TUNATARWA

141 3 0
                                    

Hello watpaddians! Fatar kuna lfy?
Sorry nasan ban k'yauta ba da yanke muku jindadin wannan littafin da nayi but reason with me, ina sone nasan masoyana na hak'ik'a shiyasa ammh i promise y'all nxt littafina mai suna 'KABILARMU BA DAYA BANE' kai tsaye zaizo muku ne ak'yauta, ko chikini bazaku biya ba insha Allah.

But for now show me some love by paying for diz book 'SAWUN GIWA' ,ki biya naira dari biyu kacal ki karanta cikin aminci ta wannan asusun bankin 0824409678, Hafsat Mustapha, access bank, ko kuma katin waya ta MTN ta 07065481260.Idan kuma ya fita har kika karance ba tare da kin biya ba, babu damuwa na yafeki in har halin biyan ne baki da.Allah rufa mana asiri (Ameen🤲🏻).Sai ki turo da screenshot ta wannan WhatsApp line d'in 07065481260.Nagode Anatare🙌🏻_

        
.......K'ARIN D'and'ano........

"Ummi kwana biyu kin gujeni ko tambayata ma bak'ya yi."
Cike da kunya tace"Laa Anty Yasmin wannan ba gaskiya bane, Ki tambayi Nana kullum sai nayi mata zancenki Allah ne dai kawai bai bani ikon zuwa ba sai yau." Kafin Anty Yasmin tace wani abu sai ji sukai an doko sallama cikin zazzak'ar murya.

Saurayin ya bayyana cikin shiga ta kananun kaya wanda suka zauna fes ajikinsa.Mutum ne k'yakkyawan gaske, Kamarsa sak na mahaifinsa sai dara daran fararen idanuwan mahaifiyarsa daya dakko, Farinsa kalar na hutu ga fatarsa da take amurje, Suman kansa baki sidik kuma anannad'e kamar na larabawa, Doguwar Fuska gareshi mai dauke da yalwataccen gashin gira dana idanu, gazar gazar, Hancin nan nasa madaidaici, zirr dashi kamar murfin biro, wanda yayi daidai da kakkauran labbansa pink masu matukar daukar hankali.Hak'oransa farare ajere tsaf gwanin ban sha'awa.Ma'abocin barin saje wanda ya had'e da tsararren guntun gemunsa.Hakan ya kara fidda fasalin fuskarsa.

Mutum ne wanda yayi rik'o da addini, wayewa da kuma aji.Mutum mai sanyi da hak'uri, mara son b'atawa mutum, ga ladabi da biyayya.Kakaf shine ya gaji duka iyayensu don duk kowannensu ya had'a halayen wannan nagartaccen saurayin dana ambato.

Zuba mishi idanu sukai cike da sha'awarsa, da mamaki ya ware hannaye yana fadin"Hey guys wannan kallon kurillan fa.? Nasan Hasino ya had'u ta ko'ina ammh ku d'an dunga yi kuna ragewa kar watarana ku cinyeni musamman wancan mai idanun magen."

Ya ida magana yana mai nuna Ummi da 'yar yatsa gami da shafa tacaccen gemunsa yana murmushi, ya zub'e saman kujera.Dariya suka sanya duka,banda Ummin wacce sunkui da kai kasa tayi tana murmushi, ta d'an daki cinyar Nanar dake kusa da ita tace ahankali"Ashe Ya Abul ya dawo shine ko ki gaya mun.?"

"Shekaranjiya suka diro kasar wlh, dazun hira ce ta dauke mana hankali shiyasa na manta ban gaya miki ba, afuwan Sahiba." Ummi ta harareta.

Ita kuwa Anty Yasmin cewa tayi"Hasino kai dai mai hali baya fasa halinsa, Tuntuni na maka waya nace kazo it's urgent ammh ji sai yanzu kake zuwa, Allah sai ince na fasa ma."
Nana tace"Anty ni ban ma san gidanki zaizo ba ai dana jira munzo tare."

Wani kallon raini ya watsa mata kana yace"Ke dawa.?hala ni sa'anki ne da har zamu jera tafiya tare.?" Dariya Ummi da Anty Yasmin suka saki, Anty tace"Dadina dakai Hasino akwai jarabar son girma, Ke kuma Nana akwai shisshigin da babu Farin jini." Babu wanda ya tankata cikinsu, Ummi ta zamo kasa cikin sanyi tace"Ya Abul barka da yini, Fatar kun dawo lfy.?Allah ya karba ibadah."

Dago kai yayi daga danne dannen wayarsa da yakeyi ya watsa idanunsa kan Fuskarta, ji tayi bazata iya jure kallon k'wayar idanunsa ba sabida wani irin k'warjini taji yayi mata, lallausar murmushi ya saki yana Fadin" *ZEEYNAB* bazan amsa ba, anan ne yakamata ki gaisheni.?kowa da kowa yaje har gida mana barka da dawowa ammh banda ke." Dayake su Najla da umma tun aranar da suka dawo suka shiga gaishesu.

"Kai Hasino komi naka sai ka had'a da wani k'ak'ale aciki.Ana Zainab meye kuma wani Zeeynab.?" Anty Yasmin ta furta tana dariya.

"Wai Anty Yasmin yau lafiyarki kuwa da kika tasani gaba haka.?" Turbune Fuska tayi tana maka mishi harara"Kadan ma ka gani, Ka gode Allah ma ban zaneka da b'atamun lokaci da kayi ba." Kasaitaccen dariya mai burgewa yayi yana Fadin"Haba dai duka kuma sai kace wani d'an yaro, ay tuni na girmi nan."

Suma dariyan ne suka tayashi, can ya sake duban Ummi yace"Amarya baki bani amsar tambayata ba, nace meya hanaki zuwa yimun barka da zuwa.?" Gabanta ne taji ya bada rass, su Anty Yasmin kuwa jinjina abin sukai aransu.Ummi tayi murmushi tace"A'ah Ya Abul amaryarka tana can gida." Yace"Ai dake da ita d'in duk daya ne awajena." Anty Yasmin tace"No bafa daya suke ba, Najla daban, Ummi daban." Nana ta kashe mata ido daya tana Fadin"Hakane antina fada masa gaskiya dai." Filon kujera ya dauka ya wurga mata yana fadin"Khadijah zanci gidanku in manya na magana kina saka musu baki, an tambayeki ne.?"

Da taga abun nashi na neman girmama, sai kawai taja baki tayi shiru don ta sani sarai Abul bayason raini ko kadan.Ummin ce tayi mishi bayani da bakinta cewa ta koma gidan wani dan'uwan babanta anan Unguwar Mu'azu.Daga shi har Anty Yasmin hamdala sukai kuma sosai suka tayata Farin cikin canjin rayuwar data samu.

Abul na Fira dasu sama sama ayayin da yake chat da Najla, Fad'a suke sosai don yace muddin bata sauya ba tofa ta manta da batun aurensu, ita kuma sai raina masa hankali take don aganinta tunda auren ya matso ai bazai iya sa afasa ba.Kuma ai shi d'in ma bazai tab'a iya rayuwa babu ita ba.Ran Abul in yayi dubu toya b'aci, gashi ayau su Ya Muhammad suka had'u sukai mishi tatas akanta, su kace muddin bai dau mataki akanta ba tofa su zasu dauka ne.Hakan ne ya tunzurashi nason yaga ya tsoratata.

Anty Yasmin ta dubeshi tace"Kaga Hasino ba k'iranka nayi nan ka koyamun yadda ake tab'e tab'en waya ba, Na k'iraka ne don ka Fadi mun shoe size da kuma bra size na amaryarka, an gama had'a komi na kayan lefe su kawai suka rage, an k'iraka kuma ka zauna kana shirmen banza." Ta karashe maganarta ah kufule.Hasino sunansa ne na kwallo.Murmushi ya saki as usual wanda yin hakan ya riga ya gama bin jikinsa sannan ya shafa kai yana Fadin"Am sorry, d'an bani 2mins."

Ya cigaba da chatting d'insa, ita kuma tashiwa tayi ta shiga cikin daki don dakkowa Nana sak'on Hajiya wanda garin magani ne ta samo mata na maganin diabetes.Tambayar Najla yayi"Ke tell me ur shoe nd bra size am waiting." Cike da rashin kunya ta bashi amsa"Anki afad'a d'in, bayan ka gama cin mutuncina shine kuma kake tambayata size d'in shoe da bra.?ina ce ko kai ne ka gama fadi yanzu cewa bazaka aureni ba.?Then why asking again.?" "K....." kawai ya aika mata dashi sannan ya kashe data ransa duk ab'ace. Anty Yasmin ta Fito da Sak'on Hajiyar sai kuma samfur d'in wasu takalma masu k'yan gaske different sizes, zubasu tayi akasa su Nana nata yabawa k'yansu.

"Nawa sizes d'in.?" Ta tambayeshi.
Yace"Taki gayamun, kawai kisa kowani size inma bai mata ba ita ta sani." Girgiza kai tayi tana Fadin"Yayi k'yau." Ta kalli Ummi wacce sam bata ji dadin abunda Najla take yi, Anty tace"Ummi shin kin san shoe size d'in yar'uwar taki.?"

Cike da sanyi tace"I think ni da ita muna saka size d'aya don itama bata da wani girman kafa, muna sanya 38 ko 39." Kansa akasa ammh ya kasa kunnuwa yana sauraronta.Anty yasmin ta duba takalman ta zak'ulo sizes 38 da 39.ta kawo gaban Ummi ta ciro kowanne kafa dadd'aya ta dire tace"Gwadasu mu gani, in sun miki tou which means itama zasu mata d'in kenan." Ahankali ta zura kafarta ana size 39 ruwan hanta, Abul na kallonta ammh kasa kasa yake kallon, aransa yace"Hasbunallahu! Ji yadda yayi mata k'yau sosai." Su Anty Yasmin ma "whaooo" suka ce ganin yadda yayi d'as akafarta kamar don ita akai.

Dayan size d'inne bai shigeta ba, sai Anty tace"Da gani dai 39 d'in dai shine zai fi fitting, dama wa'ennan samples ne na kwaso wajen kawata Maryam, don awajenta ne zamu siya takalman, zuwa gobe zanje sai in zab'i sizes 39 d'in ko kuma babban 38 don nasan zaiyi.Yanzu ya size d'in twins nata suke.?"

Sosai abun ya basu Kunya da dariya har shi d'in.Da sauri ya tashi ya fice waje.Suka rakashi da dariya.Wannan ne kuma ummi bata sani ba, ammh sai tayi k'ok'arin kwatanta yadda mamunan Najlan suke don kuwa tafi Najlan nonuwa nesa ba kusa ba.

Basu suka bar gidan ba sai after 6, Daqyar suka samu Abul ya kwashesu amotarsa, Ya soma dropping Ummi sa'annan suka wuce gida....................✍️


'''KARKI MANTA KI BIYA KI KARANTA CIKIN AMINCI'''

*HAFNAN💜*

SAWUN GIWA...!🐘Where stories live. Discover now