'a Zaki iya zuwa ki wuni ko ki kwana a gidan Nan saboda baban su bayi gari"

" Toh mama na gode sai anjima"

Tana Isa gidan hajiya ta zaunar da ita tayi Mata fada sosai Dan gidan wani babban 'dan siyasa za'a kaita dole ta Zaki Mai qwazo Kuma Mai tsafta,

Bata wani zauna a gidan ba suka tafi gidan aikin ta dake badawa layout, tangamemen gida ne na gani na fada haka leesa ta sake Baki shaaa tana kallon Yanda aka tsantsara ginin gidan Kai harda anguwan gaba Daya Dan dukan gidajen gidan babu na yarwa.

Saida aka caje su sosai kafin aka sanar ma matar gidan zuwan su ta bada Izinin su shigo.

A babban parlor suka same ta wata matashiyar Mata at her late 20's taci ado har ta gaji ga wasu ornaments masu tsada a jikin ta, tana zaune a kujera tana kallo a fankacecen Cinema dake jikin bango qafar ta Akan dan qaramin table tana taunan chewing gum cike da izza da Isa,

Suna shiga taga hajiya ta zube a qasa tana kwasar gaisuwa ita tabi ta suka zube tare,

Fuskar matar a murtuqe ta daqo tana qare musu kallon tana wani yatsine_yatsine kaman taga Kashi, Bata amsa gaisuwar ba ta nuna Leesa da yatsa tana
"Wannan 'yar abun ne Mai aikin da aka kawo min?"

" Eh ranki ya Dade qarama ce Amman akwai qwazo"

Tabe Baki tayi ta kalli Leesa daga sama har qasa sannan ta kawar da kanta ta maida Hankalin ta Kan TV, tafi 20 minutes batace komai ba kaman ma ta manta da rayuwar su cikin parlorn kafin can ta juyo tace

"Kin iya girki ne?"

Hajiya ta amsa Mata da "eh ranki ya dade ta iya"

"Dakata malama ba ke aka tambayar ba ita bata da Baki ne?"

Gyada Kai Leesa tayi " eh na iya"

"To zan dauke ki aiki Amman ana samun matsala dake zan Kore ki cause I don't tolerate nonesense, bani son shishshigi kada ki kuskura ki shiga abin da Bai dame ki ba ko menene shi kinjini ko?"

Duqar da Kai Leesa tayi tace " eh ranki shi dade"

"Ba sunana ranki shi dade ba, call me madam stupid illitrate"

Leesa taji zafin zagin da ta Mata Amman ya zamo dole ta shanye, matar taci gaba da cewa

"Kudin aikin ta 30k ko wani wata" ta zaro kudi a purse dinta masu Dan yawa ta jefa ma hajiya hajiya tayi Mata alaman ta fice da hannun ta, babu jimawa wata dattijuwar Mata ta fito cikin uniform dinta fari qarr da qaramin hijab baqi akai ta wuce da Leesa ciki,

Ba qaramin murnan da mamakin samun irin wa'innan kudaden masu tarin yawa lokaci Daya tayi ba, tasan kwanan Nan zata Tara kudin da zata bayar a Nemo Mata iyayen ta da Wanda zata sayi bindiga dashi, saidai tarin ayyukan da ta gani yasa tasan kudin da suke sakewa ba a banza ba.

Ana Gama nuna Mata ayyukan da ya Kamata ta dinga aka kaita dakin kwanan ta Mai gadaje guda uku sama da qasa ta ajiye jakar ta aka Bata uniform itama ta saka sannan suka bazama aikin yamma.

Sosai Leesa ta zage tayi aiki gashi Bata cika magana ba, duk surutun da wata ma'akaciya bilkisu take zuba Mata Bata tankawa saidai tace mata uhm ko uhm_uhm,

Duk cikin ma'aikatan gidan su biyu ne masu qananun shekarun sauran duk sun Dan manyanta, da aka fara Shirin girka dinner ma Leesa da chef da bilkisu ne suka dafa na hajiya wasu daga cikin ma'aikatan iuma suka dafa na karankaf masu aikin gidan.

Gaba dayan su Basu Sami zama ba sar 9 Bayan sun kammala komai suka koma dakunan su suna hutawa, bilkisu kaman wata carki taci gaba da bata labarin mai gidan da yaran gidan Wanda yazu haka suna London matan mutumin guda 2 ya tafi can da uwar gidan.

Har leesa ta canza kayanta tayi brush tayi alwala tazo ta kwanta bilkisu na jabe tana Basu labari, taja hannun ta da qarfi ta tura ta toilet tana fadin labaran sun Isa haka BBC hausa,

ranar saboda leesa da wuri sukayi barci don bilkisu na fitowa ta kashe wutan dakin kaman Yanda take yi ma Salee, kowa yayi barci Amman idanun ta biyu tana tunanin yaune Rana ta uku da zata kwana ba tare da 'yar uwar ta a gefen ta ba, Bata San wani Hali yanzu Saleeha take ciki ba tana son taji muryan ta ko sau daya ne Amman tasan Bata buqatar ta yanzu Sa'eed tafi buqata.

**********
A cikin satin Sa'eed ya dago baba alhaji da uncle Ishaq daga Mexico ba tare da sanin Sa'ood ba suka zo suka nema mishi auren Salee a hannun iyayen qarya da ya same mata aka Gama komai aka saka Rana suka bada sadaki suka koma.

Dan saboda kada suna kusantar Sa'eed ne Sa'ood ya tattara su ya maida su can da gargadin kada kowa ya taimake shi Koda kuwa momy ne har sai ya fito musu da Sarwa,

Biki sauran sati guda Sa'eed ya kawo akwatin shi manya guda biyu ranar anyi breaking record a gidan Shugaba for the first time karuwa zatayi aure a gidan mutunci, kallon da duniya suke Mata kenan,

Sosai tayi farin ciki Amman idan ta tuna babu iyayen ta babu 'yan uwanta tare da ita a wannan muhimmiyar ranar sai taji farin cikinta ya koma.

Duk wa'innan bidirin da akeyi Zarah Bata sani ba, sai Bayan ankai Kaya da sati biyun kafin maqwafciyar ta matar Mai gadi ta kawo Mata gulma...............🧚

#vote
#share
#comment

Seguir leyendo

Tambi茅n te gustar谩n

65.6K 8.5K 37
The idea of arranged marriage vanished into thin air when she set her eyes on him. Although he is nothing close to the man of her dreams, he is a 'pi...
220K 16.2K 20
Avantika Aadish Rajawat Aadi, with his fiery nature, adds intensity and excitement to their relationship, igniting a spark in Avni. Avni, like the ca...
Gentle touch Por K

Ficci贸n General

49.5K 1.1K 32
It had been mere months after her eighteen birthday, when she was pulled from the safe haven of her life and forced into the fantasy the women had cr...
18.6K 2.1K 37
STRANGE LOVE (THE FULANI BRIDE 2)... Yes! It's strange for a thirteen year old girl to find herself tied in marriage with someone she never knew...ho...