04

189 4 0
                                    

        ♡
                  ♡ ♡
_*🐘SAWUN GIWA...!*_
          _(The Elephant's Foot)_

  _★For How Long Will The Elephant's Foot Be Radioactive?_

 

       *FInd out💥*
     

       *WATTPAD*➖ _HAFNANCY01_

*DEDICATED TO:-Mamina (Sis Nerja'art & Yayata (Ummudilshad)*
          
_*•SPECIAL GIFT TO:-Tawar (Maman Kausy)*_

_Huntynah kina da bukatar karanta littafin nan don haka karki wuceshi😉_
__________________________________

                *BABI NA HUDU♡*
___________________________________

     ↗0⃣4️⃣

.........Haj.Sa'adatu Ahmadu shine asalin sunanta, iyayenta 'yan Bwari ne, su biyu ne kacal awajen iyayensu, da ita da wanta Alhaji Aminu Ahmadu.Iyayensu nada d'an rufin asiri daidai gwargwado wanda hakan ya basu damar kula da tarbiyan ya'yan nasu har suka tsaya akan tsayin daka na ganin yaran sun samu ingantaccen ilimi har zuwa matakin jami'a.

Sa'ade na had'a degree d'inta bata je gaba ba, Aminu ne ya tafi hada masters d'insa don kusan atare matakin karatunsu yake tafiya, Tun tana 'yar kankanuwarta take da hazaka sosai shiyasa kusan alokaci daya suka shiga makaranta ita da wan nata Aminu, abunda yasa mutane ke ganin kamar karatunshi baiyi sauri ba kenan don ba'a sakashi makaranta da wuri ba.

Sa'ade nada hankali da nutsuwa sosai ammh matsalarta guda, ta dorawa kanta son abun k'yal kyali, tana burin ta kasance cikin jerin matan da ake damawa dasu aduniya, Ya zamana ko ina ta shiga sai an nunata, aita bata girma tana jin kanta asaman nan.

Ta hadu da president Aliyu Muhammad Tukura ah Base university inda ta kare karatunta, shi kuma mutumin Kazaure ne, Hakika sunso juna ammh matsalarta guda daya dashi, shima nashi iyayen irin nata ne, wato ba wasu masu mukami bane, Tanason Aliyu sosai kuma sunyi alkawarin aure. Bayan sun kare karatunsu dukah, ya dauki tsawon lokaci yana neman aiki ammh shiru, duk wani aiki na rufin asiri da idan ya samu sai tace kar yayi accepting, Allah ya kiyaye yayi kaza da kaza ai ya wuce wannan ajin, Su d'an k'ara hakuri aiki mai tsoka nanan tafe, kwata kwata bata damu da neman nata ba sai nashi, wato in Alu ya samu ai za'ace ga matar Alu nan😃.

Sannu ahankali ta soma cusa masa ra’ayin shiga politics, Tun bayason zancen har ya soma saurarenta, yazo yayi na’am, ya fito takarar neman kujerar chairman na local gvt nasu, Alhaji Aminu ne ya tsaya masa alokacin campaign dake harma ya soma aiki da INEC, yana cikin *INEC COMMITTEE'S*

Cikin ikon Allah yaci zab'e, Haj.Sa'ade kamar zata zuba ruwa akasa tasha don murna na ganin wasa wasa fa har burinta ya soma cika, babu jimawa sukai aure, bata cika shekara ba kuwa Allah ya albarkaceta da haihuwar Maryam wacce ake kira da Mamu.

Daga nan fa shikenan Allah yayita daukaka Aliyu, daga wannan kujerar zuwa na samanta, Suka sake samun haihuwar Abdulhameed wanda yafi tsaya musu arai, suna matukar sonsa sosai, sai Fareed wanda daga shi bata sake haihuwa ba ta juya mahaifarta wai ita alan dole batason ta tsofe da wuri.

Bayan wasu shekaru masu yawan gaske Aliyu Muhammad ya fito takara yana neman kujerar shugabar kasa gabaki daya, Sosai hankalinsa ya tashi na ganin yana da opponents da yawa, ammh sai Haj.Sa'ade tayi ta kwantar masa da hankali na cewa ai gasu da Dan'uwanta Alhaji Aminu, insha Allahu zai tsaya masu, dake ayanzu shine INEC chairman.

Sai dai kuma ta bashi sharudd'a wanda muddin idan ya amince tofa insha Allahu tayi alkawari zai samu kujerar da yake nema, ba tare da wani dogon Tunani ba yace ya amince, Tace idan ta shige masa gaba har ya samu kujerar shugabar kasa tofa komi zai dawo karkashin ikonta ne hatta dashi kansa, Mulkin ne dai zaiyi ammh ita zata mulki gidanshi, zaya zamana duk wani hukunci da idan ta zartar tofa daga shi har ya'yansa dole ne su karbeshi da hannu bibbiyu babu korafi, sa'annan kuma babu zancen kishiya, ita kadai ta isheshi rayuwa.Tace idan ya aminta toh shikenan, idan kuma yace a'ah sai ta dakatar da Yaya Aminu da kokarin da yake na ganin ya taimakeshi.

SAWUN GIWA...!🐘Where stories live. Discover now