SAWUN GIWA...!🐘

By Hafnancy01

3.2K 68 8

"Dallah gafara can malama, har ke kin isa ki mana abunda Allah bai mana shi ba? Akanki ne aka Fara irin hakan... More

INTRODUCTION
01
02
03
04
05
06
07
08
09
10
11
12
13
14
TUNATARWA
SHIGO DAGA CIKI...

15

191 5 0
By Hafnancy01

           ♡
               ♡ ♡
_*🐘SAWUN GIWA...!*_
          _(The Elephant's Foot)_

  _★For How Long Will The Elephant's Foot Be Radioactive?_

 
  *FInd out💥*
     

       *WATTPAD*➖ _HAFNANCY01_

*DEDICATED TO:-Mamina (Sis Nerja'art & Yayata (Ummudilshad)*
          
_*•SPECIAL GIFT TO:-Tawar (Maman Kausy)*_
__________________________________

                *BABI NA SHA BIYAR♡*
___________________________________

                       1️⃣5️⃣

       _Last free page_

_______________

"Ya Zaid dama ashe kai ne wanda Abba yake shirin aura mun.?Meyasa.?meyasa zakui haka.?Ko Kun manta cewa ka tab'a shiga sahun maneman yar'uwata ne.?To wallahi ku sani bana yi, bazan tab'a baku goyon baya akan wannan abun kunyar ba, Allah azatona abu ne wanda zan iya shanyewa, ashe abunda ban sani ba al'amari ne wanda zaizo yasha k'arfina" Ta ida magana tana mai rushewa da kuka, Gabaki d'aya yaji kansa yayi wani irin girman gaske tamk'ar wanda aka azawa damin kaya, Fuskarsa ta bayyana tsantsar tashin hankali mara fassaruwa, Tuni idanunsa suka canza launi zuwa jawur don Zaid bai iya shiga tashin hankali ba Musamman in har akan 'ya mace ne.
                    
.  Kamar zai saki d'an marayan kuka yace"Zainab pls dan girman Allah karki mana haka, Ki sani babu haramun acikin aurena dake Tunda ban auri Najlat ba, ina dai amsa sunan maneminta ne ammh bata tab'a bani fuskar soyayya ba, dama nine kawai nake ta haukana, inata b'atar da Lokacina akanta, daga baya dana Lura da gaske ba sona take ba shiyasa na fita daga rayuwarta, Cikin hukuncin ubangiji sai ya had'ani da mace mai sona don Allah, Sunanta Harira, Yarinya nutsastsiya kamarki, ada bikinmu zai kama rana d'aya ne danasu Najlat ammh sai Allah ya dauki abinshi, Shekaranjiya take cike kwanaki goma sha bakwai da rasuwa, Zainab ina cikin halin ha'ula'i, Na had'aki da Allah karki karamun wani damuwar akan nada, ki taimaka ki karbi kokon barata agareki ki maye mun gurbin Harira, wallahi i love you Zeeyta, daga jiya zuwa yau kadai gabaki d'aya na rasa tunanina akanki, ga abokina can Junaid shine zai fi baki labari dak'yau."

Hak'ika ta tausaya mishi kwarai da gaske da babban rashin da yayi, sai dai bata jin hakan zai sa tayi abunda yakeso, Karon farko arayuwarta tana neman watsawa Abbanta kasa a ido, Runtse idanu tayi wasu zafafun hawaye suka kwaranyo mata, Cikin k'aryewar murya take Fadin"Wallahi Tallahi Ya zaid duk kuyi hak'uri ammh bazan iya aikata abunda kukeso ba, in ku zaku iya had'o idanu da Najlat bazaku ji kunya ba, to ni zanji sosai harda ma na fitar hayyaci, Dan Allah na rok'eku kuyi saurin barin gidan nan don bani son Umma ko ita Najlat d'in su farga da abunda ke shirin Faruwa."

"Zainab karki watsawa Abbanki kasa a ido don karki so kiga yadda yake ta yabonki yace bazaki tab'a bashi kunya ba, so pls in ma so kike in k'ara miki Lokaci kiyi nazari zan ara miki ammh kar kice bazaki aureni ba don wani dalili naki mara k'arfi." Afusace tace"Allah babu wani nazarin da zanyi, amsar guda d'aya ce kuma shine bana yi." Azafafe shima yace"Zainab wai meyasa kika fiya taurin kai ne.?kwata kwata baki da Fahimta." Har ta bud'e baki zatai mishi masifa, da sauri ya Fuzgo hannunta ta fad'o cikin Falon babu shiri don so take ta daga murya har mutan gidan su Farga da halin da suke ciki.

 
    **

"Wai miye haka ne ka wani tattare hanya kaki bani wuri in wuce bayan kuma kai ne ina baccina hankalin kwance kazo ka tasheni wai surukaina sun zo gaishemu, ka bani wuri inje in gansu, inga ya kamanninsu yake ammh ka hana, wannan wani irin fitina ce haka.?Anya Habibu kodai kana da wata akasa ne dani.?" Ajiyar zuciya mai zafi ya sauke yana Fadin"Kiyi hak'uri so nake su d'an tab'a abun motsa bakin da aka kai musu kafin ki shiga don na sanki sarai zuwa zakiy ki sasu agaba har su kasa sakewa su ci abun kirki."Wani tsalle tayi ta diro ta gabanshi tana Fadi da kumfar baki"Ay lallai kam naga alama, wato ga mayya wacce zata lashesu ko.?dadin abun dai duk haduwarsa nasan bazai tab'a kama kafar Hassan ba, dallah bani wuri inje inga jememmen fuskar tasa."

Ta ida magana tana mai bankad'e shi gefe ta fice, binta da kallon Allah ga shiryaki yayi sannan yabi bayanta gabansa na bugawa da k'arfi.

 
......Afusace Ummi ta mik'e tana bin Zaid da wani irin kallon tsana, Tun kafin tayi magana Junaid yayi saurin mik'ewa yana Fadin"Look guy's kufa ba yara bane da har zaku tsaya kuna irin wannan abin, Kai Zaid nasha fad'a maka ba'a neman soyayya ta k'arfi da yaji, bi ake sannu ahankali, idan kuma yarinya ta nuna alallai baka yi mata ba tou the best thing shine ka fita daga harkarta aganina abun da yafi kawai kenan, don arayuwar nan da kake gani ba komi ne zaka nema kuma ka sameshi ba, Ke kuma Zainab abunda abokina ya fad'a gaskiya ne, babu haramun acikin aurenki dashi don kawai ya kasance manemin yar'uwarki ada can, idan kika ce zaki bi ta kunyar duniya ne to fa zaki tab'e, gashi dai ranki na son abu ammh kina neman cutar da kanki akan wani dalili mara tushe, Zaid zai ara miki lokaci ki zauna kiyi tunani, kuma insha Allahu duk wata shawarar da kika yanke, mun dau miki alk'awari zamu karbeshi da hannu bibbiyu babu korafi, Fatarmu ayanzu dai Allah yasa kiyi shawara me k'yau wanda zai mana dadi duka."
Kallonsa ya mayar akan Zaid wanda yake cikin tashin hankali sosai yace"Muje ko.?ka rabu da ita tayi tunani don't force her." Gyad'a kai yayi alamun ya gamsu da abunda yace, daukar bak'ar hularsa yayi wanda ya ajje akan hannun kujera ya kafa akai, sharr ya fito kamar ango.Adaidai gabanta ya dakata, kanta aduk'e tana juya zancen Junaid aranta, ga dukkan alamu jikinta yayi sanyi, don har ga Allah in tace bata jin wani abu akan Zaid tayi wa mahaliccinta k'arya.Zaid yace cikin kwantar da murya"Zeeyta zan k'ara miki lokaci kamar yadda Junaid ya bukata, ammh pls karki sa mu cuci kanmu akan dalili marasa tushe alhalin muna son junanmu, sai munyi waya, kuma pls kibar mun asarar tsadadden hawayenki bcz u don't know how much value they are to me." Ya sakar mata wani tsadadden murmushi sannan yayi gaba ya barta cikin tunani.

Tun daga nesa Umma take hango fassasun glasses da kuma bottle water, sai kwalin Frutta orange juice, Cike da mamaki ta juya tana kallon Abba dake binta abaya lotoloto tace"Ba abin bak'in bane nan akasa.?" Kafin yakai ga bata amsa sai gasu Zaid sun Fito, da sauri sauri Abba ya nufosu yana Fadin"Har zaku tafi.?Gashi ma da dukkan alamu ko ruwa baku sha ba yarinyar nan ta barar da abu kuma bata tsaya ta kwashe ba, ke Zainab ina kike ne.?ke agarinku haka akeyi ne.?" Junaid ne yace yana d'an sosa k'eya"A'ah Abba ai kowa bai wuci kuskure ba, ayi mata hak'uri, sannan kuma mu d'in mun samu wani k'iran gaggawa ne babu shiri shiyasa muka daga, ammh insha Allahu zamu sake shigowa agaisa anatse dak'yau." Abba yace"Tou tou tou ai shikenan babu matsala, ga mahaifiyar yarinya nan ku gaisa da ita." Da sauri suka duk'a suna gaida Umma wacce tunda ta had'a idanu da Zaid ta saki baki Tana kallonsa mamaki fal ranta, shi ko Zaid d'in fuskewa yayi.Amaimakon ta karba gaisuwar tasu sai cewa tayi tana nuna shi da 'yar yatsa"Wannan ba Zaid d'in Najla bane.?" Abba yace cikin dakewa"Eh Zaid d'in Najla ada ba, ammh ayanzu Zaid d'in Zainabu yake, ma'ana shine wanda zai aureta insha Allah."

Cike da kaduwa Umma tace"Mene.?Habibu ban jika dak'yau ba.?Wani Zaid d'in ne zai auri Ummi.?" Abun na Umma ya mugun soya ran su Zaid yadda take cin mutuncin mijinta agabansu, Sam batai la'akari da cewa Surukai ne agabansu ba.Abba shi kansa kunya ne ya rufeshi, ji yayi tamk'ar kasa ta tsage ya afka ciki.

Bayan Junaid ya gama jera Kayan da Ummi ta barar, Sai kawai yaja hannun Zaid don bai dace su tsaya Umma na ciwa Abba fuska agabansu ba, Sosai zasu ji kunyar da yafi wanda suke ji ayanzu, Shi kansa Abban ma haka.Sake duk'awa har kasa sukai suna mishi sallama kana suka mik'e alokaci d'aya sukai gaba, Kafin su isa kofa sai ga Idrisu ya shigo gidan, Cike da mamaki yace"Har zaku wuce kenan.?"

Kafin su bashi amsa suka jiyo Umma na Fadin"Yanzu fisabilillahi Zaid kaima had'a kai zakai dasu aci amanar Najla.?ban tsammani Najla ta cancanci hakan daga gareka ba, koka manta Ummi k'anwarta ce.?To maza ina mai shawartarka in ma asiri sukai maka kaje ka wanke idanunka karka bari su lik'a maka ita." Junaid ne yayi saurin jan Zaid suka fice don so yake ya bata amsa sai Junaid d'in ya hana.

Fitarsu keda wuya Abba ya daga hannu ya kifa mata wawan mari yana huci, yace"Billahil azimu Karima idan baki Fita a idona ba saina aikata abunda ba'a so, Kije duk inda zaki shiga ki shiga ammh insha Allahu Zainab bata da mijin daya wuce Zaid kuma ke baki isa ki hana hakan Faruwa ba." Dafe inda ya Mareta cike da mamaki don bai tab'a daga hannu ya dora ajikinta ba sai ayau kuma wai duk akan Ummi, Tuni taji wani irin wutar tsanarta na kara ruruwa acikin jininta.

"Habibu ni ka mara akan wannan shegiyar yarinyar.?"
Sake dauketa yayi da wani irin mahaukacin marin da sai data ga walkiya ya gifta idanunta yace"Karki sake danganta 'yata da shegiya bayan kuwa tana da cikakkiyar asalinta, 'yarki ce shegiya Ko kin manta ne in Tuna miki.?"

. Gabanta ne yayi wani irin bugawa, Sai kawai ta zub'e akasa ta hau shure shure na borin kunya, Idrisu ya karaso wajen ransa duk ba dadi yace"Umma meyasa kike haka ne.?yanzu miye ribarki akan abubuwan tirr d'in da kike aikatawa.?Me Zainab ta tsare miki ne arayuwa da kika bi kika tsangwami rayuwarta ne.?"

Silifas d'in dake kusa da ita ta dauka ta jefeshi akai kuma ya sameshi, da sauri yakai hannu ya dafe wajen yana binta da kallon tsana, Cike da Zafi tace"Ka tashi ka bani wuri dan iska mashayi kawai har kai ka isa ka zauna kana mun nasiha bayan kai kanka aljihun baya ne.?"

Shima d'in cike da zafi yace"Dad'in abun Kaina nake cuta ba wani ba, ke kuwa rayuwar marainiyar Allah kike neman nakasawa, Umma ni d'anki ne kuma ya zama dole na fada miki gsky." Saurin taran numfashinsa tayi"Kul karka sake k'iran kanka da d'ana donni ban haifi d'a namiji ba, 'ya macece na haifa ita d'aya kuma itace Najla."

Murmushi mai ciwo ya saki don ba yau ne farau ba, sau tari hakan take gaya masa aduk sanda ya b'ata mata rai.Tashiwa yayi abinsa ya shige dakinsa ya kulle, Kana ya fada kan katifarsa ya hau cizgar kuka.

Abba na jinsu daga Falo a inda yake ta lallashin Ummi.Bai tab'a sanin cewa ashe taimakon Karima zaizo ya zame mishi musiba bane, da yasan hakan ne zai kasance da wlh babu abunda zaisa yaji sha'awar taimakon nata afarko.Mahaifin Ummi wato Dauda tun azir ya nuna masa abunda zai je yazo muddin ya aureta ammh alokacin idanunsa ya rufe, tamk'ar tayi mishi hayak'i haka yake taji awannan lokacin, har sai daya aureta sa'annan aka samu kwanciyar hankali dashi.

**********
A b'angaren Hameed kuwa ya bawa Momy hadin kai agame da batun Suhaila, ba karamin dadi taji da hakan ba, har ya soma zuwa zance wajenta, yanzu maganar da ake ciki yanzu an ajje ranar kai gaisuwanta ne had'e da kudin sadaki gaba d'aya.Yanzu Momy babu wanda tafi riritawa take kuma ji dashi acikin ya'yanta sama da Abdulhameed don yana kokarin bada goyon baya kan abunda takeso ta dadin rai.A gefen Dad d'insa kuwa sosai ya maida hankali na ganin plan d'insa ya tafi akan yadda ya tsara.Sakamakon da zai fito muddin Hameed ya auri Suhaila ba abune wanda zai yiwa Haj.Sa'ade dadi bane, so yake darasin da zata dauka ya zamo izina ga sauran uwaye masu hali irin nata.Wannan shine kudirin mai girma shugaban kasa Alhaji Aliyu Muhammad Tukura.

***
"Ummina tashi kije ki had'a kayayyakinki ayau zaki bar gidan nan." Cike da Mamaki ta dubeshi har zatai magana yayi saurin rigata"Bana son tambaya, kedai kawai kiyi abunda na saki." Jiki amace ta mik'e tana Fadin "Toh." Sannan ta fice.Tana fitowa taga Umma zaune akan benci ta zuba uban Tagumi, gefenta Najla ce wacce daga baya ta dawo har Umman ta fesa mata abunda ke Faruwa.

Najlat na ganinta ta mik'e tana kumfar baki"Shegiya macuciya, dama Surayya ta fadamun tace muddin ban tashi tsaye akanki ba sai kin rabani da duk wani masoyina, waya sani ko Hassan kika so kwacewa kika ga yafi k'arfinki shine aka koma kan shi solombiyon.?"

Kala bata ce mata ba ta wuce dakinta tana matsar kwalla, har zata bita sai ganin Abba tayi ya fito ya rufeta da dukan tsiya, sai ihu take tana kururuwa, Umma na son ta kwaceta ammh babu hali.Allah ya taimaka har zuwa wannan lokacin Hajiyar Abul basu komo gida ba, mai gadi ne da 'yar aiki kawai suke ta jin komi, suna fadin Allah ya k'yauta.

Sai dayayi mata likis tana ta jera masa Allah ya isa, ko kulata bai sakeyi ba don Najla ko amutu ko arayu ce, ko kasheta zakai bakinta baya tab'a rufuwa.Ya tasa Ummi agaba da trolley d'inta daya sai gana must go, sai kuka take tayi, ya doka mata wani tsawa"Ke kuma zaki mun shiru ko kuwa sai kema jikinki ya gaya miki.?wai akansu kike zubda hawayenki abanza.?"

Ya furta yana nuna su Umma, Su kuwa lokaci daya suka mik'e suna binsu da kallon mamaki, Umam ce tayi karfin halin cewa"Habibu ina zaka kaita.?"

"Inda kikeson taje." Ya bata amsa atak'aice.Bai sake kulasu ba yayi gaba ayayin da ummin ta bishi abaya da kaya.A booth ya saka mata kayan sannan yaja mota yabar gidan.Unguwar Mu'azu ya nufa, dama tuntuni ya yanke shawarar maidata wajen wani amininsa Mal.Baffa wanda kwarai yasan da irin zaman da Ummin take agidan.Ya tab'a neman alfarman Abba ya bashi Ummin ya rik'eta har zuwa sanda za'a aurar da ita.Toh shine yau ya kaita.

Gidan ba bak'on Ummi bane don yawancin lokaci Abba yakan aiketa gidan.Yara na ganinta suka hau murna"La ga anty Ummi! La ga anty ummi."

Cike da Farin ciki itama ta rungumesu har Innani mahaifiyarsu.Yara ne kanana don duk cikinsu hudun babu wanda yayi sa'an Ummin, kasancewar Mal.Baffa bai yi auren wuri ba.Innani nason Ummi sosai don ji take kamar itace ya haifeta.Daga ita har yara suka hau Murna jin cewa Ummin ta dawo gidan da zama. Cike da murna suka shigar mata da kaya daki.

"Zainab kiyi hakuri da yadda rayuwa ta kasance miki, Nasan muddin kika cigaba da hakuri watarana zaki ci ribarsa.Anan zaki zauna har zuwa sanda Allah zai kawo miki miji na gari, bazan matsa miki akan Zaid ba kamar yadda na Fad'a tun farko dai, ki zauna kiyi nazari sosai karki cutar da kanki, kibi abinda zuciyarki keso, sannan kuma bani son su Karima susan inda kike zaune, don Allah ki zauna anan banda yawace yawace duk da cewar nasan baki da yawo, ammh dai ki kiyaye banson ki taka zuwa wannan gidan har sai randa na baki umarnin hakan, ak'arshe kuma inason ki rik'i Mal.Baffa da mai dakinsa tamk'ar iyayenki, inason ki dunga musu kallon ni, banso inji ance kinyi kaza kinyi kaza, nasanki sarai Zainab akwai tarbiyya, don haka ki cigaba ayadda na sanki karki canza, sannan kuma ki kula da lafiyarki sosai, ki cire damuwa aranki don itace ke cutar da lafiyarki.Na gaya musu komi dangane da rashin lafiyarki kuma sosai sukai alk'awarin kula dake yadda ya kamata.in kina da magana kiyi in kuma babu to ni zan tafi saina kuma shigowa."

Kuka ta rushe dashi mai tab'a zuciya gami da kankame kafarsa tace"Abbana shikenan yanzu ka rabani da muhallinka kenan.?Zan koma rayuwa cikin mutanen da ban had'a komi dasu ba." Kukanta ya tsananta, hannu yasa yana share hawayensa kan yace cikin rauni"Zainab kiyi hakuri don Allah ya gani zuciyata bazata cigaba da daukar abubuwan dasu karima ke miki ba, Allah zai kamani da wannan laifin gobe kiyama shiyasa na dakkoki na kawoki wajen aminina, ba don bani da wasu yan'uwan bane shiyasa ban kaiki wajensu ba, a'ah sabida yardan da nayi wa Mal.Baffa Dattijo shiyasa na kawoki cikin iyalinsa, kasancewar yafi kowa nawa sanin halin da kike ciki agidana kuma ya dau alk'awarin taimakonki, Zainab ki yafemun ammh ba ason raina bane, sai don ni kaina banda yadda zanyi ne shiyasa."

Sun dad'e suna kokawa, daga k'arshe Mal.Baffa da Innani suka shigo suna lallashinsu, koda Abba zai tafi daqyar aka iya raba Ummi da jikinsa don taki barinsa ya tafi.

_Alhamdulillahi! Toh Jama'a duka duka anan na kawo k'arshen free pages, ga mai bukatar jin yadda zata k'aya sai ya biya naira dari biyu kacal ta wannan asususun bankin 0824409678, Hafsat Mustapha, access bank, saika turo da screenshot ta shaidar biya ta wannan layin 07065481260, ko kuma katin waya ta MTN ta 07065481260.Ki sani hajiyata koda kudinki saida rabonki.Karki sake SAWUN GIWA ya wuceki don ayanzu ne za'a soma wasar._

_Shin yan'uwan Abul Hassan na barinsa ya auri Najla.?_
_Ita fa Ummi.?shin Zaid na aurenta.?_
_Ina labarin Hameed.? Yana auren Suhaila.?in har yana auranta d'in to menene plans d'in Dad akansu.?_
_Wani *ALK'AWARIN JININ* ne kuma ke tsakanin Abudulhameed da MARYAM?_

_Duka amsoshin tambayoyinku na tare da *HAFSAT HAFNAN* don haka ku biyoni acikin SAWUN GIWA🖊_

_Fans zan dan huta tunda na gama free pages, duk wa'ennan free pages d'in wasa nayi ammh insha Allahu zafafun updates zasu soma starting from 14th sept Monday kenan, naku dai ku kasance ni😍_

*GARA'BASA! GARA'BASA!! GARA'BASA!!!*
_Akwai gara'basar k'ayatattun novels d'inmu guda ukku zaku samesu akan farashi me sauk'i 👉 *KUWWA DA KUWWA* na Sis Nerja'art, tare da novel d'in *SAWUN GIWA* na sharararriyar marubuciyar nan watau *HAFNAN* sai littafin *MARUBUCIYA* na fasihar marubuciyar nan *UMMUDILSHAD*_
_Za'a samesu gabad'aya cikin sauk'i da rahusa akan naira d'ari biyar (N500), ga masu buk'atar biyu daga ciki zasu turo naira d'ari ukku (N300), ga wad'anda zasuyi transfer ta bank ga account number d'in da za'a turo ta shi 0824409678, (Mustapha Hafsat Access Bank), ga kuma wad'anda zasu turo katin zasu turo *Mtn* digit ga wannan number 07013872581_
_kar kubari abarku baya acikin wannan gara'basar ko da kud'inka sai da rabonka_
*Muna maraba da masoyanmu😍👍🏻*

*#Ilove💓*
*#Anatare*
*#IWA*
*#Nagode*
_#ʰaᶠⁿaⁿᶜʸ_

    ♡

_*INA ZUWA🏃🏻‍♀️*_

Continue Reading

You'll Also Like

2.8M 163K 50
"You all must have heard that a ray of light is definitely visible in the darkness which takes us towards light. But what if instead of light the dev...
4.8M 303K 109
What will happen when an innocent girl gets trapped in the clutches of a devil mafia? This is the story of Rishabh and Anokhi. Anokhi's life is as...
7.5K 137 7
LABARIN RUGUNTSUMI: SARKAKIYAR RAYUWA, MAKIRCI DA TSANTSAR HASSADA, SHIN NA FADA MUKU YANA DAUKE DA TSAFTATACCIYAR KAUNA MARAR GAURAYE? LABARI NE NA...
10.3K 409 42
🎀 This book is written by cyficschuu_ 📍 Author's Note : - if there's any grammatical errors please tell me so I can fix it! - english is not my fi...