KAMA DA WANE....(Completed)

By Seemahwrites

13.2K 1.8K 210

even though they look alike that doesn't mean they should have same goals, their life is filled with regret... More

chapter 1
chapter 2
chapter 3
chapter 4
chapter 5
chapter 6
chapter 7
chapter 9
chapter 10
chapter 12
chapter 11
chapter 13
chapter 14
chapter 15
chapter 16
chapter 17
chapter 18
chapter 19
chapter 20
chapter 21
chapter 22
chapter 23
Apology
chapter 24
chapter 25
chapter 26
chapter 27
chapter 28
chapter 29
chapter 30
chapter 31
chapter 32
chapter 33
chapter 34
chapter 35
chapter 36
chapter 37
chapter 38
chapter 39
chapter 40
chapter 41
chapter 42
chapter 43
chapter 44
chapter 45
chapter 46
chapter 47
chapter 48
chapter 49
FINAL
Trailer

chapter 8

248 36 1
By Seemahwrites


(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
  🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
                          BATA WANE👩🏻‍🦱
   💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *Na*
        *UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Special gift to *Muhammad karim*
          And Fenarh matar Soja

08👯
4:00am
Ta farka saboda kiraye kirayen sallah da akeyi, har yanzu wuri da duhu sai dan hasken wutan lantarki dake can gefe kusa da masallacin Tasha.

tsoro ne ya Kama ta sosai da taga mutanen dake kwace Akan benches suna barci ga kwalaben giya da sigari barbaje ta ko Ina, tasan motsi kadan zatayi su farka hakan yasa ta koma wurin da take kwance ta rungume jakar ta a qirjin zuciyar ta cike da fargaba.

Kaman a cikin kunnen ta ake Kiran sallan haka take ji, ta Saba hudu nayi ita da Salee zasu farka suyi sallah kafin su fara tilawan Al-qur'ani har a shiga sallan asuba.

Ko a wani Hali Salee take yanzu? Tana cikin kwanciyar hankali Koko Aa? Kodayake tasan ba zata damu da rashin ta ba tunda ta iya fitar da ita daga zuciyar ta, a ko wani Hali Salee take tana Mata fatan alkhairi, Allah yasa Sa'eed ya Bata kulawa.

Har gari ya fara haske mutanen Nan Basu farka ba itama Bata fito daga wurin da take labe ba, saiq 6:30 na safiya kafin drivers da sauran ma'aikatan tashar harda passengers suka fara shigowa.

Hamdala tayi da taga wurin ya fara cika da sauri ta fito rungume da Jakarta tana bin mutanen wurin da kallo, taje wurin toilet din Mata ta zaro 1k daga cikin 27k dake Jakarta ta bada kudin shiga.

Kallon ta kudin tayi tace Bata da canji saidai take wurin 'yan talla ta Nemo, Leesa batayi musu ba ta sake kinkimar jakar ta take wurin da take tunanin zata samu canji tana ankare da idon mutanen dake kanta, tunda ta Ciro kudin Nan suke binta da kallo.

Qosai na 100 ta siya da pure water na 20 ta zuba a cikin jakar kayan ta ta koma wurin public toilet din ta biya kudin shiga naira 50, ta cika ruwa a buta zata shige matar tace
"Baiwar Allah ki bar jakan a Nan wurin Mana a kula Miki da ita kafin ki fito"

Murmushin Yaqe tayi tace
" Aa hakan ma yayi " Bata jira cewar ta ba ta shige toilet din, bada jimawa ba ta fito tayi alwala, sannan ta ciro zani ta shimfida tayi sallah jakar ta na gaban ta tana kallon shi.

Tana idarwa ko addu'a batayi ba ta tashi daga wurin Dan ta lura da mutanen dake zagaye da ita son rabata da sauran abun da ya rage Mata sukeyi ta nufi wurin da ake shiga motoci.

Kaduna taso zuwa wurin wata aunty Helen, saidai motan kaduna babba ce kuma namiji Daya ne a ciki, ga wa'innan mutanen har yanzu suna biye da ita Bata da zabin da ya wuce ta shiga motan KANO Wanda ya kusan cikawa, tana shiga daya daga cikin su yabi ta cikin motan baifi da minti 30 ba aka karbi kudan mota suka dau hanya.

Tunani take yi ita yanzu Ina zataje a Kano Bata San kowa ba Bata San ko Ina ba gashi abinda ta guje mawa ya biyo ta.

Saida suka kusan Isa sannan ta tuna da gidan su qawar ta Ameerah dake DUKAWA saidai fatan ta Daya Allah yasa Basu tashi ba don rabon ta da Ameerah tun primary school, baban ta drivern babban mota ne da yake tafiyar da Kaya gari zuwa gari.

Suna Isa Bata 'bata lokaci ba ta tsari a dadidaita sahu suka nufi DUKAWA, sauqe ajiyan zuciya tayi ganin sun tsere ma wancan mugun mutumin saidai batasan ko Yana biye da ita ba, addu'a kawai takeyi Allah yasa baban Ameerah bayi gida don babu shakka idan Yana gida bazai barta ta zauna ba saidai ta tafi wani wurin daban.

**********

Yau Salee Bata farka da wuri ba Saida Lateefa ta buga Mata qofa ganin Basu fara aikin su ba Kuma sunada zuwa makaranta.

Tashi tayi ta zauna tana murtsuke idanu, cikin muryar bacci tace
"Leesa open the door"

Shirun da taji yasa ta fara laluba wurin da take kwanciya, tsaki taja ta bude idon ta a hankali ta tashi ta bude qofar a tunanin ta fita Leesa tayi Bata tashe ta ba.

Lateefa ta gani jikin qofar su cike Dan damuwa tace
"Salee Yaya ya Baku tashi kunyi aikin ku da wuri ba? Kunbar Shugaba tana ta fada, Ina Leesa take ne?"

" Taje toilet"

" Anya kuwa? Daga toilet din nake Kuma Banga alamun tana ciki ba saidai idan wani wurin taje".

Komawa dakin tayi ta dauko buta ta fita tayi alwala, har ta idar da sallah Bata lura da takardan da Leesa ta ajiye Mata ba, ta fita ta fara shara tana gamawa ta dauki bucket ta zaga dibo ruwa a ranta taraddadin Ina Leesa ta tafi da safiyar nan? Bata Saba irin haka ba ita ba Mai yawo bace to Ina ta tafi Kenan?.

Bata Gama diban ruwan ba ta ajiye bucket dinta don hankalinta ya fara tashi taje ta sanar ma shugaba ba'a ga Leesa ba.

Har 10:00 Basu samu Leesa ba a gaba Daya unguwar hankalin Salee yanzu Kam ya Gama tashi taci kuka har taba ma uku Lada, Wanda sukaje Nemo ta a school suna dawowa suka fada musu ba'a same ta ba nan Salee ta qara birkicewa, kaman Wanda ta tuna wani Abu ta koma dakin su ta duba akwatin su Amman babu kayan Leesa a ciki.

Kaman mahaukaciya ta fara firfito da kayan akwatin, ga nan takardan da aka tsince su dashi Amman babu necklace din Leesa Kuma ta lura kaman an taba kudin da suke Tarawa, hakan na nufin Leesa guduwa tayi Kenan?

A birkice ta fara watsi da dan kayan dakin tana dube_dube can ta hango takardan da Leesa ta ajiye Mata da gudu ta qarasa ta dauka hannun ta na rawa ta bude ta karanta, ihu ta saka ta zube a Kan guiwowin ta cikin qara take Kiran
"HALEESAHHHH please ki dawo wallahi bazan sake ba"

**********

Tana sauqa a bakin layin su Ameerah ta qara runguman Jakarta tana taka wa a hankali zuwa cikin unguwar, kowa ta samu sai tayi Masa tambaya a haka har takai ga qofar gidan, tana Shirin sallama saiga Ameeran ta fito da 200 a hannun ta da alama aika zataje.

Murmushi Leesa tayi ta Kira sunan ta, Saida ta qare Mata kallo na 'yan sakwanni kafin cikin tsananin mamaki tace "Salee?"

"Har yanzu Baki banbance mu ko?"

Daka tsalle tayi ta dale ta cikin murna tace "Leesa ce, oyoyo my Leesa shigo ciki Mana"

Ja tayi ta tsaya fuskar ta dauke da qaramin murmushi tace " baban ki bayi Nan ne?"

"Yana Nan Amman kada ki damu yanzu zai tafi Bauchi sai jibi zai dawo zo muje na kaiki dakin mu kafin ya Gama shiryawa"

A sudade suka shiga gidan suka wuce dakin su Ameerah dake can qurya, duk qannen ta sun tafi makaranta itama a ss2 tayi paper saboda ana shirin yi mata aure.

Zaunar da ita tayi ta kawo Mata ruwa
"Leesa Bari naje aikan baba na dawo saina kawo Miki breakfast"

Gyada Mata Kai kawai tayi tana fita ta Ciro qosan da ta siya a Tasha ya Gama sanyi haka ta tuttura Saida ta kusan cinyewa Tass kafin Tasha ruwa tana gyatsa Dan ba qaramin yunwa taji ba.

Har Ameerah takai aikan baban su yayi sallama ya tafi Leesa na maqale a daki tana faman raba idanu, sai Bayan ya fita da dadewa kafin Ameerah ta bude curtains din dakin tace mata
"Ki fito ku gaisa da mama na baban ya tafi"

Maman Ameerah Bata nuna wani damuwa a Kan zuwan Leesa gidan ba saboda ta santa sosai tun a jigawa Saidai tana tsoron Yanda Leesa ta tattaro kayan ta idan zama zatayi baban Ameerah bazai yarda ba
"Haleesa Mai yasa Kika bar jigawa Kika zo kano ko kina da wani Wanda Kika sani ne?" Shine tambayar da mama tayi mata

Girgiza Kai tayi hade da fadin "Aa Salee tayi aure ne ni Kuna bazan iya zaman gidan Shugaba ni kadai ba shiyasa nazo Nan garin neman aiki na samu na tallafa ma kaina nayi karatu Mai zurfi dan an fada Mun a garin Nan ba'a rasa aiki"

" Hakane Amman kinsan a wurin da Zaki samu aikin?"

" Aa, shiyasa nazo Nan Dan Allah ki taimaka ki nema min, Koda aikatau ne zanyi ko zaman shago koma menene idan zan samu halali inaso"

Sauqe numfashi mama tayi tasan kafin baban Ameerah ya dawo gidan ba zata rasa aikin da zata nema wa Leesa ba
"To shikkenan 'yata Bari a Baki abinci ki kwanta ki huta zuwa yamma sai muje neman aikin muga ko za'a dace"

Godiya Leesa ta hauyi kaman ta ari Baki
" Na gode sosai mama, Allah ya saka Miki da alkhairi ya biyaki da gidan aljannah"

" ameen Allah yayi Mana jagora".

**********
Qarfe 10 nayi Sa'eed yayi sallama ma Zarah Kan zai wuce kasuwa, addu'a yaran shi suka fara mishi, dady Allah ya kiyaye Allah ya tsare Amman Zarah tana tsaye qeqam tana kallon shi, har yanzu Bata manta incident din shekaran jiya ba gashi tun lokacin ta kasa ganewa Sa'eed Allah dai yasa ba da gaske karuwan zai auro ba, da kuwa ya Gama da rayuwar ta.

Takowa tayi gaban shi a nutse Yana faman ba ma yaran shi peck a kumatu ta tsaya tana qare mishi kallo, sauqar da kanta qasa tayi ta Kira shi da
"Miel(honey)"

In shock Sa'eed ya dago Yana kallon ta ya manta rabon da ta Kira shi da wani suna Bayan sunan da mahaifiyar shi ta rada mishi, tunda yaji haka yasan maganar babba ce yace Al-ameen ya riqe hannun Islam su shiga ciki idan ya dawo sai su tafi asibitin Dan yau ranar checkup dinsa ne.

Suna shiga ya zuba hannayen shi a aljihu Yana jiran ba'asi, a kunyace ta qaraso daff dashi ta dago dara_daran idanun ta, ta zuba mishi
"Miel I'm sorry for what I did to you earlier, I didn't meant to insult you but I can't help it, it's hurt's deep inside to know that you are in relationship with a prostitute, but insha Allah I will never repeat my mistake, forgive me"

Tallafo fuskar ta yayi Yana Jin kaman ya fada ma Zarah Salee 'yar uwarsu ce Sarwa laqanin karuwa bai dace dasu ba Amman yafi son sai ya dauke su ya mayar dasu ma Sa'ood tukunna.

"Inaso kisani cikin ko wani yanayi Ina matuqar qaunar ki Zarah, son ki a cikin jini na yake kece barin jikina duk wani abun da zai same mu a rayuwa inaso ki dauke shi a matsayin qaddara ta hakan ne kawai Zaki samu dacewa.

Abubuwa da yawa suna faruwa ba a son Raina ba Amor(love) bani da wata hanyar da zanyi maganin shi sai Wanda Allah ya hore min, please ki kasance tare dani ki zamo min bangon dafawa ko na samu na gyara Kira kuren rayuwa ta, I love you ok?" Ya Kai Mata peck a lips sannan ya fita a gidan ya nufi hanyar gidan su Salee.

Kamar wancan lokacin yauma Yana zuwa ya saka aka mishi sallama da ita lokacin tana kwance tana rusgan kuka anyi rarrashin har an gaji, tana Jin ance ana sallama da ita Bata tsaya tambayan ko waye ba ta zari hijab dinta ta fita da Sauri Dan tasan Sa'eed ne kadai me yin haka.

Tana fita ta hango shi tsaye ta gefen gidan da gudu taje ta shige jikin shi tana qara sakin kuka, a take yaji wani shock tun daga tsakiyar kanshi har yatsun qafar shi da qyar ya iya tattaro kuzarin shi ya bambare ta daga jikin shi Yana tambayan ta ko lafiya.

"Malam Sa'eed Leesa ta gudu ta tafi ta barni ni kadai bansan Ina ta tafi ba"

Dum..durum..dum Haka qirjin shi ya fara jumping baisan lokacin da cikin tsawa yace "GARIN YAYA?" Ba.

Harta Salee ta tsorata da yanayin shi lokaci guda ya rikice ya daburce, hawaye na kwalala a idanun ta tace
"Ban sani ba, kawai tace nayi choosing ne ni Kuma na Zabe ka ban dauka abinda take nufi ba kenan, ban taba tsammanin zata tafi ta barni ni kadai ba please ka taimaka min"

"Salee Mai yasa zakiyi haka? Why did you choose me over your twin sister? Why?"

" Because I LOVE YOU malam Sa'eed ko Kai baka so na ne?"................🧚

#vote
#share
#comment

Continue Reading

You'll Also Like

33.6K 2.9K 27
အချစ်ရူးနှင့်တော်၀င်ပန်း
221K 16.2K 20
Avantika Aadish Rajawat Aadi, with his fiery nature, adds intensity and excitement to their relationship, igniting a spark in Avni. Avni, like the ca...
102K 9.5K 51
Boddo is a Fulani girl, who will be married at young age of 13yrs to the man who she never knew or saw in her life who is also educated.....how will...
356K 21.7K 37
Let's see how different personalities mends with each other to form a beautifull bond together. Where the Eldest is calm and cold, Second is aggress...