KAMA DA WANE....(Completed)

Bởi Seemahwrites

13.2K 1.8K 210

even though they look alike that doesn't mean they should have same goals, their life is filled with regret... Xem Thêm

chapter 1
chapter 2
chapter 3
chapter 4
chapter 6
chapter 7
chapter 8
chapter 9
chapter 10
chapter 12
chapter 11
chapter 13
chapter 14
chapter 15
chapter 16
chapter 17
chapter 18
chapter 19
chapter 20
chapter 21
chapter 22
chapter 23
Apology
chapter 24
chapter 25
chapter 26
chapter 27
chapter 28
chapter 29
chapter 30
chapter 31
chapter 32
chapter 33
chapter 34
chapter 35
chapter 36
chapter 37
chapter 38
chapter 39
chapter 40
chapter 41
chapter 42
chapter 43
chapter 44
chapter 45
chapter 46
chapter 47
chapter 48
chapter 49
FINAL
Trailer

chapter 5

280 28 0
Bởi Seemahwrites

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
  🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
                          BATA WANE👩🏻‍🦱
   💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *Na*
        *UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Wannan shafin naku ne masoyan gaskiya, members din *REAL KAMA DA WANE FANS*
Special thanks to
*My Umma sulaiman, Aisha Hamza (sweetheart), maman hafeez, maman saudat, Aisha Lameengel (namesy), maman sadeeq, my pinky(ruqy), antimee,zee dauda, hadiza mustapaha, ummu al'amin, hadiza aminu Ali, Maryam gambo, Mrs Abdullahi, sis pha'ixer, sis hussy, maman Shaheed, maman ammar*......... *Wanda ma basuji sunan su ba ma su jira coming pages sharhin ku na qayatar Dani matuqa, love you so much ❤️❤️❤️*

05👯
Tsayawa tayi a qofar gidan su tana karanto addu'oi kafin ta tattaro qwarin gwiwar ta na tunkaran Leesa ta shiga cikin gidan, Bata tsaya ko Ina ba sai dakin su lokacin na Shirin islamiyya.

Ta saka uniform tana qoqarin saka socks ta dago tana kallon Salee da ta rakube a jikin qofa tace
"Wato ke idan Kika fita sai an ganki ko? Tun kafin na debo ruwa Kika fita siyo sweet gashi har na shirya kina tsaye a wurin, kinsan dai ba jiran ki zanyi ba wallahi Ina gamawa tafiya ta zanyi"

Qarasowa kusa da ita tayi ta zauna tare da sunna Kai qasa tana faman murza laidan hannun ta da kaganta kaga marar gaskiya, a hankali ta Kira sunan ta.

Saida ta leqa fuskar ta kafin ta dago kanta tana Mata kallo Mai alaman tambaya tace "meye?"

Gyara zama Salee tayi ta fara bayani
" Kinga dai kyautatawa Yana da kyau ko? Kuma idan ka fitar da wani daga qunci kaima Allah zai fitar dakai, Kuma kin tuna malam yace Mana sadaka na maganin baqin ciki Yana yaye masifa Kuma kema kullum sai kinyi sadaka da safe saboda burin mu ya cika ko ba haka ba?"

Daure fuska Leesa tayi tace " eh haka ne, sai akayi Yaya"

"Umm... Am...Daman inaaso ne na taimaki wani bawan Allah wallahi Baki ganshi ba abun tausayi, matar shi bata bashi abinci wani lokaci kwana yake da yunwa shine nakeso ki amince Mun na....."

" Na amince Miki ki ciyar dashi ko? Gaki 'yar gidan qaruna"

" Aa da kudin shi fa, ya roqeni ne yanaso Yana bada kudin shi a dinga dafa mishi abinci daga gidan Nan ana Kai mishi"

Miqewa tayi ta jawo hijabin ta tana qoqarin sakawa tace
"Waye shi?"

Da sauri Salee take
"Malam Sa'eed dinnan ne na school dinmu wanda nace Miki yaran shi kyawawaa"

" To ban yarda ba, akwai restaurant bila adadin a garin Nan idan bayi da kudin da zai iya ci a wurin yaje maciya ya siya Amman baza a dinga Kai Masa abinci daga gidan Nan ba kinji na fada Miki, idan kin Gama ki same ni a makaranta Kuma kiyi sauri"

Tana Gama fadan haka ta fita, dama Salee tasan da'a rina Kuma tayi alqawarin ko Leesa Bata so sai ta dinga kaiwa malam Sa'eed abinci Koda kuwa a boye ne.

Da suke dawowa daga islamiyya ma haka Salee ta matsa tana Mata Magiya Amman turmushishi taqi, itama daga Nan tahau dokin zuciya bataga dalilin da zaisa Leesa tana mulkanta tana juya ta Yanda taga dama ba Bayan tsakanin su ma babu wani rata.

Haka da daddare sukayi ta zaman kurame kowa na fushi da kowa, har Leesa ta Gama assignment dinta suka kwanta basuyi ma juna magana ba, cikin gaggawa Salee ta shirya ta tafi makaranta.

Da aka tashi ma Bata tsaya jiran Leesa ba ta fito ta dawo gida ko uniform Bata cire ba ta dauki kudi ta wuce shago ta auno shinkafa da mangyada da Maggi taje ta siyo kayan Miya sannan ta koma ta girka ma malam Sa'eed lafiyayyen jallof rice .

Tana kitchen Leesa ta dawo, kallo Daya tayi Mata kau da Kai ta ajiye plastic bucket din awaran su ta tattari wanke_wanke ta fara yi.

Salee taji zafin hakan Amman idan Akan malam Sa'eed ne a shirye take da ta dauki duk want wulaqancin da Leesa zatayi Mata.

2:30pm

Ta Gama hada abincin ta dauki wata madaidaiciyar food plask a cikin na shugaba ta zuba a cikin sannan ta dauki medium hijab ta daura Akan uniform din jikin ta Leesa tana kallonta ta fita.

Runtse Ido tayi hawaye na sauqa a idanun ta, yau ne Kari na farko da Salee 
Fara bijire Mata, tanaji a jikin ta wannan Sa'eed din ya shigo rayuwar su be kawai don ya Bata tsakanin ta da 'yar uwar ta Kuma ba zata taba barin haka ya faru ba.

Mai a daidaita Yana sauqan shi a farkon layin ya hango ta tana nufar qofar gidan shi da food plask niqi niqi a hannun ta Kuma da alamu shiga ciki zatayi, da sauri ya biya shi kudin shi ya qarasa wurin ta har Yana tuntube saboda gaggawa.

Daidai zata buga qofar gidan ya jawo hannun ta baya suka shigar lungun dake gefen gidan Yana binta da kallon tuhuma.

Kallon hannun shi dake riqe da nata tayi ta kalli kyakkyawar fuskar shi tana tuna maganar da Leesa take yawan fada Mata
"Duk mutumin da zai taba jikin ki Bayan ke ba Muharraman sa bace to ba mutumin arziqi bane Kuma bazai taba sonki da gaske ba don ba'a hada halal da Haram a wuri daya"

Saidai wani bari na zuciyar ta na hure Mata kunne, ta juri duk abinda malam Sa'eed dai Mata shi baiyi Kama da mutumin banza ba, Kuma ai abunda yake mata alama ne na ya nuna Yana sonta ba wani Abu ba.

Muryar shi ne ya katse Mata tunani, fuska babu alamun wasa yace
"Where do you think you are going?"

Raurau tayi da idanu tace " abincin ka ne zankai maka gida?"

Ya zaro Ido hade da fadin "are you crazy? Kinsan abinda kike yi kuwa? Da Mata ta ta cikin gidan shine Zaki shigar da abinci kice Mata na me? Kada ki sake min irin haka wallahi, idan kin kawo ki dinga bawa wancan Mai shagon Yana ajiye Mun zanzo na dinga karba"

Gyada Kai yayi babu ko godiya yace " to wuce ki tafi"

Jiki a sanyaye ta juya ta fara tafiya shima sai yaga rashin dacewar hakar, a hankali ya Kira sunan ta ai kuwa kaman jira take yi ta juyo.

Ya Ciro 500 a aljihun shi ya miqa Mata
"Gashi kudin na gobe thanks"

Kaman yace Mata I love you haka taji ta karba ta juya tana murna kaman an Mata albishir da aljannah, sai alhamdulillah take maimaitawa har ta Isa gida, she can't believe Wai itace  zata dinga dafa ma malam Sa'eed abinci, she is extremely happy she just love Sa'eed so much. (What? Daga ganin sarkin fawa sai Miya tayi zaqi?)

Da food plask din a hannun shi ya shiga gida, ya samu Zarah a tsakar gida tana fige kaza sai qananun mita takeyi don a da batasan wahalar shi ba, packaged chicken suke siya komi yawan shi haka za'a kawo su a gyare a yayyanke Kuma a kawo maids dinta su sarrafa shi.

Dan murmushi yayi cikin son ya kunnata ya qaraso Yana Mata sannu kaman abun arziqi yasan yanzu zata hau ta cika tayi fam Amman Zarah Bata sani ba idan tana fushi dada yi Masa kyau takeyi, Kuma ko me take mishi Yana dada Jin sonta cikin ranshi.

Tsaki taja ta juyar da kanta Bata kula shi ba taci gaba da gyaran Kazan ta tana qara sautin mitan ta don yaji abun da take fada.
"Saboda wahalar aiki wataran sai qasusuwa na sun gutsutstsure, ace mutum haka dai zauna kamar inji yayi ta aiki, Shi Kuma wancan yaron da na aike shi tuntuni ya kasa dawowa shima ya kwashi halin ubanshi bayi aikata wani Abun arziqi ko glasses dinshi ne sukayi expire a hanya oho"

Dariya yayi yace "mi alma al'amin ne ko? Kiyi haquri Bari ni na Taya ki idan ya dawo sai na Zane shi tunda Yana sa matata fushi fuskar ta yayi ta ja kaman strawberry"

Wuqan hannun ta ta saita a fuskar shi kaman zata tsole mishi idanu
"Ka tashi ka bani wuri Sa'eed kafin kaima nayi maka sanadin fara saka glasses, ai duk sanadin Kane nake wannan wahalar Allah ya Mun maganin ta Dan talauci musiba ce"

Daga hannun shi sama yayi alaman yayi surrender yace "yi haquri ranki ya dade, Kinga tafiya ta"

Daki ya shiga ya rage kayan jikin shi sannan ya fada toilet ya watsa ruwan sanyi dan bayi Bata lokacin shi tambayan Zarah Mai zafi yasan ba bashi zatayi ba.

Yana fitowa Islam tazo da gudu ta dale jikin shi tana oyoyo dady,
Daga ta sama yayi ya manna Mata kiss a cheeks yace "oyoyo my Eesy ina kikaje ne dady ya dawo Baki Nan"

" Munje aika ne nida ya al'amin, dady wata aunty Mai kirki ta bamu sweet a hanya sunan ta aunty Salee"

" What? Salee Kuma?"

" Yes dady kagan shi ma" ta fito da sweets din tana nuna mishi.

Tura ta was kawai yayi ya zauna Yana nazarin al'amuran yarinyan nan abun nata har ya fara bashi tsoro, duk da sunyi irin haka da Zarah Amman ko a lokacin ta girme ta Amman wannan fa yarinya ce qanqanuwa har tasan Yanda zata jawo hankalin namiji gareta? Kai Allah yayi Mana maganin zamani.

Da tunanin Salee a ransa ya Gama shiryawa ya Kira Islam da al'amin ya baje musu girki suka kwashi gara sai yaba qwazo irin na Salee yakeyi Yanda ta iya girki Mai dadi, dan bazai yaudari kanshi ba Zarah Bata iya girki ba, don rabon ta da ta kwatanta dafa wani Abu na musamman saboda shi tun tana amarya.

**********

Bata damu da rashin kulata da Leesa take yi ba don yau malam Sa'eed ya wanke Mata zuciyar ta tass, Haka ta wuni tana aikin ta cikin annashuwa saboda yau Thursday ne babu islamiyya, sai rera waqar soyayya take yi tana maganganu ita daga kaman Mai tabin hankali, tanayi tana murmushi.

Da daddare taje tayi sayayyan kayan abincin da zata dafa mishi gobe tana dawowa ta samu Leesa na zaune a qofar dakin su tana jiran ta, har zata wuce ciki ta jiyo ta tana fadin.

"Ina Kika je da wannan daren Baki sanar dani ba?"

Dan Juyowa tayi tana kallon ta sannan ta tabe Baki tace
"Nasan ko na tambayi Izinin ki ba Bari zakiyi ba tunda dai gashi naje na dawo lafiya ai shikkenan"

Numfashi Mai zafi Leesa ta furzar sannan ta tashi ta tako daf da ita tana kallon ta cikin Ido
"Salee Ina takura ki da yawa ko? Na Hana ki sakewa ko? Kina tunanin abinda nake Miki tauye 'yanci ne ko? Ni Kuma a nawa qaramin tunanin tunda na rasa uwa mai kula dani bazan barki kiyi rashin uwa ba inason nayi Miki gata baniso kiyi kukan maraici ko kuma kiyi dana sani idan rayuwar ki ta lalace a cikin wannan gidan, nayi kuskure da na Bari Kika zamo weakness dina da ace iyayena ne Naga wani Abu zai cutar dasu bazan taba kulawa ko na nuna damuwa ba Amman ke! Bazanyi Dana sani ba idan na sadaukar da rayuwata gareki"

Juyawa tayi zata tafi Salee tayi saurin riqo hannun ta qwalla na taruwa a idon ta take
"Kiyi haqurin Leesa bazan sake ba Amman Dan Allah ki Bari in dinga dafa wa malam Sa'eed abinci Nima in samu aikin alkhairin da zan dinga alfahari dashi"

"Shikkenan tunda Haka Kika zaba Amman da sharadin ba ke Zaki dinga Kai mishi ba sedai kina aika yaro saboda wallahi baniso wani Abu  ya shiga tsakanin ku ko kadan"

" Toh" kawai tace mata badan taji dadin hukuncin da ta yanke ba Dan Leesa ta makara, zuciyar ta ya riga yayi nisa cikin kogin son Sa'eed dukda Bata San shi waye bane ita yanzu babban burin ta shine ta samu hankalin shi shima ya nuna Yana son ta.

Tun daga wannan lokacin Salee ke faman rangada ma Sa'eed girki ta bayar akai shagon da yace ana ajiye mishi a wurin, Amman daga baya sai ta faki idon Leesa taje ta same shi daga baya su zauna su Sha Hira.

Har yanzu bayan mutunci da sabo babu wani baqon yanayin da take ji game da Salee, baisan abun da take zuciyar ta ba Amman shi tun a da Bai iya wulaqanci ba shiyasa mutane suke yawan sabo dashi sosai fiye da Sa'ood Kuma yammata suke saurin falling mishi, shidai yasan Salee ta iya zance duk da qananun shekarun ta Amman tana tauna zance ta tace shi kafin ta fitar dashi Wanda kwata_kwata Zarah Bata iya wannan ba, ko wani magana ya fito daga bakinta Bata tauna shi haka take fitarwa.

A hakanma har suka shafe watanni 5 Salee tana kawo mishi abinci Zarah Bata taba nuna damuwar ta ba, kullum kuwa dada son malam Sa'eed takeyi burin ta kawai Allah ya mallaka Mata shi.

Idris Kuwa ya daina kawo masa labarun qarya game da Sa'eed Dan yanzu tsoro ya shige shi sosai, wasu bangare na jikin mamanmu sun fara aiki da kansu shiyasa aka rage Mata machines din da suke taimaka Mata.

Gaba daya mailafiya family sunyi murna da wannan improvement din saidai idris da Sa'eed tsoro ne ya cika zuciyar su, idan har mamanmu ta farka Sa'eed baisan me zaice Mata Akan whereabout din Sarwa ba Idris Kuma yasan tana tashi dubun shi ya cika Dole ya shiga prison girban abinda ya shuka.

*********
4:40
Ya shigo cikin gidan da mamakin shi baiga Zarah a tsakar gidan ba, Dan ko bazatayi Masa tarban arziqi ba idan tasan lokacin dawowar shi yayi zata fito tayi mishi na tsiya.

Yana Shirin fara dubata cikin dakinta ko Bayan gida ta shiga ya jiyo saitin kukan ta ta Bayan shi da sauri ya juya Yana kallon ta.............🧚

#vote
#share
#comment

Đọc tiếp

Bạn Cũng Sẽ Thích

1.4M 127K 62
RATHOD In a broken family, every person suffers from his insecurities and guilt. Successful in every field but a big failure when it comes to emotio...
Ice Cold Bởi m

Tiểu Thuyết Chung

2.2M 83.3K 49
[boyxboy] Wren Ridley is always two steps ahead of everyone, or so he thinks. His life seems out of his control when he starts having feelings for so...
18.6K 2.1K 37
STRANGE LOVE (THE FULANI BRIDE 2)... Yes! It's strange for a thirteen year old girl to find herself tied in marriage with someone she never knew...ho...
5K 442 40
love is a strange feeling but also a very strong connection that will either be your strength or your weakness it all depends on who you've to be wit...