12

94 3 0
                                    

          ♡
                  ♡ ♡
_*🐘SAWUN GIWA...!*_
          _(The Elephant's Foot)_

  _★For How Long Will The Elephant's Foot Be Radioactive?_

 

       *FInd out💥*
     

       *WATTPAD*➖ _HAFNANCY01_

*DEDICATED TO:-Mamina (Sis Nerja'art & Yayata (Ummudilshad)*
          
_*•SPECIAL GIFT TO:-Tawar (Maman Kausy)*_
__________________________________

                *BABI NA SHA BIYU♡*
___________________________________

                     1️⃣2️⃣

K'iran duniyar nan Hajiya tayi wa Najlat ammh firr taki daga waya, So take ta bata hak'uri akan abunda ya Faru ammh bata daga k'iran ba, Sosai hankalin Hajiya ya Tashi, Zura hijabi tayi da nufin zuwa gidan da kanta, bata sanar da Nana inda zata ba ammh Tuni ta gano inda Hajiyar ke shirin Zuwa.Afusace ta mik'e da sassarfa taje ta kulle k'ofar Fita gami da cire makullin ta rik'e.Ak'aik'aice Hajiyar ke kallonta kan tace"Me hakan ke nufi.?"Cike da b'acin rai tace"Hajiya wlh babu inda zaki, bazan tab'a bari ki siyawa kanki raini da wulak'anci awajen wannan fitsararriyar yarinyar ba, ai gaskiya su Ya Muhammad suka fad'i mata don haka ki bata dama taje ta zauna tayi nazari." Wani wawan marin daya sauka kan Fuskarta ne ya yanke mata magana, Cike da Zafi Hajiya ta d'aga 'yar yatsarta tana nunata dashi"Nazarin ubanki zata zauna tayi.?Khadijah Kin ganni nan, wlh bani son Fitina da tashin hankali arayuwata, akullum burina shine in wanye da kowa lfy ammh ke na lura kwata kwata baki k'wadayin hakan, Nasan bata k'yautata mana ammh ko kece aka miki abunda aka mata ayau bazaki tab'a jindadi ba, Khadijah abunda nake son ki sani shine, duk abunda ruwan zafi ya dafa to idan anyi hak'uri na sanyi ma zai dafa, abun nufi anan shine idan akayi hak'uri komi ma mai wucewa ne, baza'a tab'a dawwama ahakan ba, balle ma ni ina da yak'inin cewa surukata zata canza nan bada jimawa ba insha Allah."
"Haba Hajiya nifa agaskiya..."
"Nana zan ji miki wlh in baki rufemun baki ba, Ki k'yaleni in je ko kasheni zatai tayi ammh kinji na rantse miki zanje har gidansu in bata hak'uri kuma babu wanda ya isa ya dakatar dani, durqusawa wada ba gajiyawa bane, Maza ki bud'e mun k'ofa kan na cire hijabi in ci ubanki dak'yau." Babu yadda Nana ta iya illa yi mata abunda take so, Tana kallo Hajiya tasa kai ta fice, ji tayi kamar tabi bayanta aguje ta rufeta da duka ammh inaa! Ba zata iya ba domin kuwa mahaifiya ce.Wani uban kuka ne yaso kufce mata, da gudu ta nufi dakinta ta zub'e saman gado, Allah ya gani annabi ya shaida ita akullum muguwar addu'ar take musu bai wuci kan Allah yasa zancen auransu ya ruguje ba, don wlh abun na Najlat yayi yawa, Hassan yafi kowa sanin hakan ammh dake mak'auniyar soyayya ta rufe idonsa shiyasa yake gudun b'acin ran ita Najlat d'in. "Ya Allah ina mai sake kai kukana agareka don kai kadai kake wanda ake nufa da bukata wanda bai haifa ba kuma ba'a haife shi ba, Ya Allah in har babu alkhairi a auren dan'uwana Hassan da kuma Najlat, to ina mai rokonka da sunayenka k'yawawa wad'anda ka siffanta su acikin littafinka daka gaggauta rabasu, sa'annan ka musanya wa kowannensu da alkhairinsa." Yau an d'an ci sa'a ta nemi zab'in ubangiji, Ta bar wa Allah komi don shine yasan daidai, in ba haka ba addu'arta akodayaushe shine"Ya Allah ka kawo sanadin rabuwarsu." Ammh ayau tayi abunda ya kamata data bar wa Ar-rahmanu Ar-rahimu komi.Muma nan sai mu tayasu neman zab'in alkhairin.🤲🏻

A tsakar gidan Hajiya ta samesu sunyi kaca kaca ana aikin Nama, kodayake su Idrisu ne da Abba, Su Umma kuwa ana can daki don Tunda Najlat ta dawo da kukan haukanta suka shige daki basu sake Fitowa ba, Ummi kuma bayan Tayi sallar Zuhur Abba yace ta kwanta ta huta abunta, dake yanzu d'in sosai yake sa idanu akan al'amuranta, ko kadan baya bari su umma su matsa mata.Abba na ganinta yayi saurin dauraye hannayensa yana fad'ad'a fara'arsa, Su Idris daga inda suke suka duk'a har k'asa suna gaisheta, Ta amsasu cike da sakin Fuska.Abba ya nufota suka shiga gaisawa gaisuwa irinna surukan da suka san darajar juna.Daga nan suka rankaya Zuwa ciki ya mata iso a Katafaran Falon.Sa'annan ya nufi dakinsu Umma don sanar masu da Zuwanta duk da cewa kwarai yasan sun ji muryarta ammh suka dake.

SAWUN GIWA...!🐘Where stories live. Discover now