MIJINA NE! ✅

By Aishatuh_M

92.4K 12.2K 1.9K

Ashe dama ana mutuwa a dawo? Ashe dama in mutum ya mutu, aka binne shi a kasa zaka iya ganinshi a rayuwarka? ... More

Daya
Biyu
Ukku
Hudu
Biyar
Shida
Bakwai
Takwas
Tara
Goma
Sha Biyu
Sha Ukku
Sha Hudu
Sha Biyar
Sha Shida
Sha Bakwai
Sha Takwas
Sha Tara
Ashirin
Ashirin Da Daya
Ashirin Da Biyu
Ashirin Da Ukku
Ashirin Da Hudu
Ashirin Da Biyar
Ashirin Da Shida
Ashirin Da Bakwai
Ashirin Da Takwas
Ashirin Da Tara
Talatin
Talatin Da Daya
Talatin Da Biyu
Talatin Da Uku
Talatin Da Hudu
Talatin Da Biyar
Talatin Da Shida
Talatin Da Bakwai
Talatin Da Takwas
Talatin Da Tara
Arba'in
Arba'in Da Daya
Arba'in Da Biyu
Arba'in Da Uku
Arba'in Da Hudu
Arba'in Da Biyar
Arba'in Da Shida
Arba'in Da Bakwai
Arba'in Da Takwas
Arba'in Da Tara
Hamsin
Hamsin Da Daya
Hamsin Da Biyu
Hamsin Da Uku
Hamsin Da Hudu
Karshe.

Sha Daya

1.7K 342 84
By Aishatuh_M

Saida ta shiga motar ta zauna kafin ta juyo da dan guntun murmushinta. "Ina wuni?" Ta furta a hankali tana fara wasa da yatsun hannunta. Ita kam nauyin Dr Aliyu takeji. Eh tasan kunya tana daya daga cikin dabi'unta amma nauyi da kunyarshi da takeji daban ne, kila hakan yana da alaka da kwarjinin da yake mata.

Yar dariya yayi ya juyo yana kallonta hade da girgiza kai, "Wannan hausa taki da anji ansan daga Katsina kike ko baki fada ba. Ina yini ake cewa ba ina wuni ba." Sai lokacin ta fahimci dalilin kallonta da yakeyi da kuma murmushin dayake mata.

Dan turbune baki tayi a hankali, "Kaidai kawai ka ansa shikenan ba sai an zauna ana kidayar hausar wane gari nikeyi ba."

Dariya ya fara yanzu, "Nakeyi ba zakice. To in zan amsa ki me zance?" Daga gani dukda ba wata hira suke ba amma abun yana mashi dadi. Saida ta kalleshi da kamar bazata amsa ba can kuma ta dan dake irin to koma menene ai ba laifi nayi ba.

"Lahiya lau zakace ko? Da ya ake amsa gaisuwa?" Dr Aliyu baisan lokacin daya fashe da wata irin muguwar dariya ba. Sai kara maimaita 'Lahiya Lau' yake kamar wanda yau ya fara jin ana cewa haka. Ganin ta bata fuska yasa ya daina dariyar ya juyo yana kallonta.

"Yi hakuri toh, na daina dariyar. Amma yanzu tunda Abuja kike ki daina maganar yan Katsina. Ba wannan ba, naga bakizo asibiti ba yau, ko lafiya ta samu?" Kallonta yake kyam yanaso yaga yanayin yanda zata mashi magana wanda ta hanyar ne zai fahimce ta.

Dan murmushi tayi kafin ta gyada mashi kai. "Eh toh, Alhamdulillah zance. Zan iya daina zuwa ko kuwa dole sai naje?"

Cikin girgiza kai ya bata amsa, "Aa, muda mukesan kima manta kin taba zuwa asibitin. In har kinaji you can cope, ba sai kinzo ba. Amma ni zan iya zuwa?" Dakyar ya samu maganar nan ta fito bakinshi kamar wanda yayi laifi yana jiran hukuncin alkali.

Ramlah wani kasake tayi tana kallonshi, itadai ba yarinya ba balle ta nuna mashi cewar bata gane abunda yake nufi ba. Dukda cewar girman nata itama rayuwa ce ta mayar da ita babba bawai dan takai shekarun girman ba. Dan wayincewa tayi, "Kazo? Ina zakazo?"

Sarai yasan da gangan take nuna bata gane abunda yake nufi ba, "Nan gidan mana, ko kar nazo?"

"Me zakayi in kazo?"

"Wajenki zanzo mana."

"Me zan maka toh?"

"Ganinki kawai zanyi, muyi labari, kiman hausar Katsinawa sai na tafi na bawa Hafsah labarin Amminta." Ita ba kasafai ta cika san irin yan maganganun nan ba, duk yanzu a haka ma yanda suke ya gama dagula mata lissafi. Jin ya ambaci sunan Hafsah yasa ta samu mafita.

"Allah sarki Hafsah, ya take? Nayi missing dinta."

Baice mata komai ba ya ciro waya ya kira Hajia Mama, kamar kuwa yasan wayar ma tana hannun Hafsah muryarta sukaji tana fadin, "Hello? Wake magana? Hajia Mama tana bangaren Baba Alhaji, kuma munyi fada dashi nace bazan kara zuwa wajenshi ba, idan ta dawo zan gaya mata an kira."

Dama a speaker ya saka wayar, dariya kawai suke fashe da ita a tare. "Innalillahi, Hafsah yanzu da Baba Alhajin ake fada?" Ramlah batasan lokacin da tayi magana ba muryarta cike da dariya.

Shiru sukaji kafin a hankali Hafsah ta fara magana, "Ammi? Tsaya, wai dama Abba ne?! Ammi karki fada mashi nayi fada da Baba Alhaji, shima wai sai yace tunda nayi fada da Babanshi shima ba ruwanshi dani."

Ramlah juyawa tayi tana kallon Aliyu da sai murmushi yake, ba sai ya fada ba zakaga tsantsan soyayyar diyarshi cikin idonshi. "To indai bakisan Abba yaji da mun gama waya sai kije kibawa Baba Alhaji hakuri kinji?"

Hafsah sai gyada mata kai take kamar tana gabanta, "Eh Ammi. Ina yini? Ammi nayi missing dinki." Fira suka farayi har suka gama Aliyu yana jinsh amma ko kadan baice ko kala ba. Karshe ma komawa yayi ya tsaida nashi idanun akan Ramlah wacce sai dariya take suna fira da Hafsah. In ka ganta tana dariya bazaka tana tunanin ta taba shiga kuncin rayuwa ba.

Bata jima ba bayan sun gama waya da Hafsah ta mashi sallama ta dawo cikin gida. Dakin Lubnah ta wuce kai tsaye, ganinta a dakinta ba karamin mamaki yana Lubnah ba, da murna ta rungume ta tana janyota suka zauna bakin gado. "Kinma kuwa taba zuwa dakina Ramlah? Ah lallai Dr Aliyu ba karamin aiki yake ma zuciyarki ba."

Dariya Ramlah tayi tana girgiza kai, "Ni wallahi ba komai fa tsakanin mu, ina diyarshi Hafsah? Itace kawai take tunanin wai ni Amminta ce shine fa, nima tana tuna man Hanan kuma ina santa sosai."

"Baban nata ma za'a so shi nan bada dadewa ba." Dan dukan wasa Ramlah ta kai mata sai dariya suke. Nan Lubnah ta fara bata labarin makaranta kafin can tayi wani ihu.

"Ke wallahi nama manta nikam!" Wayarta ta janyo ta nuna mata hotanta da wata budurwa kyakyawa, "Kinsan na taba nuna hoton Zainab ko?" Daga kai Ramlah tayi tana kara kallon hoton, "To bikinta ya kusa, yar Maiduguri ce, kuma nace ban yarda kowa yayi hoton biki ba sai ke. Ai kun kusa gama classes dinku ko?"

"Ranar juma'a zamu karbi certificate dinmu. Amma Lubnah anya kuwa? Bikin yan gayu ne fah." Dariya Lubnah ta mata tana dan dukan kafadarta.

"Kema ai yar gayun ce. Bari ma in baki labari kiji, na riga na sai mana anko, kuma gayu zakici kisha ado kinsan dai yan Maiduguri yanda suke, waya sani kila ki samo kana angon namu a can. Yauwa, na samo maki assistants har biyu, mace da namiji suma photographers ne amma yan kaduna, idan mun dawo sai a fara maganar bude studio ko?"

Kallonta kawai Ramlah takeyi idonta yayi rau rau da hawaye kafin ta rungume ta, "Bansan da wane irin baki zan gode maki ba Lubnah, Allah yai maki yanda kika mun, mafiyi ma insha Allahu."

Dariya Lubnah tayi tace Ameen kafin ta kara kallonta, "Kuma ba kyauta zaki mata ba, sai an biyaki. Yanzu dai nace mata baki da account to gobe sai muje banki ki bude da komai da komai."

"Banso, ta baki kudin." Dariya ma Lubnah abun ya bata.

"Ke dallah nuna mata nayi ba karamar mutum bace ke, in kika nuna wasa sime sime kuma shikenan, san raina nayi charging dinta kudin professionals. Yanzu dai duk ba wannan ba, so nake muje da Rayyan bikin, kina ganin zai bimu?"

Ramlah tsayawa tayi tana kallon yanda Lubnah ke murmushi irin na wanda ya fada soyayya, "Wannan Rayyan dai ana sanshi, amma yana da kirki shima kamarki, in kukayi aure gidan yan aljanna zan rika cema gidanku."

Dariya Lubnah tayi tana kulle idanunta, "Ni kinsan me? Shi daga gani kawarshi kawai ya daukeni, ni kuma tsakani da Allah banma san yanda akayi ba na fara sanshi, abun ma ni har tsoro yake bani. Yanzu ya kike ganin za'ayi? Banso in dizga kaina in tambayeshi kuma yace bazaizo ba."

Juyowa Ramlah tayi tana fuskantarta, "Yaushe ne bikin?"

"Nan da sati daya."

"Ko kice mashi direba zaiyi tafiya dan Allah shi ya kaimu?" Da hanzari ma Lubnah ta girgiza kanta.

"Ai ba'a mota zamu ba, kin ganni nan tsoron hanyar Maiduguri nake kamar mutuwa ta. A dai samo wata hanyar ba wannan ba."

Dariya Ramlah tayi tana karkada kai alamar tunani, "Wannan soyayya dai da gaske ake yinta. Kinsan ya za'ayi? Ina wayarki?" Miko mata wayar Lubnah tayi ba tare data tambayeta akasin hakan ba.

Sako ta rubuta kafin fa mikama Lubnah akan taga in yayi, "Kina ganin hakan zaiyi?"

"To nidai ba wani iya soyayya nayi ba amma dai nasan it's high time kin fara nuna mashi kina sanshi ko yaya ne kuwa. Bari dai mugani, inma ya nuna bai gani ba sai mu fito mashi a mutum."

"Ramlahhh." Lubnah ta fada da muryar mutum me kamar san kuka, ita tama rasa yanda zatayi.

"Dan Allah daina karki bani kunya, ke yana ma sanki nasani, kila dukanku kowa dauka yake aboki kowa ya dauki dan'uwanshi. Ki fara nunawa ko kadan ne sai mugani. Amma dai kafin mu dawo Maiduguri tabbas asa ya fara sanki."

"To ta yaya? Ni su Mama ma nakeso suce ayi auren yanzu, ke wallahi sanshi nake." Wata dariya Ramlah take ganin Lubnah da gasken gaske take san Rayyan take. Irin san nan wanda mutum yake tunanin ya zaiyi da wanda yakeso?

"Anya kuwa? To kodai kodai? Ni sai yanzu ma nake fahimtar inda kika dosa, sai kice man aure kikeso in taimaka inyi ma Mama bayani..." ai Ramlah bata ida magana ba Lubnah ta dak'a mata duka suka fashe da dariya. Rabon da taji ranta ya mata sanyi, zuciyarta ta mata fari tun bayan mutuwar Abban Hanan, wannan itace sila ta rushewar dukkan wani farin ciki nata.

Karshe ma da fira tayi dadi kitchen sukaje Lubnah tana hada masu abinci suna fira, koda suka gama ci falo suka zauna suna kallo dukda cewar dare yayi, amma Lubnah tace Ramlah ta rasa abubuwa na rayuwa da yawa, ta tabbatar taji dadin duniyarta. Wanda shine ta shirya yi yanzu, ta aje komai na rayuwar da tayi ta gode ma Allah ta rayu cikin farin ciki.

Tunda dai baku comments zan tafi hutun sati daya.

Bissalam.

Continue Reading

You'll Also Like

115K 11K 62
Labari ne da ya k'unshi tsana, k'iyayyaya, mugunta, da uwa uba soyayya. Ku biyo ni kuji me zai faru a littafin //Zafin Rabo//
286K 14.6K 83
🍁ကောင်းခြင်းတည်မြဲ.. 🍁 နိုင်ငံခြားပြန်ကောင်လေး။ ရုပ်ရည်၊ ပညာ၊ စည်းစိမ်ဥစ္စာပြည့်စုံကြွယ်ဝသူမို့ အတော်လေးကြီးကျယ်သည့်လူ။ သူ့ကိုသူလည်း အထင်ကြီးလွန်းပ...
349K 22.6K 36
unexpected relationship last longer,,,, as east meets west in love....
334K 8.3K 79
တောင်ပေါ်သားနဲ့ မြေပြန့်သူ ဇာတ်လမ်းလေးပါရှင့်