08

151 4 1
                                    


♡ ♡
_*🐘SAWUN GIWA...!*_
_(The Elephant's Foot)_

_★For How Long Will The Elephant's Foot Be Radioactive?_


*FInd out💥*

*WATTPAD*➖ _HAFNANCY01_

*DEDICATED TO:-Mamina (Sis Nerja'art & Yayata (Ummudilshad)*

_*•SPECIAL GIFT TO:-Tawar (Maman Kausy)*_
__________________________________

*BABI NA TAKWAS♡*
___________________________________


↗0⃣8️⃣

"Fareeeeed!!!"
"Innalillahi! Wallahi Ka kasheshi, duba ka gani Allah baya numfashi."

Anty Mamu ce ke wannan sambatun Cikin gushewar Hankali, Kwata kwata bata da Kuzarin iya karisawa Wajen motar. Fareed Wanda shima hankalin nasa amatuk'ar tashe yake, Shine yayi k'arfin Halin nufar inda motar take don fiddoshi tare da Taimakon Wasu tawagar Mutane Wa'enda yawancinsu Suma Matafiyan ne, Tsaida ababen hawansu sukai alokacin da Abun ya faru.

Bayan an fiddoshin, aka shimfid'eshi Flat ak'asa, Babu alamun gurjewa atattare dashi sai dai numfashin daya dauke masa, hakan ya taimaka Wajen ayyana cewar da gani rai yayi halinsa ne azukatan Mutanen Wajen.

"Abdulhameed dan girman Allah ka tashi wlh bazan sake b'ata maka rai ba..."

Mamu ta furta cike da firgici, sai ayanzu ne ta samu Wani k'arfin yunkurawa ta nufi inda yake yashe da gudunta, da hanzari Wasu suka hana mata samun kusanci da inda yake.Fareed ma tsabar Tashin hankali kasa fidda sautin kukansa yayi, Sai Wasu Zafafun hawayen da suke ta gangaro masa babu Shiri.

Wani acikin Mutanen yace asamo ruwa don yana Tunanin kamar Somewa yayi.Da azama Fareed ya mik'e daga durqusan da yayi agaban Hameed ya nufi motarsa da d'an gudu gudu don baya rasa Ruwan gora aciki.

Gabaki d'aya Anty Mamu ta gama ayyanawa Kanta cewa babu rai ajikin Hameed Kawai b'ata Lokacinsu Zasuyi.Ta dora laifin Mutuwarsa kacokam akanta.Magana take kamar Wata zautacciya, Kun san Halin Mutanenmu na yanzu kamar jira Suke Wani al'amari ya afku Sai asamu na Watsawa duniya ta gani.Balle kuma abunka da al'amarin ya'yan manya, an samu na tsegumi benci da benci.

Ana ta batun ceton rai ammh Wasu ta Video coverage da daukar hotunar Hameed kawai suke tayi, hatta da maganganun Mamu Sun kwashe.Kowa sai mamaki yake da jin cewa musabbabin Shiga Kuncin Hameed ta dalilin Momy ne, dake Mamu Sai zuba Zance take tayi bata san inda hankalinta ya tafi ba.

"Momy kizo ki gani, ina fatar ayau Zaki zuba ruwa ak'asa kisha don murna Tunda Hameed yabar miki duniyar, Sai ki haifo Wani Abdulhameedun ki aura masa Suhailah domin kuwa Wannan Allah ya k'arbi abunsa."

Fareed ne ya toshe mata baki yana Fadin"Haba Anty Mamu meye haka?Kin san me kike fad'a kuwa?Duba can kiga ga Abdulhameed ya farfad'o, dama ni nasan bai Mutu ba, Suma yayi, gashi can ya dawo don ya fuskanci Sauran yak'in dake jiransa, sai dai Wannan karon bazan barshi shi kadai ba, Zanyi tarayya da kuma gwagwarmaya dashi acikin Wannan yak'in, ya Zama dole mu kwatarwa kanmu 'yanci awajen Momy."

Alok'aci d'aya tayi tsit da kukanta, Ta koma hayyacinta, idanunta biyu suka sauka akan Hameed Wanda ke zaune akasa mutane sun d'an zagayeshi, da gaske yana raye don two eyes d'insa ita suke kallo.

Cike da Farin ciki ta ture Fareed, da azama ta mik'e ta nufi inda yake, Tayi k'okarin rab'awa Cikin jama'ar don Samun kusanci da k'anin nata.Sai gani tayi ya d'aga mata hannu daya, Cikin muryar da bata fita yake Fadin"Dakata daga Wurin! Karki kuskura ki karaso kusa dani, ashe kema d'in daya kike da ita ban sani ba Sai yau, k'aryar so kike ta gwada mun Ni kuma na sakankance kamar Wawa ina biye miki, Wai ni aganina yar'uwata tana qaunata ashe abunda ban sani ba, bakinku d'aya, daga yau banaso ki sake kusantoni, Maryam kema ki fita daga rayuwata!."

SAWUN GIWA...!🐘Where stories live. Discover now