07

175 2 1
                                    

            ♡
                  ♡ ♡
_*🐘SAWUN GIWA...!*_
          _(The Elephant's Foot)_

  _★For How Long Will The Elephant's Foot Be Radioactive?_

 

       *FInd out💥*
     

       *WATTPAD*➖ _HAFNANCY01_

*DEDICATED TO:-Mamina (Sis Nerja'art & Yayata (Ummudilshad)*
          
_*•SPECIAL GIFT TO:-Tawar (Maman Kausy)*_
__________________________________

                *BABI NA BAKWAI♡*
___________________________________

     ↗0⃣7️⃣

.........Driving yake Kawai atsiyace ba'a Cikin cikakken hankalinsa ba, Duk inda ya gota Sai an bi motar da Kallo, Kowa na tofa albarkacin bakinsa.Allah ne kawai ya taimaki Anty Mamu dayasa bai b'ace mata ba, dake ita kanta kwararriya ce afannin tukin, Gudu kawai take ta shararawa don ta cim masa, Kowa sai bin motocin biyu yake da Kallo Cike da al'ajabi, da yawan mutane na tunanin matasa ne acikin motocin, dake Glasses d'in mai duhu ne baka iya ganin Wanda ke ciki.Shiyasa suke ganin kamar 'yan iskan yaran masu Kudin nan ne ke wasar mota agari.Ga dukkan alamun basu san sunan wani abu wai shi _DAMUWA_ ba acikin rayuwarsu, Shiyasa duniyar take musu dadi, Suke cinta da tsinke.

Nikam nace manta fa! Kudi dai Suna ya tara, ammh kwanciyar hankali da kuma koshin lfy sune dukiya, in baka dasu tofa duk kudin daka tara ya zama na banza ne.Da za'a ajje Wani Talakan da mai kudi, sa'annan ace mutane su zab'i Wanda suke ganin zaifi samun kwanciyar hankali da kuma koshin lfy, To ina mai tabbatar muku da cewa kaso 99% acikin 100% Zasu zab'i Mai kudin ne, Su aganinsu tunda ai yana da dukiya tofa zaiyi wuya ace bashi da kwanciyar hankali da Koshin Lfy.

Kuma abun ba haka yake ba, Sau tari zaka samu mutumin da komai yana dashi arayuwarsa, bai nemi komi ya rasa ba, ammh sai kaga Allah ya jarabceshi ta Wani hanyar, Zai kawo masa cikas awani al'amari na rayuwarsa dazai hana masa kwanciyar hankali, Shiyasa ake cewa ba komi bawa yake nema arayuwa kuma ya samu ba.Hakan yasa yake da matukar kyawu mu dunga tawakkali da kuma godewa Allah aduk irin halin da muka riski kanmu aciki.Mu zama masu rungumar kaddara walau mai k'yau ko mara k'yau, domin kuwa hakan ne kadai zai taimaka mana Wajen cinye jarabawarmu.Ki sani, ka sani, bawa baya tab'a rayuwa ba tare da an bud'e masa shafin Kaddara ba.Allah yasa mu dace.

Data lura cewa da gaske dai Abujan ya nufa, dasauri ta dauki Wayarta jikinta na rawa, dakyar ta lalubo layin Fareed.

Fareed da Fitowarsa Wanka kenan, ya tsaya gaban mirror yana taje gashin kansa, Sai wak'a yake rerawa irin tasu ta 'yan champions.Yana ajje comp ya nufi closet don zabar kayan da zai saka, Sai kawai yaji wayarsa ta hau ruri tana neman attention d'insa.

Karkata ak'alar tafiyarsa yayi Zuwa inda wayar yake yashe a tsakiyar gado, Da hanzari ya daga wayar ganin k'iran daga Anty Mamu ne.

"Fareed dan girman Allah duk inda kake ka hanzarta tashiwa ka biyo hanya mu ceto rayuwar Abdulhameed, Ban san abunda ya shiga k'wak'walwata har na b'ata mishi rai ba, Kafin na ankara naga kawai ya shige mota ya figeta atsiya ce, Fareed baka ga yadda yake rough driving bane, abun kaima zaiyi matuk'ar tsorata ka, My fear now is dat kar wani abu ya sameshi, oooo meyasa ma nake wannan bayanin bayan bamu da lokaci, Ka tafiiii Fareed ka shawo mana gabansa ni kuma ina biye dashi ne, I think Juz 2km ya rage in taddashi...plsss be fast..."

Ta ida magana Tana sakin wani uban kuka mai raunana Zuciya, Fareed dai baisan ya akai ba, ashe Sanda suke Kan maganar bai gama sauraronta ba ya jefar da wayar, dasauri ya jawo bak'ar jallabiyarsa dake rataye ajikin hanger ya zura, Wayarsa da key d'in mota ya kwasa da gudu ya fice, bai sanarwa kowa da fitarsa ba.In less than 3mins ya fita daga Villa ya hau hanya.

SAWUN GIWA...!🐘Where stories live. Discover now