SHIGO DAGA CIKI...

138 1 0
                                    


Haba wattpadian! Ana ta barinku abaya fa? Hurry and get urself registered, juz 200naira ne kacal zaku nuna soyayyarku agareni.

.....KARIN Dand'ano.........

  ...Fareed na lab'e jikin kofa yana sauraronsa kuma duk yaji tattaunawar tasu, Sanda Abul ya soma wayar da Brave, Shi Fareed na kwance ya runtse ido kamar yana bacci, To gudun kar yaji tattaunawar tasu ne yasa ya shige bandak'i. Yana shiga Fareed ya mik'e ya lab'e.Sai daya ga ya kare wayar ne shine ya koma da sauri ya kwanta.

Abul na fitowa ya shiga Kai da komo acikin bedroom, duk Fareed na kallonsa ammh shi sam bai da masaniyar hakan, azatonsa yayi bacci.Sosai tausayin Coachy d'in nasa ya kanainaye zuciyarsa, shi tsoronsa daya kar yaje shi kadai wani mummunar abun ya sameshi in har ya kasance ransa akeso.

Tabbas yakamata yayi Wani abu akai, Zai sanar dasu Alhaji Abbi idan yaso sai su bishi abaya ba tare da saninsa ba, ammh Kuma ai Brave ya bada sound warning akan karya kuskura ya sanar da kowa ko kuma yayi k'ok'arin had'a kai da jami'an tsaro, anya bai kamata ya tayashi bin tsarin nasu ba don tsiratar da rayuwar Ummin.?

Kamata yayi kawai ace ya tayasu da addu'a ammh bawai ya sanar dasu Abbi ba gudun kar asamu matsala.

Yana Kallo aka sake k'iran Abul, komawa yayi bandak'i da sauri ganin bak'uwar lamba, sai dai wannan karon Fareed bai yi yunkurin bin bayansa don lab'ewa ba.

Ogan Braves ne ya k'irashi da wani Layi ammh sai ya b'oye, ya nuna 'private number'. Yace"Sorry mantuwa nayi ban gargad'eka kan karka sake ka sanar da kowa naka zancen da mukai ni dakai ba don ana iya samun munafikin da zai je ya had'a kai da jami'an tsaro, Hassan karka ce zaka mana wayau ko dabara don mun wuce yadda kake zato da kuma tunani."

Sosai Abul yaji zafin maganganunsa ammh ya zama dole ya saukar dakai kasa don ya lura mutanan nan ko kadan basu da digon imani, Tabbas suna iya aikata duk abunda suka ce in har ya kuskura ya jawo musu matsala.Zai yi yadda sukeso insha Allah in har hakan ne kadai zai iya kubutar da Ummi daga hannunsu, kai inma ta kama ransa ne zai iya sadaukarwa, burinsa kawai su saketa ta tafi ba tare da an tab'a lafiyar jikinta ba. Sai dai yadau alk'awari in har da sauran kwanakinsa agaba, to insha Allahu koma wanene keda hannu acikin wannan al'amari sai ya tabbata yayi regretting.

"Nace maka naji insha Allahu ba za'a zamu wata matsala ba."
"Good..kuma kafin ka taho ka tabbata aljihunka tayi nauyi domin zamu fanshe kudin ciyar da matarka da mukai, and again banda african time, Na tsani jiran mutum Sai dai shi yama jirani, K'arfe 10 d'in da muka ajje zaka Fito, Zan turo wani ya daukeka ah NARIYA, k'arshenta kafin akai railway, Saina k'iraka." Dif! Ya katse.

    ******

Tunda aka kai Najla take ta rusar kuka, K'arin bak'in cikinta ma bai wuci irin dakin da aka sauketa wai amatsayin nata ba, ciki da Falo ne wanda basu da wani girman kirki, domin Kafcecen gadonta kadai ma daqyar aka samu ya shiga, duk ya cinye daki, dressing mirror d'inta ma yazo gab da gab ne da bakin gadon.

Wadrope kuwa shi ba'a ma maganarsa don bai samu karbuwa ba, sai aka gyara dakin k'anwar Zaid wato Ruqayyah, aka keb'anceshi Kafin asan abunyi.Akwatinan lefenta da kuma wanda Abba yayi k'ok'arin had'a mata, akwatuna bibbiyu ya siya ma kowacce, daga Ummin har ita, sai ya zuba lessussuka, Shaddoji da kuma atamfofi aciki daidai k'arfinsa.Daqyar aka matse wuri aka jere akwatunan.Burin da taci akan jera kayan dakinta ah tsararre da kuma isasshen wuri, sai gashi alokaci daya komi ya wargaje, an dakushe mata dogon burinta ta k'arfi da yaji. Saitin kujerunta an samu three seater ya shiga, sai kuma one one, ammh mai two seater bai samu waje ba, shima d'in dakin Ruqayya aka kaishi ajiya.

.Ruqayya nata murna ta samu kaya daga sama, don alk'awari tayi saita rakarkashe kujerar dak'yau, haka ma Wadrope kafin adaukeshi saita moreshi, yadda kasan dai bakinsu daya da dan'uwanta, don duk wani nasa babu wanda ke qaunar Najla sabida irin wulak'ancin da tayi masa abaya.

SAWUN GIWA...!🐘Where stories live. Discover now