14

115 3 0
                                    

     ♡
                  ♡ ♡
_*🐘SAWUN GIWA...!*_
          _(The Elephant's Foot)_

  _★For How Long Will The Elephant's Foot Be Radioactive?_

 
  *FInd out💥*
     

       *WATTPAD*➖ _HAFNANCY01_

*DEDICATED TO:-Mamina (Sis Nerja'art & Yayata (Ummudilshad)*
          
_*•SPECIAL GIFT TO:-Tawar (Maman Kausy)*_
__________________________________

                *BABI NA SHA HUDU♡*
___________________________________

                     1️⃣4️⃣

.
..Ummi ce durqushe kusa da kafafun Abba duk sun zuba uban Tagumi suna kallon tulin kudin dake gabansu, kudi ne rututu har dubu goma biyar.Madam Deborah ce tazo har gida ta sake cin mutuncin Ummi kamar bata tab'a saninta ba, duk da kasancewar Abba ba mafadaci bane ammh ayau ya tanka mata ganin irin kazafin data kullawa Ummi wai tana biye-biyen maza bata son zuwa shago shiyasa ta koreta, sa'annan kuma ga raguwar kudinta nan dubu sha biyar ta kawo.Sosai Mutane suka cike gida aka shiga tsakani don kiris zuciya ta kusa sa Abba aikata abunda bai dace ba akan Madam Deborah, kuma yaci alwashin sai ya hadata da hukuma akan mummunar kazafin da tayi wa 'yarsa.Mutane ne suka dunga tausarsa kuma yawancinsu sun bada sheda ta gari akan ita Ummin, hakan ne yadan sanyaya zuciyar Abban.Mutane suka tisa k'eyar Madam Deborah zuwa waje.Allah ya taimaka awannan ranar su Hajiyar Abul basa gida duk sun Fita kai ziyara balle su ji kalar husumar data tashi agidan surukan nasu ayau kuma.Al'amarin nan ba karamin dadi yayi wa Umma da Najlat ba ganin anci mutuncin Ummi agaban jama'a, ji suke tamk'ar su zuba ruwa akasa su sha don murna.Abba na lure dasu ammh sai ya batsar, ya kasa kunni yana sauraron kukan da Ummi ke rerawa cikin karamin sautin da bata fita sosai, ba kadan ba kukan nata ke masa ciwo, sai dai ya kasa wani yunk'urin lallashinta don shima karan kansa ayau kadai yana bukatar alallasheshi, ammh ina yake da mace ta gari wacce zata tsaya tayi mishi hakan.?sai dai ma ta cika ita madam Deboran da sha tara ta arziki don aganinta ta burgeta da cin mutuncin mijinta da tayi.Allah ya kyauta shine abunda ya iya kubcewa daga bakinsa.Duban Ummi yayi sannan yace"Zainab kibar wannan kukan ya isa hakanan kinji.?Na fad'a miki tun rannan ko da'ace duka mutane su sun yadda wai kina biye biyen mazan, tofa Ni Habibu bazan tab'a yarda ba don nasan irin tarbiyan da aka baki, karki damu Zainab na gaya miki nan da d'an kank'anin lokaci zan 'yantaki, insha Allahu zan sadaki da inda ake tausayinki, inda za'a soki akuma mutuntaki da kuma darajaki."Kuka ta fashe dashi mai daga hankali tana Fadin"Nagode Abbana! Nagode Allah ya biyaka da gidan Aljannah." Hannu yasa yana dauke guntun hawayen bak'in cikin daya d'an shatato masa yace"Ameen uwata..zan kwashi kudin nan in had'asu dana wajena in siya miki kayan daki ammh in kina da bukatar wani abun ne sai ki gayamun inyaso na ware kadan in baki aciki ki biya bukatar taki." Shiru ta masa tana juya maganar aranta.Umma da Najlat dake lab'e ajikin k'ofa, wa'enda dama jira suke suji yadda za'ai da kudin, jin abunda yace ne yasa suka fito wuf kamar an jefosu, Umma tace tana tafa hannayenta"Habibu ban ji abunda kace dak'yau ba don Allah k'ara maimaitawa."Wani irin wawan kallo ya watsa mata wanda yasa hanjin cikinta kadawa sannan yace"Ay ko baku yi lab'en ba dama ina da niyyar taraku in fesa muku abun Farin cikin dake shirin samun 'yata Zainab, wato abun nufi anan shine 'yata Zainab tayi miji, mijin nunawa sa'a, nagartacce, mutum mai tsananin sonta, mai tausayin irin halin rayuwar da take fuskanta ayanzu." Jan gwauron numfashi yayi sa'annan ya cigaba da magana dauke da k'yakkyawan murmushi saman fuskarsa"Albishirinku! Na shirya aurata ga wannan nagartaccen namijin rana d'aya da naki ke Najlat."

Jin zancen sukai tamk'ar saukar aradu, Kamar hadin baki sai suka tsinci kansu da sanya hannu suna mai dafe k'irji, Najlat ce tayi k'arfin halin cewa cikin k'askantar da murya"Abba kana nufin Ummi zatayi aure harma rana d'aya da nawa.?" Fad'ada fara'arsa yayi yace yana kallonta"Kwarai kuwa Malama Najlat, Ummi Zainabuna aure zatai insha Allahu, kuma rana guda da naki, Kamar abun ya shayar daku madarar mamaki ko.?Kuna mamakin ta yadda abun yazo akurarren Lokaci babu wani shiri hakane.?" Umma ce tayi saurin taran numfashinsa"Ni bama wannan ne abun mamakin ba, mamakina shine yaushe har ta samu mijin bayan kowa ya sani ko mashinshini bata dashi, ban tab'a jin wani yayi sallama yace wurinta yazo ba, to in hakane a ina ne ta samu mijin.?dan gidan uban waye shi.?" Tayi tambaya tana zazzaro idanu kamar zata dakeshi.Hakan da tayi ba karamin dariya taso ba Abba ba ammh sai ya cije yace"Karima ba sai kin dakeni ba, Ki kwantar da hankalinki insha Allahu nan da karfe hudu zai shigo gaishemu, anan ne zakui gamo da nagartaccen wanda wata tayi rashinsa." Daga Umma har Najlat sai kallon juna suke don sun rasa gane inda zancen nasa ya dosa, sosai ya lura da halin rud'anin da duk suka shiga, hakan kuwa ba karamin dadi yayi masa ba, alokaci d'aya ya mik'e gami dasa hannu ya kwashi kudad'en dake gabansa ya watsa a aljihu Kafin ya nema ya rasasu don karamin aikin Karima ne ta laluba ta kwashesu tas kuma idan anyi tambaya tace watakila mashayin gidan ne ya wawushe, idan kaga yadda take cin mutuncinsa sai ka rantse da Allah ba ita ta tsugunna ta haifeshi ba, kai Karima dai murdadd'en hali gareta gata nan dai ne, Ta riga ta gama nannad'e tabarmanta agaban manzon Allah.

SAWUN GIWA...!🐘Where stories live. Discover now