KAMA DA WANE....(Completed)

Oleh Seemahwrites

13.2K 1.8K 210

even though they look alike that doesn't mean they should have same goals, their life is filled with regret... Lebih Banyak

chapter 1
chapter 2
chapter 3
chapter 5
chapter 6
chapter 7
chapter 8
chapter 9
chapter 10
chapter 12
chapter 11
chapter 13
chapter 14
chapter 15
chapter 16
chapter 17
chapter 18
chapter 19
chapter 20
chapter 21
chapter 22
chapter 23
Apology
chapter 24
chapter 25
chapter 26
chapter 27
chapter 28
chapter 29
chapter 30
chapter 31
chapter 32
chapter 33
chapter 34
chapter 35
chapter 36
chapter 37
chapter 38
chapter 39
chapter 40
chapter 41
chapter 42
chapter 43
chapter 44
chapter 45
chapter 46
chapter 47
chapter 48
chapter 49
FINAL
Trailer

chapter 4

303 35 0
Oleh Seemahwrites

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
  🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
                          BATA WANE👩🏻‍🦱
   💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *Na*
        *UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Special gift to *Muhammad Karim*
       *And Fenarh matar Soja*

04👯
Ranshi a mugun bace ya tako har zuwa wurin da take tsaye Yana kallon ta cikin Ido, tuni jikin ta ya fara kyarma don wani kwarjini yayi Mata sosai ya cika Mata Ido.
"Ban taba dukan wata ya mace ba, kada ki saka na fara a kanki wallahi ki kiyaye ni Zarah"

Saida ta tausasa murya kaman zatayi kuka tace
"To Dan Allah ka sake ni na koma gurin iyaye na, wallahi na gaji bazan iya zaman talauci ba mutuwa zanyi"

Saida yayi 'yar qaramar dariya sannan yace
"Ai auren mu na zobe ne babu saki, abunda hausawa suke cewa mutu ka raba, duk inda zanje tare dake zan tafi komi dadin wurin komi wahalan shi kabari ne kawai ba zamu shiga tare ba shima kawai zan barki ne ki kulamin da yara na.

Kin riga kin dasa min sonki a cikin zuciya ta ya zamo Miki dole kiyi haqurin zama dani, lokacin da Zaki aure ni ma ai haka kike fadamun idan babu ni mutuwa zakiyi Kuma gashi yanzu kina neman rabuwa dani dan haka idan ban sake ki bama nasan babu mutuwan da zakiyi"

Ya shafo fuskar ta cikin kula murya can qasa yace
"Bazan rabu dake ba mi alma(my soul) duk wacce ma zata shigo cikin gidan Nan haka zata same mu, bazan yada ke ba please ki qara haquri wata rana sai labari komai zai wuce kaman ba'ayi ba"

Raurau tayi da idanun ta qolla na taruwa a ciki, tana son zama da Sa'eed Kuma tana kishin sa sosai Amman ba zata iya zama dashi a cikin talauci ba
"Please kayi haquri ka sawwaqe Mun na koma gidan iyayena na zauna idan kana so ma zan iya bari maka 'ya'yan ka a Nan please set me free"

Zarah tana bashi takaici, a rayuwan ta wato ita Bata san qaddara ba bare ta rungume shi ta samu dacewa na duniya da lahira, no ita kawai aji dadin duniya shikkenan.

"Mi alma your mother is also part of the mailafiya family and kinsan Sarwa ta bace da duk wani mahadi da mabudin dukiyar mu Wanda yake wurin babanmu, har yau mamanmu Bata farka ba ballantana a samu wannan kudin su dawo garemu, so idan Kika koma gida ma ba wani amfani hakan zai Miki ba"

" Amman ai mahaifina ba 'dan zuri'an mailafiya bane ko? Kawai ka sake ni ka fita harqata"

" Bazanyi ba cariña do whatever you want"

" To wallahi Kai da zaman lafiya kunyi sallama a cikin gidan Nan tashin hankali yanzu ka fara gani"

" I don't care tunda kina da tsoro har kikan lanqwasa harshen ki zanyi manage a haka"

Yana Gama fadan haka ya wuce dakin shi ranshi yana mishi zafi, yana addu'an Allah ya bayyana Sarwa wa'innan matsalolin suzo qarshe.

**********
Salee na shiga gida taci Karo da Helen da Lateefa suna tsaye cirko_cirko ana jiran dawowar ta, damuwar da ta gani Akan fuskokin su yasa annurin fuskarta bat ya bace, hankalin ta ya tashi a tunanin ta wani Abu ne ya Sami Leesa.

Suna hangota suka hayayyaqo suna masifa kaman zasu ari baki don daga musu hankali da Leesa tayi ba na wa bane,  da ta dawo taga babu Salee a cikin gidan haka ta baje a tsakar gidan tana birgima har Shugaba Saida hankalin ta ya tashi.

"Ina Kika tsaya Salee, wani irin rashin hankali ne wannan anfi awa 2 da tashin ku a makaranta Amman sai yanzu Kika dawo kin daga hankalin Leesa gashi tun dazu ta fita neman ki itama Bata dawo ba"

Itama hankalin ta a tashe ta juya ta fita daga gidan Bata tsaya sauraron abin da suke fada Mata ba.

Gaba Daya unguwan su Saida ta zaga tana duba Leesa Bata ganta ba, can kaman ta tuna wani Abu ta shigar lungun da suke bi idan zasu dawo daga makaranta, daga nesa  ta hango Leesa tana zaune dabas a qasa ta hada Kai da guiwa tana kuka, da sauri ta qarasa wurin ta

"Leesa ki daina kuka gani na dawo babu abinda ya sameni fa naje wurin ma......"

Bata qarasa magana ba Leesa ta dauke ta da mari
"Mahmuda again? Ke meyasa kunnen ki na qashi be bayi Jin magana? Ina raba ki da maza bakiji nayi Miki Imani da Allah idan Kika sake wani Abu makamancin haka sai kinyi nadama sakarya kawai"

Tana Gama fadan haka tayi gaba, Salee kuwa ta tsuke bakin ta tayi shiru, gwanda suje Akan mahmudan ne Amman idan har tasan wurin Sa'eed ta tsaya sunan ta sorry.

Har suka Gama Shirin islamiyya Salee na faman bawa Leesa haquri Amman taqi haqura, gashi taqi cin abinci tayi kicin_kicin sai cika take tana batsewa.

Koda suka Isa aji ma Bata zauna seat daya tare da ita ba haka ta koma seat dinsu munnira tanajin Yanda suke zagin ta a cikin kunnen Amman ta gwammace hakan Akan ta koma wurin Salee saboda ta nuna Mata tsananin fushin ta.

Washe gari da cramps Salee ta tashi da qyar ta iya Taya Leesa wasu daga cikin ayyukan gida ta koma ta kwanta, haka leesa ta qarashe aikin Shugaba Tass tayi awara ta tafi school dashi saboda suna buqatar kudin abinci da na magani.

Sa'eed baiga salee ba Kuma Bai damu ya neme ta ba don Bata gabanshi, da aka tashi daga school Leesa na kallon Yanda 'yammata suke rubibin siyan Abu a wurin shi, shi Kuma sai arhantar musu da murmushin shi yake yi hakan da yayi ya qara dasa tsanar shi a zuciyar Leesa tana Allah wadai da irin wa'innan mazan masu rudan Yan Mata su kaisu su baro.

Tunda ta koma gida Salee me faman binta da Ido tana son tambayanta malam Sa'eed Amman tana mugun tsoro, jiya ma daqyar ta samu ta sake Mata fuska Saida ta ganta a qasa tana murqusoson ciwon ciki kafin ta kulata.

Ganin kallon yaqi ci yaqi cinyewa yasa ta qaraso wurin da take kwance ta zauna a gefen ta tace

"Kina buqatar wani Abu ne?"

Kaman tace Mata malam Sa'eed take kallo tace
"Aa yunwa nake ji"

Murmushi tayi Mata sannan ta tashi ta dauko Mata sauran abincin da ya rage a food plask dinsu ta kawo mata, a dole ta dinga turawa badon tana Jin yunwa ba saidan ta samu lokacin zantawa da 'yar uwar ta.

"Yanzu ace na samu mijin aure Zaki barni nayi?"
Kaman daga sama Leesa taji Salee ta jefo Mata wannan tambayar.

Murmushi Mai sauti tayi sannan tace
"Me zai hana my Salee? Amman sai lokacin da muka cika burin mu tukunna, sai Kinga iyayen ki ni Kuma na dauki fansa, lokacin muma Mun zamo wasu babu Mai wulaqanta mu"

" Leesa ni na fasa cika burina, saboda bansan ranar cikan shi ba, a jikin takardan Nan sun rubuta cewa zasu zo su dauke mu bada jimawa ba Amman har yanzu babu labari, babu wata hanya da muke dashi Wanda zamu Nemo su, kudin da muke Tarawa ma muna Bata lokacin mu ne don lalube zamuyi tayi a cikin duhu please mu haqura haka Nan"

" Haba Salee kada ki sare da wuri Mana, idan mukayi karatu mukayi kudi zasu zo da qafansu su same mu Daman gudun talauci ne yasa suka yada mu, ko ke Baki son wataran ki tuqa mota irin na hajiya talatu?"

" Baniso bazan iya jurewa ba kina ganin irin halinda nake ciki, bani son inyi ta mafarkin da bazai zamo gaskiya ba, ni aure nake son nayi in rufa ma kaina asiri na samu wannan tabon karuwan cin dake jikina ya wanke Nima a dinga respecting dina kamar ko wace matar aure Kuma 'yar mutunci ba kilaki ba"

Kaman wata zararriya haka Leesa ta birkice ta fara sumbatu tasan kafiya irin na Salee Kuma ba zata zuba Ido tana gani tabar rayuwar ta ya lalace ba, qarasowa gaban ta tayi ta tsunguna akan guiwowin ta cikin muryar lallashi tace

"Salee inadai bawai kin fara soyayya da wani a boye bane? Ina ba mahmuda kike so ba? Dan Allah kada ki yarje ma zuciyar ki ta aminta dashi ba sonki da gaske yake ba, ya riga ya fito fili ya fada Miki abinda yake so daga gareki Dan Allah ki rufamin asiri"

" Niba mahmuda nake so ba, bani soyayya da kowa am...."

"Yauwa Masha Allah Dan Allah ki qara haquri kadan kawai, ki qaramin lokaci Leesa kudin Nan na qara yawa zankai ma hukuma a Nemo Mana su, idan yaso sai kiyi auren ki daga baya Kinga a lokacin babu Mai Miki gori"

Ganin Yanda gava Daya ta rikice yasa Salee ta gyada Mata Kai ba tare da ta sake cewa komai ba, ganin haka yasa ta saki murmushi tayi Mata peck a goshi ta miqe hade da fadin
"Bari na kawo Miki magani Kisha"

Washe gari dukda tanajin sauran ciwon cikin haka ta daddage sukayi aikin gidan tare sannan ta shirya tayi sammakon zuwa makaranta don kawai taga malam Sa'eed.

Saidai har aka tashi Bata ganshi ba baby ma alaman yazo makarantar, haka ta jera kusan sati tana baza Ido ko zata ganshi Amman shiru.

*********

Bangaren Sa'eed kuwa tunda yaji Sa'ood shiru Bai sake kawo masa hari ba ya koma shagon shi na kasuwa.

Sa'ood kuwa ya samu daman shiga jikin daya daga cikin yaran Garba TK masu kusanci dashi sosai, ganin irin qwazon shi a harqan ta'addanci da Yanda sunan shi yayi qauri dukda ko hukuma Basu taba ganin fuskar shi ba, yasa suka amince dashi sosai ba tare da sanin cewa shi maqiyin su bane.

Sosai ya maida hankali Yana son gano ta hanyar da zai illata ogan su, bayi samun lokacin da zai waiwayi Sa'eed har ya takura shi Kan maganar Sarwa.

*********

Salee ta Gama shiga damuwan rashin ganin malam Sa'eed har wata Yar Rama tayi she missed his smile and his voice tana son sake ganin shi ko ta Yaya ne.

Da yamma ta fita da nufin taje gidan shi ta duba ko lafiya Dan shirun yayi Mata yawa, kafin ta qarasa layin su ta hango shi zaune a wani local restaurant na wata arniya gaba Daya wurin kaman ba restaurant ba very dirty gashi Nan, ga Kan matan a bude yasha gashin dokin da babu gyara.

Gaba Daya wurin gardawan maza ne amman Bata damu ba ta shiga ciki don ba yau ta fara ganin irin hakan ba, ta riga ta Saba da zama wuri daya dasu.

Zama tayi a kujeran dake gaban nashi ta qura mishi ido, gaba Daya hankalin shi bayi jikin shi.

Dan tafa hannuwan ta tayi yayi firgigit Yana kallon ta baima San tazo wurin ba hankalin gaba daya na Kan maganar da Nabila ta fada mishi akan mamanmu ana ta samun improvement akan rashin lafiyar ta.

Murmushi ta sakar masa ta kashe murya kafin tace
"Ina wuni malam Sa'eed"

Shima Dan yaqe yayi yace "lafiya, Mai kikeyi a Nan?"

"Babu, kawai nazo wucewa ne na ganka kana barci a zaune shine nazo tada ka kada a sace min aboki na Bai sani ba"

Dariya yayi sosai Saida fararen haqwaran shi ya bayyana yace
"Ke koh? Yanzu dai fadamin Ina zakije?"

Shiru tayi ta fara was da yatsun hannun ta cikin kunya tace
"Gida zanje duba ka, Naga kwana biyu baka zuwa makaranta ne shiyasa nayi tunanin ko baka da lafiya ne"

Saida yaji qirjin shi ya buga Jin maganar ta, why did she care so much about him? Karfa ta fara son shi ne! Lallai kuwa akwaita don shi damuwan dake kanshi kadai ya ishe shi bare azo Kan Zarah, bayi son abinda zai qara Bata Mata Rai Akan Wanda take fama dashi na babu gaira babu dalili.

"Yaya baka ci abincin ba? Gashi har yayi sanyi" muryar ta ya katse mishi tunani.

Dan murmushi yayi baice Mata komai ba, tace
"Ohh babu Dadi ko?"

Gyada Mata Kai yayi,

" ok yanzu muyi wani Abu daya ka dinga kawo kudin abincin ka sai ana dafa maka a gidan mu ana kawo maka hakan yayi?

Girgiza Kai yayi yace "no thank you Amman matata ba zataji dadin hakan ba"

" Mtsww tasan da hakan take barin ka kana cin abinci a waje? Saidai idan kaima kanajin qyamar mu ne kaman Yanda sauran mutane keyi"

Da sauri yace " noo ko kadan, kefa qawata ce Yaya za'ayi nayi qyamar ki?"

Murmushin cin nasara tayi tace " tunda haka ne daga gobe za'a fara kawo maka abinci, na farko za'ayi maka shi kyauta idan yayi maka Dadi sai kana bada kudin ana dafa maka ko?

Gyada Mata Kai yayi kaman wani Wawa,
"Yauwa ni zan tafi sai goben idan an kawo maka nasan Leesa tana jirana idan na dade zatayi fada, sai anjima"

Tana daga Masa hannu har tabar restaurant din ya Mata rakiyan idanu,

Tunda ta tunkaro gidan qirjin ta yake dukan uku_uku tana taraddadin Yanda zata samu Leesa da maganar abincin Sa'eed Wanda a garin karambanin ta ta jajibo ma kanta..............🧚

#vote
#share
#comment

Lanjutkan Membaca

Kamu Akan Menyukai Ini

1.6K 148 28
Ayzar hisham Alee a man who doesn't believe in love again was ordered to marry an ordinary girl. Najma khaleel a lady with good values. She is loving...
1.5M 128K 62
RATHOD In a broken family, every person suffers from his insecurities and guilt. Successful in every field but a big failure when it comes to emotio...
5K 442 40
love is a strange feeling but also a very strong connection that will either be your strength or your weakness it all depends on who you've to be wit...
445K 16.2K 192
Won Yoo-ha, a trainee unfairly deprived of the opportunity to appear on a survival program scheduled to hit the jackpot, became a failure of an idol...